Bayan doguwar nasiha, da tunatarwa kan muhimmancin bawa ya yarda da ƙaddarorin da suke cakuɗe da rayuwarsa masu kyau da marasa kyau. Haɗe da tausasan kalamai na kwantar da hankali, ya dire maganganun da faɗa mata Khamis zai ƙara aure, auren kuma na gaugawa, a taƙaicema saura kwanaki biyu a wannan lokacin.
"Duuuuuummm!"
Shi ne sautin da kunnuwanta suka ɗauka na tsawon wasu daƙiƙu. Duk da zaman tsama da suke yi na tsawon lokaci tsakaninta da Khamis wani abu da ita kanta ya bata mamaki shi ne jin yadda wani mahaukacin kishi ya taso. . .