Skip to content
Part 28 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

A karo na biyu Hajiya Ladidi ta sake kwashewa da dariya, tana kallon yadda jikin Rahma ke rawar da ya gaza ɓoyuwa.

Idanunta ta mayar kan Samira tana cewa.

“Eh lallai na yarda, ɗanya ce shataf a wannan harka. Amma ba wani abin damuwa a ciki.

Da sannu za ta fahimci komai, za’ayi mata regista da Ƙungiya bayan anyi mata wankan dafa’i da jalabi. Yanzu dai ki shiga da ita ciki ta huta, ki bata duk abinda za ta buƙata. Ko jibi haka za’a haɗa taron ƙungiya taga membobin ƙungiya su ma ganta matsayin sabuwar zuwa.”

“To Hajjaju, godiya muke.”

Samira ta amsa cikin farin ciki.

Hannun Rahma da ko kaɗan bata so bayan tanƙamemen falon ta ƙara taka wani guri a cikin gidan ba ta ja suka nufi ɗaya daga cikin ɗakunan Hajiyar. Suna shiga taja tunga a tsakar ɗakin, ta ɗaure fuska tamau.

“Me yasa kika janyo ni cikin ɗaki? Na zaci daga can falon wucewa za muyi?”

“Wucewa kuma? Daga zuwanmu ko ruwan gidan Hajjaju baki sha ba ki ce mu wuce?”

Ta tambayeta da mamaki sosai a fuskarta.

Sai a lokacin ta lura da yadda Rahmar ta harhaɗe gabas da yamma.

“Lafiya dai ƙawata? Me aka miki haka kika sha mur? Ko wani abin kika tuna…?”

“Ba wani abu da na tuna. Kinga Samira tsakaninmu ba ɓoye-ɓoye. Zancen gaskiya tun da muka shigo gidannan matarnan bata kwanta min ba. Mace tsohuwar guzuma sai kallona take yi tana lashe baki kamar tsohuwar mayya? Duk wani zaurance da kuke yi tsaf na fahimci inda kuka dosa, don haka ni kam wannan ƙungiya taku akai kasuwa. Bayan zunubin da kika taka muhimmiyar rawa gurin tsunduma ni a ciki ina ji ina gani bazan ƙara jefa kaina cikin wani bala’in da aka hallakar da al’ummar Annabi Luɗu saboda ita ba. Ni kinga tafiyata.”

Daman tun shigarsu ko jakarta bata aje ba balle ta cire mayafi, cikin sauri ta fice daga ɗakin ba tare da ta saurari kiran da Samira take mata ba.

Hajiya Ladidi tana amsa waya taga fitowar Rahma da sassarfa, ko kallonta bata yi ba ta nufi ƙofar fita daga falon. Kafin ta katse wayar ta tambayeta ina za ta har ta fice gaba ɗaya daga cikin falon ta mako ƙofar ta can waje da ƙarfi.

Baki buɗe take kallon ƙofar, mamaki fal fuskarta tsulum taga fitowar Samira ita ma da sauri tana ƙwalla kiran sunan Rahma.

“Ta tafi! Lafiya kuwa? Na ga ta fito da sauri ko kallona bata yi ba ta fita, ko rasuwa aka yi mata?”

Kusa da Hajiyar ta nemi gurin zama, ranta a ɓace. Ƙasa ƙasa taja tsaki kafin ta mayar ma da Hajiyar bayanin duk abinda ya faru bayan shigewarsu cikin ɗaki.

“Wannan yarinyar fa da ganinta kifin rijiya ce.

Ki kwantar da hankalinki, yadda ta fita da ƙafafunta haka za ta dawo. Ba dai ta sha ruwan gidannan ba?”

“Bata sha ba fa Hajiya.”
Ta sake amsawa da damuwa a muryarta.

“Ba matsala, da ta sha, lamarin zai fi zuwa da sauƙi. Amma duk da bata sha ba baza’a rasa yadda za’a jawo ta cikin ƙungiya dumu-dumu ba. Ganin yau kaɗai da nayi ma yarinyar ta kwanta min arai.”

“Hajiya har da kallon da kike mata kina lashe baki fa ya tsoratata. Ce min tayi kina abu kamar mayya.”

A tare su biyun suka kwashe da dariya.

******

Kwanci tashi ba wuya a gurin mahaliccin sammai da ƙassai. Yau har ga shi Firdausi ta gama istibra’i da kwana biyar. Ba tare da ɓata lokaci ba Alhaji Lukman ya sanar da Yaya Yusuf.

“Alhamdulillah! Ma sha Allah! Yau muna asabar ko Alhaji? To jibi litinin in sha Allah muna tafe da komai da komai na ɗaura aure. In yaso ko bayan sallar azahar sai a ɗaura auren. Mu dai a ɓangarenmu ba sai munyi gagarumin gayyata ba, fatanmu Allah yasa albarka, ya zaunar da su lafiya.”

“Amin ya Allah! Madallah! Babu laifi hakan, Allah ya kaimu jibin da rai da lafiya.”

Haka suka rabu, fuskar Alhaji Lukhman yalwace da farin ciki ya juya yana sanar da iyalansa yadda suka yi da Yaya Yusuf.

“Abba?”

Fiddausi da tun fara zancen bata tanka ba ta kira sunan da suke faɗawa uban, muryarta a sanyaye. Tana zaune ne aka kafet can gefe ɗaya, tana sanye da zumbulelen hijabi, a hannunta casbaha ne take ja, tun bayan idar da sallar walha da tayi tana zaune a gurin tana lazumi.

Ko da aka sharari wata guda ba tare da mummunan yanayin ya motsa ma Fiddausi ba ita da Iyayenta suka tabbatar ta gama samun sauƙi. Tun kafin lokacin ma su a karan kansu sun fahimci gwaggwaɓar canji a tare da ita.

Da bakinta ta faɗa ma mahaifiyarta ranar da Khamis ya faɗa musu an karya asirin, bayan ta tashi barci, ta ce tana ji kamar an zare mata wani ƙaya da ya daɗe yana sukarta. Ko da iyayen suka faɗa mata hukuncin da aka yanke na sai tayi Istibra’i za’a ɗaura auren basu ga damuwa ko kaɗan a fuskarta ba.

Saboda dawowarta cikin hankali da nutsuwarta sai nadama sosai ya ƙara lulluɓeta na munanan abubuwan da ta aikata a rayuwarta. Ta sani Khamis ya taka muhimmiyar rawa gurin lalata rayuwarta, amma fa idan an bi ta ɓarawo abi ta mabi sawu. Tun farkon fari da ta haɗu da shi ta fahimci ba aurenta yasa ya maƙale mata ba me yasa ta biye mishi? Har ta yarda a fakaice ya dinga zigeta tana koran masu sonta da aure? Tunda ta san ba son ta yake yi ba, kuma bai nuna yana so ya aure ta ba, me yasa ta rasa wanda za ta kai ma kukanta lokacin da Abbanta ya ce ta fito da miji sai shi? Me yasa ta yarda da shi sadda ya bata lambar malaminsa? Wani daƙiƙanci da wauta ne yasa ta yarda da shi yayi mata wankan magani? Hadithi ne ingantacce duk sadda namiji da mace suka keɓe na ukunsu shaiɗan ne, balle ita kuma da suka keɓe tana tsaye a gabansa haihuwar mahaifiyarta da sunan yana mata wankan magani… Tana zuwa nan a tunaninta sai zafafan hawaye su ɓalle mata wasu na korar wasu.

Sannu a hankali yanayi na muzanta da jin kunyan ahalinta ya lulluɓeta. Duk sun san abinda ta aikata, ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba. Ba ta samun nutsuwa sai idan ta fuskanci ubangijinta tana Istigfari, ta zama wata shiru-shiru, babu abinda take so kuma take ƙara samun nutsuwa illah ta keɓe daga cikin iyaye da ƴan’uwanta tana neman gafarar Ubangijinta. Duk da ta roƙi iyayenta da ƴan’uwanta gafara, kuma sun tabbatar sun yafe mata ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ta kasa sakin jiki da su, ta kasa komawa kamar da, yarinya mai walwala da saurin shiga rai.

Duk yanda ƴan’uwan suka so janta a jiki ta ƙi basu damar haka, a dole suka haƙura ba don ransu yana son yadda take ɗari-ɗari da su ba. Basu samu nutsuwa ba sai da iyayen suka janyo hankalinsu, suka nusar da su keɓewa da istigfarin da take yi abu ne mai kyau. Yana daga cikin sharuɗɗan tuba, a roƙi Allah ya yafe kura-kuran baya da alƙawarin baza a sake komawa kan zunubin da aka aikata a baya ba.

Lokacin da watanni uku suka cika suka tabbatar ta tsarkaka, sannan babu komai a cikin mahaifarta ba ƙaramin farin ciki suka yi ba. Ƴan’uwanta har wani ƙwarya-ƙwaryan liyafa suka so haɗawa ba tare da sun bayyana ma duniya maƙasudin haɗa liyafar ba uban ya dakatar da su.

“Me kuke ci na baka na zuba? Ku kwantar da hankalinku. Kar ku manta nan da kwanaki kaɗan za’a ɗaura mata aure. Ku jira lokacin sai kuyi faffaɗar walimar da ta ƙunshi murna da farin ciki ta ko wane ɓangare, kunga lokacin ba wanda zai tambayi walimar me ake yi? Kai tsaye za’a fahimci na murnar aurar da tilon ƴar’uwarku ne.”

“Haka ne kuma Abba. Allah ya kaimu.”

A lokacin da suke wannan maganar, tana zaune tana saurarensu. Amma ko uhummm bata ce ba.

Gaba ɗaya hankulansu suka mayar kanta, suna jiran jin me za ta ce? Yadda ta zama shiru-shiru har so suke su ji ta buɗe baki ta ce wani abu idan suna hira.

“Na’am! Ya aka yi Ƴar Baba?”

Uban ya amsa kiran da tayi mishi, a bayyane fuskarsa ke nuna tsananin ƙaunarsa gare ta.

Kafin ta ce komai, addu’a ta shafa. Ta miƙe tsaye a nutse ta naɗe sallayar da take zaune akai ta ajiye a saman kujera. Kusa da ƙafafun uban ta koma ta zauna, kan kafet ɗin da ya malale tsakar falon.

“Kuyi haƙuri Abba, Umma, Ƴan’uwana. Na san a wannan gaɓar babu abinda kuke so illah ku aurar da ni. Don Allah ku yafe min, na sani ban kasance yarinya ta gari ba a shekarun baya, amma ina roƙon Allah duk juyin juya hali irinna ƙaddara kar Allah yasa in sake maimaita kwatankwacin abinda na aikata a baya. Ina fatan ku ma za ku cigaba da taya ni addu’a.”

“In sha Allah Nana Firdausi. Ki kwantar da hankalinki, tuni mun daɗe da yafe miki. Shi kuwa Allah gafururraheem ne.”

Mahaifiyarta ta amsa mata da haka, da taushin murya.

“Na gode Mummy. Abba, Yayyena kuyi haƙuri. Bazan auri Khamis ba…”

Yadda suka ɗago kawunansu a firgice idanuwansu a warwaje yasa ta kasa aje numfashin maganarta daidai.

Runtse idanu tayi, ta saukar da kanta ƙasa sosai tana jin yadda ƙirjinta ke bugun tara-tara. Duk da taga yanayin da suka shiga bai sa ta fasa maimaita musu abinda ta ce ba.

“Da gaske nake yi Abba. Bazan auri Khamis ba. Amma na amince ka zaɓa min ko tsoho ne ka ɗaura aure na da shi a jibin matuƙar hakan zai kwantar muku da hankali…”

“Me yasa baza ki aure shi ba Firdausi? A wannan halin da ake ciki babu wanda ya dace ya aure ki face Khamis, shukar da ya ɗauki tsawon lokaci yana yi bai kamata lokaci ɗaya wani ya girbe ba. Ko kina so a aura miki mijin da zai wulaƙanta ki ne?”

Yayanta Idris ya faɗi maganganun cikin zafin rai.

Basu san kuka take yi ba, sai da suka ji sannu a hankali tana jan shessheƙa. Kamar baza ta sake magana ba, sai ta ɗago fuskarta da yai shaɓa-shaɓa da hawaye tace,

“Khamis shi ne wanda zan aura in ga gagarumin wulaƙanci irin wanda ban taɓa tsammanin gani ba a rayuwata. Ba kuma wai don zan ƙi yi mishi biyayya ba, Ko da kun tilasta Khamis ya aure ni, ina tabbatar muku babu inda auren zai je.

Wannan matsalar yana ɗaya daga cikin illar da budurwa ke fuskanta matuƙar ta yarda saurayi ya keta alfarmarta kafin aure. Zargi, zai kasance ko wane lokaci yana zargina ne ina zarginsa, saboda kar ta san kar ne. Kuma bazai taɓa ɗaukata da darajaba saboda duk abinda zanyi taƙama da shi bayan auren ya riga ya san yadda komai yake tun kafin ya aure ni.

Kuma idan kun manta in tuna muku, tun farko Khamis ya rantse da Allah a gaban hukuma bazai aure ni ba, ya ƙara da cewa ko kyauta aka bashi ni zai yasar ya gudu. Ba kwa tunanin yanzu da ya amince da aurena don tilastawar Yayanshi da tsoron hukuncin hukuma ne? Ba da Yayan Khamis zanyi zaman aure ba, da Khamis ne. Bazai yiwu ko wane lokaci in dinga kiran Yayanshi ko ku ina kawo ƙararshi ba.

Allah ya sani ni tsoro ma Khamis yake bani, taƙadiri ne fiye da yadda kuke tsammani. Ku dubi dai yadda ya shirya abubuwa suka tafi daidai ta yadda ko da wasa ban taɓa tsammanin yana da wata mummunar manufa akaina ba. Duk yaro matashin da zai iya aikata irin wannan baƙin asirin akan budurwa don kawai ya cimma mummunar buƙatarsa to ko shakka babu zai iya aikata komai don nesanta kanshi da wacce ya tsana.

Kuyi haƙuri, kar ku jagoranci ɗaura auren don kawai rufuwar asirina da naku daga baya a kawo muku gawata. Idan har zamana a gida zai zame muku damuwa da ƙunci da yawan tuna abinda ya wuce. Abba na amince ka zaɓo ko tsoho ne ka aura min, in Allah ya yarda zanyi mishi biyayya kamar yadda addini yayi umarni.”

Tana gama faɗin haka ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta, ta fara raira kuka a hankali, gwanin ban tausayi.

Maganganu masu tsayawa a zuciya da Firdausi ta ɗauki tsawon lokaci tana yi ba ƙaramin kashe musu jiki tayi ba. Duk sun sani, babu komai a cikin maganganunta sai gaskiya tsagwaronta. A fili Khamis yake nuna tsanar Firdausi da aurenta, cuta ce dai ya riga ya cuce su, ko ya aure ta ba shi ne zai sa ƙatoton tabon da yayi sanadiyyar samuwarsa a zukatansu ya goge ba.

Duk shiru suka yi, an rasa wanda zai ce uffan! Ba’a jin ƙaran komai a falon sai hucin A.c da sassanyar muryar Firdausi da take rera kuka kamar karatu.

Basu ga sadda mahaifinsu ya ɗaga waya ya danna kira ba, kawai sai ji suka yi yana magana da Yaya Yusuf.

“Eh! In da hali kuma idan zai yiwu yanzunnan nake buƙatar ganinku kai da Hamisu.”

Basu ji amsar da aka bashi ta can ɓangaren ba. Sai ji suka yi ya sake cewa

“To shi kenan! Allah ya kawo ku lafiya.”

Daga can ɓangaren Yaya Yusuf a wannan lokacin yana gidan Khamis ne. Zuwa da kanshi ba saƙo ba, kuma sai ya taki sa’a Khamis ɗin yana gida a lokacin, amma Ziyada ta tabbatar mishi bai tashi barci ba.

“Ba matsala Ƙanwata. Daman zuwan takanas taki ce ba tashi ba.”

“Yaya Allah yasa dai ba wani laifin aka ce nayi ba?”

Ta tambayeshi da sanyin murya, hannayenta biyu dafe da ƙirji.

Kan kujera ya zauna, da ɗan murmushi a fuskarsa ya tabbatar mata ba laifi tayi ba.

“Ina yaran suke? Na ji gidan shiru.”

“Yau asabar Yaya. Sun tafi hadda tun ƙarfe takwas na safe.”

A ƙasa ta zauna, ta sake gaishe shi karo na biyu tana tambayar ina Aunty Zainab da yara? fatan duk lafiya suke?

Bayan ya tabbatar mata da lafiyarsu shiru ne ya ratsa tsakaninsu na ƴan daƙiƙu. Kallonta yake yi da tausayi sosai a fuskarsa, ita kuwa kanta na ƙasa, tana murza yatsun hannunta na hagu cikin na dama.

Lokaci bayan lokaci ƙirjinta yana bugawa kaɗan-kaɗan, haka kawai ta ji hankalinta ya gaza kwanciya da zuwan Yayan a daidai wannan lokacin, duk ta ƙosa taji abinda ke tafe da shi, amma bata yi gaggawa ba tayi shiru tana saurarensa, har sai da don kanshi ya fara magana a nutse, cike da balaga ta iya magana.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 27Lokaci 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×