Skip to content
Part 31 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Duk yadda ta kusa raba dare tana tunanin Muhsin bai hana ta tashi tun ƙarfe huɗu na asubahi ba. Nafilfili tayi kamar yadda ta saba kafin kiran sallar asubah, ta ɗauki tsawon lokaci tana karatun Alƙur’ani mai girma sannan Ladan ya kwaɗa kiran sallar farko.

Raka’atanil fijr ta gabatar, ta daɗe tana addu’o’i sannan ta gabatar da sallar asubah! Mannira yarinya ce mai ƙwaƙwar ibada, kamar yadda al’adarta take, idan tayi sallar Asubahi sam ba ta komawa barci.

Za ta ƙara bitar karatun Al-Qur’ani har gari ya fara yin haske, sannan tayi azkar din safiya. Har tayi Azkar din ta gama, Nauwara tana kwance tana shaƙar barci.

Tun sadda za ta tayar da sallar asubah tayi-tayi da ita ta tashi tayi sallah amma kamar kullum, ko alamun tashi ma bata yi ba. A ƙarshe ma buɗe mata jajayen idanunta tayi masu cike da barci ta ce,

“Mannee na rantse da Allah idan baki ƙyale ni ba zan lakaɗa miki mugun duka da asubahinnan. Ina ruwanki da sallata?”

Dogon tsaki taja sannan ta juya mata baya ta cigaba da barcinta.

“Ba ruwana da sallarki kam! Kabarinki daban nawa daban! Allah ya shirye ki.”
Abinda ta faɗa kenan da sanyin murya ta koma kan sallaya ta tayar da sallah.

Sai da gari ya waye sosai ta tashi tana naɗe abin sallarta Nauwara ta tashi tana miƙa da salati, mintuna biyu ta ɗauka tana mayar da numfashi sannan ta sakko daga kan gadon, ko kallon Mannira bata yi ba ta shiga bayi.

Bin ta da kallo Mannira tayi fuskarta bayyane da ɓacin rai ƙarara. Ƙasa-ƙasa taja tsaki ta adana dadduma, casbaha, Alƙur’ani a mazauninsu sannan ta fice zuwa kicin.

A ciki ta samu Mommynsu tana aiki. Har ƙasa ta durƙusa tana gaidata, Ziyada ta amsa da sakakkiyar fuska.
“Mannira sarkin aiki, ba kya gajiya sam! Ke kam ko aure kika yi in sha Allah baza ki sha wahala ba. Allah ya kawo miji na gari Ammatana.”

Sai da ta sunne fuska tana dariyar jin kunya ta amsa a ciki-ciki.

‘Ai Allah ya ma kawo miji na gari Mommy, sai fatan Allah ya kai mu lokacin da zan bayyana muku shi.’

Tayi maganganun a zuciyarta.

Har ta ƙarasa kusa da Mummy da niyyar kama mata ayyuka kamar yadda ta saba sai ta dakatar da ita.

“A’ah Mannira. Yau dai ki huta don Allah. Je ki ɗaki kiyi kwanciyarki ko kiyi bitar littattafanki. Kawai idan kin shiga ki turo min waccan uwar ƴan son jikin, yau ita zata kama min ayyuka ko tana so ko bata so.”

Ɗan dariya tayi kafin ta amsa ba tare da ta musa ba.

“To Mummy. Na gode.”

Da ma barci ne sosai a idanunta, kawai dai sabo da ayyukan ne yasa ta fito, ta san da ta fara aiki barcin zai kama gabansa.

Tana komawa ɗaki ta tarar Nauwara har ta gama sallah, ta ƙara komawa kan gado ta ƙudundune da bargo, ko sallayar bata samu halin ɗaukewa daga inda tayi sallah ba.

Tsaki taja mai ƙarfi, ta gallah mata harara kamar tana kallonta sannan ta fara bubbuga gefen ƙafafunta tana kiran sunanta.

A fusace ta buɗe bargon ta watsa mata manyan idanunta da suka fara dawowa da asalin kalarsu na farare tas!

“Ke dai Mannira kin shiga uku, idan ke mayya ce kika kama mutum baza ki taɓa ƙyale shi ba sai kin cinye tas! Miye haka za ki ishe ni da farar safiya? Idan sallah ce na riga na yi, sai ki shafa min lafiya don girman Allah…!”

“Ni ina ruwana da sallarki? Ko kiyi akan lokaci ko kar kiyi matsalarki ce. Hakkina dai na tunatarwa a matsayina ta ƴar’uwarki ina saukewa daidai gwargwado. Idan kinyi kanki kika yiwa ba ni ba! Mommy take nemanki, ta ce ki je yanzunnan! Kar ki kuskura ki bari ta shigo ta same ki.”

Ƙara murtuke fuska tayi sosai kamar za ta fasa ihu. Bakinnan a gaba ta ce,

“Me zan mata ne tunda safen nan saboda Allah?! Shi kenan mutum shi kullum ba za a bar shi yayi barci cikin nutsuwa ba? Ɗan barcin ƙarshen satinnan da ƴanmata ke yi ni kullum sai an nemi takura nawa.?”

Tsabar haushi da takaicin maganganun Nauwara ta kasa mayar mata da martani. In banda rainin hankali da iskanci ko a yaushe ma ake tashinta tayi wani aikin safe da har zata ce wai ana hana ta barci? Kusan kullum ita take aikin gidan da safe, sai ɗaiɗaikun ranaku ne suke yi ita da Mummy.

Amma duk lokacin da za’a ga Nauwara tana aiki a gidan nan to haƙiƙa Mommy ce ta takura matuƙar takurawa. Don shi Daddy ba ya takura mata in dai akan aikin guda ne, sai dai ko akan karatunta, karatunma ya fi tsanantawa sosai akan na boko.

Kwanciya tayi kawai ta juya ma Nauwara baya. Tana jin sadda Nauwara ta sake kwanciya kamar za ta cigaba da barcinta, sai kuma tayi wani gurnani cikin fushi ta tashi a fusace ta fita tana ta masifa ƙasa-ƙasa don kar Mummy ta jiyo ta.

Tana fita Mannira ta ɗauki wayarta ta turawa Qalbinta saƙon barka da safiya, tare da fatan ya tashi lafiya. Da zaƙaƙan kalaman da suke nanata mishi irin matsanancin son da take mishi.

Ba tare da ta jira martanin saƙonshi ba ta kashe wayar ta sake komawa barci. Bata farka ba sai ƙarfe takwas da kwata kamar yadda ta saita alarm ɗin wayarta.

A gurguje tayi wanka, ta kimtsa cikin shirin makarantar islamiya tunda sai karfe tara da kwata suke fara karatu. A matsayinta na shugabar ɗalibai mata da suke makarantar shi yasa ba ta yarda tayi latti ko fashi idan ba da wata ƙwaƙƙwarar larura ba.

Bayan ta gama shiryawa jakar makarantarta ta ɗauka ta riƙe a hannu. Tana fita falo ta samu har Nauwara ita ma ta gama shirin makaranta. Tana zaune a ƙasan kafet kusa da kujerar da Daddy yake zaune, yana duba jarida tana mishi hira jefi jefi. Da alamun da safiyar ranar ya koma gidan, don jiya har suka yi barci bata ji dawowarsa ba. Fuskarta ne ya faɗaɗa da fara’ar ganinshi. Ta durƙusa har ƙasa ta gaishe shi a nutse, kuma cike da girmamawa.

Da fara’a ya amsa mata cike da kulawa, har yana tsokanarta.

“Kun ga shugabar ɗaliban gaba ɗaya makarantar Noorul Huda. Alsheikiya Hafiza Alarammiya Nana Khadeeja Khamis Abubakar. Ina gwanar wasu ga tawa? Gangaran ɗin mahaddaciya ce nan nake faɗa muku.”

“Na gode Daddy…”

Ta faɗa tana dariyar jin daɗi da farin ciki sosai na yadda kusan ko wane lokaci uban a fili yake nuna tsananin alfaharin da yake yi da ita.

Bata yi mamaki ba da bata ga Mommy a falon ba. Zaman doya da manja da ke tsakanin iyayen nasu har ya kai ga ba kasafai suka cika son haɗa inuwa ɗaya ba. Ba ma kamar Mummy, in dai Daddy na falon to za ta tattara duk abinda take buƙata ne ta shige cikin ɗakinta, ko kuma ta wuce kicin ta cigaba da ƴan aikace-aikacen da suke gabanta.

Har ɗaki ta bi Mummy tayi mata sannu da aiki. Sannan ta fito ta ƙarasa dinning table inda aka shirya abin karyawa. A gurguje ta bude flask ta haɗa ruwan shayi a ƙaramin kofi ta fara kurɓa a hankali, tana sha tana kallon agogo. Lokaci bayan lokaci kuma tana mayar da idanunta kan Nauwara da suke magana ƙasa-ƙasa ita da Daddy suna ƙyalƙyala dariya.

Tana gama shan shayin bata ƙara da komai ba duk da kayan ciye-ciye da suke kan teburin. Dama can ita bata cika cin abinci sosai da safe ba. Ta ɗauki jakarta tare da yiwa Nauwara magana ta tashi su tafi.

“Daddy sai mun dawo.”
Suka haɗa baki gurin faɗin haka.

Ya amsa musu da fara’a. Duk da makarantar babu nisa sosai Ɗari biyar ya basu kuɗin abin hawa kamar yadda ya saba. Nauwara ce ta karɓa, suka haɗa baki gurin yin godiya da addu’ar Allah ya ƙara buɗi. A gurguje suka leka ɗakin Mommy suka mata sallama kafin suka fice daga falon.

Yau dai kam ta ƙudirce a zuciyarta in dai Nauwara ta ƙi zuwa makaranta to tabbas sai ta faɗawa Daddy, ta gaji da ƙaryar da take sanyata tana narkawa malamansu a makaranta.

Ga mamakinta kuwa kamar Nauwarar ta san me ta ƙudurta a ranta sai ta ga ba ta da niyar zuwa ko’ina, kai tsaye suka shige ciki bayan mai keke napep ya sauke su a ƙofar makarantar.

Ko da suka shiga aji Mu’allim Sagir ya tambayeta dalilin rashin zuwanta makaranta a ƴan kwanakin, kanainayeshi tayi da ƙarya da gaskiya, har da rantsuwarta saboda tsabar ƙi faɗi da rashin sanin muhimmancin rantsuwa.

A dole Mu’allim ya ƙyale zancen ba tare da zurfafa bincike ko kuma ɗaukar wani mataki a kanta ba. Wannan abu ba ƙaramin ciwo yayi ma Mannira ba. Ta so ko horon wanke bayi a ba Nauwara, wataƙila hakan yasa ta rage fashin da take yi akai-akai, amma sai taga cikin ƙanƙanin lokaci ya watsar da maganar, har yana ce mata ta dinga yiwa Nauwara bitar littattafan da aka yi ranar da bata je ba.

Nauwara ta kasance yarinya mai tsananin wayau da iya taku da bi da mutane. Ta san yadda zata yi amfani da iya magana da kaifin harshen da Allah Ya hore mata ta sa mutane su bauta mata, da yarda da duk abinda ta ce ba tare da an tsananta bincike ba.

Shi yasa wani lokacin Mannira ba ta mamakin yadda duk tsananin sa idon Daddy har yanzu bai ramfo yadda take rayuwa irinta kura da fatar akuya ba. A zuciyarta tayi tsaki tana addu’ar Allah ya shiryi ƴar’uwar tata sannan ta mayar da hankali kan darasin da ake musu.

Ana tashinsu suka koma gida a tare. Tana ɗaukar wayarta da tun sadda za su fita ta saka a silent ta ajiye a gurin kayanta taga kiran da aka rasa na Muhsin har sau goma sha ɗaya, sai saƙonninshi na soyayya guda bakwai. Cike da zakwaɗi ta canza kayan makarantar da yake jikinta. Lallaɓawa tayi ta fita can bayan gida inda suke shanya ta danna mishi kira.

Ɓata lokaci tayi sosai a wajenshi suna hira har sai da aka kira sallar Azuhur kafin suka yi sallama da ƙyar, kamar baza su rabu ba.

Tana komawa cikin gida ta samu Mummy tsaye a tsakiyar falo, hannayenta biyu naɗe a ƙirji, ta kalleta cike da alamun tambaya da fuska mara walwala ta ce
“Daga ina kike? ina ta nemanki tun ɗazu ban ganki ba?”

Littafin da ke hannunta wanda daman ta tafi da shi ne saboda tsoron abinda zai je ya zo ta ɗaga ta nunawa Mummyn.

“Ina nan baya ina tilawar karatu ne. Kiyi haƙuri ban faɗa miki ba.”

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali.

“Shi kenan! Ki je kiyi sallah, idan kin idar ki kwashe min tuwo a kicin.”

“To Mummy.”

Ta amsa a ladabce. Sum-sum ta shige cikin ɗakinsu.

Nauwara tana kwance akan gado tana waya da murya ƙasa-ƙasa, tana ganin shigowar Mannira tayi saurin katse wayar ta jefa a ƙasan filo, alamar rashin gaskiya ƙarara a fuskarta.

Taɓe baki tayi ba tare da damuwa da yanayin Nauwara ba ta shige bayi don ɗauro alwala.

*****

Washegari litinin tunda suka yi sallar asuba su duka basu koma barci ba suka faɗa kicin don taya Mummy haɗa abin karyawa. Daddy na nan, duk da basa ga maciji a tsakaninsu idan yana nan abin karyawa na musamman ake shiryawa, ga kuma ƙannensu biyu Hafiz da Sadiya da suke tafiya abinci makaranta. Hannu da yawa maganin ƙazamar miya, duk da ƙarfin aikin Mannira da Mummy ne cikin ƙanƙanin lokaci suka gama komai, sannan suka wuce ɗakinsu domin yin shirin makaranta, har da Nauwara da take jami’a tana darasin safe, shi yasa shirin har da ita. Daman a ɓoyayyiyar ɗabi’arta ma ko da ba ta da darasin safe kullum za ta shirya ta fice da safe, har ranar da babu darasi ma ficewa take yi da cewar za suyi text, ko wani muhimmin abu a makaranta.

Bayan sun shirya babu ɓata lokaci suka fice zuwa falo domin karya kumallo. Yau kam har da Mommy, tunda Daddy har lokacin bai fito ba.

Suna tsakiyar karyawa ya fito ya shirya tsaf, da shirin fita.

Kai tsaye gurin teburin cin abincin ya nufa, idanunshi akan ƴaƴan da ako wane lokaci yake jin farin ciki idan ya tuna su ɗin fa mallakinsa ne halak – malak. Rige-rigen gaishe shi yaran suka fara yi, ita kuwa Mummy ko kallonshi bata yi ba ta miƙe tsam! Ta ɗauki kwanon farfesu da kofin tea ɗin da take sha ta nufi ɗakinta.

“Idan kun wuce Allah ya tsare, ya dawo da ku lafiya.”

Ta faɗi haka ga yaran a lokacin da take daf da shigewa cikin ɗakinta.

Cike da damuwa yaran gaba ɗaya suka bi ta da kallo, a sanyaye suka amsa mata. A bayyane take hatta Hafiz da yake autansu ba ya jin daɗin tsamar da ke tsakanin iyayen, kuma a kullum maimakon a dinga samun cigaba da daidaito ko ɗan ƙanƙani a’a, ƙara taɓarɓarewa yanayin zamantakewar nasu yake yi.

Duk yana lura da yanayin fuskokinsu. Zuciyarsa ne ta ɗan yi ƙunci, shi kanshi ba ya jin daɗin yadda yanayin zamantakewar nasu ya koma to amma ya zaiyi? Ta ko wane ɓangare Ziyada ta ƙi fahimtarsa, ta ƙi yi mishi uzuri ko kaɗan. Duk yadda a wasu lokutan shi da kanshi ya sakko yana lallaɓata ta ƙi bashi damar su shirya, ta faɗa mishi in dai yana son su daidaita to ya daina harkokin da yake yi. Shi kuma har yanzu bai shirya ma hakan ba, ya faɗa mata komai lokaci ne, wata rana ko an ce yayi bazai yi ba amma sam ta ƙi fahimtarsa, shi yasa shi ma ya tattarata ya ajiye gefe ɗaya. Ya cigaba da harkokinshi da ƴaƴanshi.

Bai zauna akan teburin cin abincin ba, can farfajiyar gidan ya fita ya umarci mai gadi ya goge mishi mota. Da alamu shi zai kai yaran makaranta.

Lura da haka yasa duk suka ƙara azama da sauri suka gama cin abinda zasu ci a gaggauce. Duk da Mummy ta yi musu sallama sai da suka leka suka sanar da ita tafiyarsu kafin suka fita gurin Daddyn da yake jiransu a jikin motarshi.

Nauwara ce a gaba kamar yadda aka saba, matukar fita za ayi in dai ba da Mommy bane, to ita ce a gaba.

Suka tsaya suka fara ajiye Hisham da Halima a tasu makarantar da yake bata da nisa da unguwar, kafin suka ɗauki hanyar makarantarsu Mannira da Mabruka, ko wane lokaci dama Nauwara ita ce ta ƙarshen saukewa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 30Lokaci 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×