Skip to content
Part 29 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Bayan doguwar nasiha, da tunatarwa kan muhimmancin bawa ya yarda da ƙaddarorin da suke cakuɗe da rayuwarsa masu kyau da marasa kyau. Haɗe da tausasan kalamai na kwantar da hankali, ya dire maganganun da faɗa mata Khamis zai ƙara aure, auren kuma na gaugawa, a taƙaicema saura kwanaki biyu a wannan lokacin.

“Duuuuuummm!”

Shi ne sautin da kunnuwanta suka ɗauka na tsawon wasu daƙiƙu. Duk da zaman tsama da suke yi na tsawon lokaci tsakaninta da Khamis wani abu da ita kanta ya bata mamaki shi ne jin yadda wani mahaukacin kishi ya taso mata lokaci ɗaya.

Idanunta suka rufe ruf, ta daɗe a cikin yanayin kafin ta ɗan dawo cikin hankalinta bayan addu’o’i masu yawa da tayi ta maimaitawa a zuciyarta.

Sau huɗu tana ƙoƙarin buɗe baki tayi magana sai taji kamar an manne bakin da supa gulu, sai a karo na biyar ta samu nasarar buɗe baki daƙyar ta iya cewa,

“Aure Yaya? Kuma ya kasa faɗa min tun da wuri sai a yanzu da lokacin yazo gaf?”
Sai hawaye suka ɓalle mata shar! shar! kamar an buɗe famfo.

Bai katse ta ba, ya sani har gobe ruwa na maganin dauɗa. Zazzafar soyayya ce irinta bugawa a jarida aka gabatar tsakanin Khamis da Ziyada kafin Allah ya ƙaddara aurensu a wani murɗaɗɗen yanayi, idan bata nuna kishinta ba ma ai sai Allah ya tambayeta.

Lokaci ya bata tayi kuka sosai don rage zafi da raɗaɗin da take ji. Ita da kanta ta dinga rage ƙarfin kukan har zuwa sa’adda ta samu nasarar tsayar da kukan gaba ɗaya, ya zama sai ajiyar zuciya take saukewa akai-akai.

“Kiyi haƙuri Ziyada.”

Ya sake faɗa a tausashe.

“Na san dole kiji babu daɗi a zuciyarki, domin kishi halitta ne da aka halicci ko wane ɗan’adam da shi. Amma idan Kina tune da irin soyayyar da Khamis yake miki za ki gane har gobe babu wata ƴa mace da ta isa tasha gabanki a fili da zuciyarsa. Kiyi haƙuri don Allah, ki kwantar da hankalinki. Kuma kin sani har gobe ina nan a matsayin Yayanki mai share miki hawaye, Khamis yana ce miki kule zan ce mishi cas, shi kanshi bai isa ya wulaƙantaki ba ballantana wata mace da za ta zauna a ƙarƙashinsa. Kiyi haƙuri kinji ko?”

Kai kawai ta iya ɗaga mishi alamar ta ji. A wannan lokacin, ji take da za ta buɗe baki tabbas ihu za ta yanka saboda wani irin zafi da take ji a zuciyarta.

“Yanzu dai faɗa min, me da me kike buƙata? Na yi magana da masu funitures za su zo su kwashe gado da kujerun falon nan su zuba sababbi. Akwai kuma wasu ƴan kuɗaɗe da zan baki kiyi siyayya, duk da amaryar ba anan gidan za ta zauna ba, kema a matsayinki na uwargida ya kamata a ga muhallinki da ke kanki fesss! Me kike buƙata bayan abubuwan da na lissafa…?”

Fitowar Khamis zuwa cikin falon yasa Yaya ɗauke idanunshi daga kan Ziyada ya mayar kanshi. Ganin fuskarshi a ɗaure tamau ya tabbatar ma kanshi Khamis ya ji batun jibi ɗaura aurenshi da Firdausi. Don haka shi ma sai ya haɗe girar sama da ƙasa yayi murtuk!

“Yaya barka da shigowa.”

Ya gaishe shi daƙyar yana ciccije baki.

“Yauwa! Maganar aurenka ne da Firdausi. Jibi idan Allah ya kaimu za muje da komai a ɗaura auren…”

“Jibi kuma Yaya?”

Ya tambaya yana kumbura baki.

“Saboda Allah me yasa jibi sai ka ce ana yaƙi?”

Ya sake faɗa ɓacin ranshi na ƙara bayyana a fili.

Da ɓacin rai Yaya ya buɗe baki zai mayar mishi da martani sai ga kiran Alhaji Lukhman ya shigo cikin wayarsa. Don haka ya dakata ya ɗaga wayar, a lokacin ne ya sanar da shi su zo da gaggawa yana nemansu shi da Khamis.

Bayan katse wayar, sama da ƙasa ya kalli Khamis ya galla mishi harara, zuciyarsa cike da takaicin yadda Khamis ɗin ya iya fitowa haka daga singileti sai gajeren wando ɗan ƙarami, duk da ya ji muryarsa a gidan.

“Shiga ciki ka saka sutura cikin mintuna uku ka fito yanzunnan mu tafi, Surukinka, baban Firdausi yake son ganinmu.”

Wani mugun kallo ya aika ma Yaya jin ya siffanta Alhaji Lukhman da surukinshi kafin yaja tsaki ƙasa-ƙasa ya juya zuwa cikin ɗaki. Zuciyarsa a ƙuntace, yana saka kaya yana ayyana in banda Yaya ɗan’uwanshi da suka fito ciki ɗaya bai isa ya dinga mishi karan tsaye a al’amuransa ba. Ko karyawa Yaya bai bashi damar yi ba ya uzuzzura mishi suka fice daga gidan.

Suna mota, Yaya yake tuƙawa, Khamis yana zaune a kujerar mai zaman banza shi kaɗai yake cika yana batsewa. Lokaci bayan lokaci yana sakin ƙaramar ƙwafa, ko kuma yaja tsaki ƙasa-ƙasa.

Sun kusa isa gidan Yaya ya ɗan waiwaya ya kalle shi, muryarshi a kausashe ya ce,

“Saura kuma mu isa kayi ƙoƙarin yin wani shirme ko maganar banza akan auren. Na rantse da Allah a gaban kowa zan yanke dangantakar da ke tsakaninmu…”

Cikin tashin hankali da rawar murya Khamis ya katse shi da cewa

“Yaya? Amanar mahaifiyarmu za ka ci don ganin ƙasa ya rufe idanunta?”

“Kai amanonin mahaifiyarmu nawa ka cinye don…”

Ya lailayo ashar ya maka masa.

“Na gaji da kai da halayenka Khamis. Allah ya sani na gaji, haƙurina yana gaf da ƙarewa. Wallahi in dai baza ka nutsu ba ina daf da yanke igiyar alaƙar da ta ƙulla Tsakaninmu. Ba dole ne sai mun rayu a matsayin ƴan’uwan juna ba, ko da ake cewa hannunka ba ya ruɓewa ka yanke bai ishi mutum da azaba bane.”

Jikin Khamis ne yayi sanyi sosai, ya kasa ƙara cewa komai har suka isa ƙofar gidan. Suna yawan samun matsala da Yaya kan munanan halayensa amma bai taɓa zagewa ya faɗa mishi maganganu masu ɗaci irin waɗannan ba. Allah ya sani ba shi da niyyar auren Firdausi ko da wasa, amma a yanzu, ya yanke shawarar zai aure ta ko don saboda Yayansa. Don Yayansa kaɗai…”

“Firdausi ta ce baza ta auri Khamis ba.”

Muryar Alhaji Lukhman ta dira a kunnuwansu ba zato ba tsammani.

A tare, kuma a firgici suka ɗago kawunansu suna kallonshi. Ƙarara fuskarsu ke nuna tantama kan abinda kunnuwansu suka jiyo musu.

“Da gaske fa. Ta kawo mana hujjojin da muka gamsu, har muka ji a ranmu sam baza mu iya tilastata ba.”

Ya sake faɗa don share tantamar da yake karanta a fuskokinsu.

“Amma me yasa Alhaji? Aure tsakanin su biyun shi ne rufuwar asirin yarinyar da shi kanshi Khamis. Me yasa sai da abu yazo gaf za ta ce a’a?”

Ya Yusuf yayi maganganun fuskarsa damalmale da damuwa.

“Inda ba ƙasa ai nan ake gardamar kokawa, ga ka ga Firdausin nan. Mu dai ta tabbatar mana baza ta aure shi ba, da ta aure shi gara in nemo ko tsoho ne a aura mata. Da wannan dalilin yasa na kira ka da gaggawa don in sanar da kai halin da ake ciki.”

Sai a lokacin suka lura da Firdausi da take zaune kusa da mahaifiyarta, ta cusa fuskarta cikin gwuiwoyinta don ma kar suga fuskarta.

Jikinsa a sanyaye ya mayar da idanu kanta.

“Nana Firdausi? Wai da gaske ne abinda nake ji…?”

“Da gaske ne Yaya, kayi haƙuri, bazan auri Khamis ba.”

Ta faɗa kai tsaye ba tare da kwana-kwana ba.

“Ina mishi fatan alkhairi. Zan kuma cigaba da addu’a a tarayyarmu da shi Allah yayi gaggawar sakawa wanda aka zalunta.”

Zaman ƙuda ne ya ratsa falon na tsawon mintuna uku! Babu abinda ake ji sai ƙarar na’urar sanyaya ɗaki da gwamuwar numfashinsu. Tsakanin iyaye, yayyen Firdausi, Khamis da Ɗan’uwansa kowa da irin saƙar da yake yi a zuciyarsa.

Da kallon yanayin Ya Yusuf ƙarara za’a gane ba haka yaso ba. Shi kuwa Khamis da kanshi ke ƙasa lokaci-lokaci yana sauke ƴan ƙananun ajiyar zuciya ya ma ƙi bari aga fuskarsa balle a karanto labarin zuciyarsa.

Alh Lukman ne ya fara katse shirun da cewa,

“Yanzu ka ji daga bakinta ko?”

Yayi tambayar idanunsa na kan Yaya Yusuf.

“Tunda kun ji daga bakinta shi kenan! Sai maganar kuɗin neman aure da sadakin da ka biya dubu ɗari biyu…”

“Don Allah ka bar wannan maganar Alhaji. Allah ya sani ban so fasa wannan auren ba, amma tunda yarinya ta ƙi, ni ma bazan so a tilastata ba. Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi. Ina mai sake baku haƙuri Alhaji, Hajiya, da ku Ƴan’uwan Firdausi. Na sani an riga an cutar da ku, babu wasu kalamai da zanyi amfani da su wajen goge baƙin fentin da ƙanina ya shafa muku. Don Allah kuyi haƙuri, sannan duk sadda hankalin Nana Firdausi ya karkato kan Khamis ta haƙura za ta aure shi ka sanar da ni Alhaji. Za mu zo da komai a ɗaura aure…”

“Hakan ma bazai faru ba in Allah ya yarda. Yaro irin Khamis idan ba shatawar layi irinta ƙaddaraba babu wanda zai so haɗa zuri’a da shi.”

Alhaji Lukhman ya faɗa kai tsaye, da fuska mara walwala.

Gwuiyawu a sanyaye kuma a muzance Ya Yusuf da Khamis suka miƙe za su fice daga falon, bayan sunyi musu sallama amma babu wanda ya amsa.

“Hamisu?”

Mahaifiyar Firdausi da babu wata magana da ya taɓa shiga tsakaninsu ta kira sunanshi.

Ƙirjinshi ne ya ɗan faɗi, daidaita yanayin fuskarsa yayi zuwa ba yabo ba fallasa kafin ya juya yana kallonta.

“Ka cutar da mu, kai ne sanadiyyar rusa kyakkyawar tubalin tarbiyar da na gina yarinyata akai. Ka ji mana ciwo a zuciya, ciwon da ko mun furta mun yafe baza mu taɓa mantawa ba. Tsakaninmu da kai, Allah ya isar mana!!”

Kawar da fuskarta tayi daga kallon fuskarsa da take ganinshi baƙi-ƙirin fiye da baƙin gawayi.

A hankali ya juya, karaf idanunshi suka faɗa cikin na Idris da Ibrahim, wani irin kallo da suke mishi a fusace, kallo ne mai ɗauke da saƙonni da yawa, amma da yake ba yau ne ya fara shiga cakwakiya makamanciyar wannan ba ko a jikinsa. Ɗan ɗage kafaɗa yayi ya kanne musu ido ɗaya sannan ya bi bayan Yayansa suka fice daga falon.

“Allah na gode maka. Yaya yanzu dai sai ka kwantar da hankalinka. Ba ni naƙi aurenta ba, ita ce taƙi aure na…”

“Khamis?”

Yaya ya katse shi ta hanyar kiran sunanshi. Sanyin da jikinshi yayi ya bayyana har a muryarsa.

“Na’am Yaya”

Ya amsa a ladabce.

“Murna kake yi saboda Firdausi ta ƙi aurenk…”

“Ƙwarai kuwa Yaya. Allah ya sani na yi farin ciki. Duk da de na amince da aurenta saboda kai kaɗai. Yanzu da ta fasa don kanta ba ƙaramin daɗi naji ba.”

Ya ƙarasa maganganun da karaɗin murna.

“Anya Khamis? Kana da hankali kuwa? Yanzu kai ko a jikinka baka damu da barinka da Allah da iyayen yarinyar nan da ita kanta suka yi ba? Ba ka tsoron haƙƙi Khamis?”

“Wani haƙƙi kuma kake magana akai Yaya? wannan al’amarin fa idan ina da laifi kashi ɗari to tabbas Firdausi na da Hamsin, don haka babu wani Allah ya isa da zai kama ni. Dama ai Allah isasshe ne, ire-iren waɗannan kalaman na ji su daga bakin iyaye mabanbanta, da za su kamani tuntuni da sai dai labarin wani Khamis ɗin ba ni ba. Don haka ka saki ranka mu cigaba da shanawa, duniya ce, watarana sai labari.”

“Uhmmm! Allah ya kyauta.”

Kalaman da ya iya furtawa kenan ya tattara hankalinsa gaba ɗaya kan tuƙin da yake yi. Zuciyarsa cike da mamaki da tsoron halayen Khamis ɗin.

Bayan Shekaru Hudu

Yammacin ranar Asabar da misalin karfe shida na yamma, yara ne ƙanana da Ƴanmata da Samari suka dinga fitowa daga cikin babbar makarantar Tahfiz ta Noorul-Huda.

Mannira Khamis Abbakar kyakkyawar matashiya mai kimanin shekaru goma sha bakwai, ita ma kamar sauran jerin ɗaliban makarantar, sanye take da riga da wando farare kar sai hijabi ruwan ƙasa wanda ya sauka mata sosai har daf da idan sahu.

A kafaɗarta rataye take da jakar makaranta, wadda ta ƙunshi Al-Qur’ani mai Girma da sauran littattafai. Hafizar yarinya ce mai masifar ƙwaƙwar karatu da nacin koyo. Shi yasa ko a cikin makarantar idan bata zo ta ɗaya ba za ta zo ta biyu.

Bangaren ƙira’a, da ƙwarewa a larabci da iya sa ko wace harfa a mazauninta ita ce kan-kat!!. A shekarunta goma sha bakwai a duniya ta sauke kuma ta haddace Alƙur’ani mai girma.

A ɓangaren musabaƙar karatun Alƙur’ani mai girma da aka gabatar ita ta zama gwarzuwar shekara a jihar kaduna, Ko da aka je yin na ƙasa a jihar Borno ita tazo ta biyu aduk faɗin Nigeria.

A hankali take tafiya cike da natsuwa da kamun kai, kanta a ƙasa, sam ba ta kallace-kallacen gefen titin. Makarantarsu da gidansu wanda suka canza a shekarun baya da suka wuce akwai ƴar tazara, amma hakan bai dameta, a ƙafa take zuwa ta dawo saboda kwaɗayin samun lada.

Bugu da kari hakan yana ɗauke mata hankali daga dogayen tunaninka na matsalolin rayuwar duniya, domin tana tafe ne tana tasbihi da hailala haɗe da istigfari.

Ita ba ma’abociyar ƙawaye ba ce kamar Nauwara, shi yasa ko yanzu ta ware kanta daga sauran abokan karatunta da suke tafiya a ƙungiyance tayi hanyar ta daban. Sam ba ta damuwa da zunɗen da sauran ɗalibai suke yi a kanta cewa girman kai ne yayi mata yawa, don tana ganin tana da ƙoƙari da farin jini shi yasa ba ta damuwa da harkan mutane.

Gab da zata karya kwanar gidansu taga napep a guje ta tsaya a gaba da ita kadan. A sace ta kalli keken, tana niyyar kawar da kanta
Nauwara ta fito daga ciki tana sallamar mai napep ɗin. A lokaci ɗaya kuma tana ƙoƙarin gyara hijabin jikinta wanda ga dukkan alamu a cikin napep din ta sanya.

Kallon Yayar tata ta tsaya tana yi a sanyaye, fuskarta cike da ɓacin rai mai tsanani. Tare suka fita daga gida da niyar zuwa makaranta, amma ita sai ta zame suna fita bakin titi ta tari abin hawa, tace mata wai makaranta zata je. Da yake yanzu Nauwara tana shekarar farko a makarantar School of Nursing and Mid-Wifery da ke Unguwar dosa , ita kuma Mannira tana ajin ƙarshe a babbar secondry.

Tasan ƙarya kawai Nauwara ta sharara mata da tace za ta je makaranta. Yawon gidajen ƙawaye za ta tafi kamar yadda ta saba. Ta rasa dalilin da yasa sam-sam Nauwara ba ta jituwa da makarantar islamiya.

Amma kasancewar a gida kulle ake musu har da na hauka shi yasa a wasu lokutan take yima Nauwara uzurin yawo-yawon da take yi. Iyayensu sun hanasu yin ƙawaye barkatai, sannan babu kula samari, kana idan ba makaranta ba za suje ba, ko yaushe suna gida basa fita ko nan da can.

Nauwara tana isa wajenta ta kalleta tana ɗan jefa mata harara, sai kuma tayi fari da manyan ƙwayoyin idanunta farare kar ta ce,

“Miye? Tun ɗazu kin wani ƙure ni da kallo kamar baki sanni ba.”

Taɓe baki tayi ta kawar da kai gefe ɗaya

“Mu’allim dai ya ce a faɗa miki idan baki je makaranta ba gobe sai ya kira Daddy da kanshi ya faɗa mishi irin fashin da kike yi. Kuma babu wanda yasan takamaimai inda kike zuwa idan kin fito da sunan zuwa islamiya.”

Ita ma bakin ta taɓe, cikin ko-in-kula tana taunar cingam ƙasa ƙasa ta ce,

“To ya faɗa mana! An faɗa mishi tsoronsu nake ji shi da Daddyn?”

Harara Mannira ta gallah mata, shi yasa sam ba wani dogon shiri suke yi ba, akwai bambancin halaye a tsakaninsu. Ita Mannira bata da hayaniya da son shiga mutane, kuma tana matuƙar bin maganar iyayenta, ba ta tsallake duk wani umarninsu.

Nauwara kuwa gaba ɗayanta opposite din Mannira ce, tana da son hayaniya, da tara ƙawaye na banza da wofi, gashi kuma maganar iyayenta a yawancin lokuta kamar iska take a wajenta, yana shiga ta kunnen dama ne ya fita ta kunnen hagu.

<< Lokaci 28Lokaci 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×