Duk yadda ta kusa raba dare tana tunanin Muhsin bai hana ta tashi tun ƙarfe huɗu na asubahi ba. Nafilfili tayi kamar yadda ta saba kafin kiran sallar asubah, ta ɗauki tsawon lokaci tana karatun Alƙur'ani mai girma sannan Ladan ya kwaɗa kiran sallar farko.
Raka'atanil fijr ta gabatar, ta daɗe tana addu'o'i sannan ta gabatar da sallar asubah! Mannira yarinya ce mai ƙwaƙwar ibada, kamar yadda al'adarta take, idan tayi sallar Asubahi sam ba ta komawa barci.
Za ta ƙara bitar karatun Al-Qur'ani har gari ya fara. . .