Skip to content
Part 32 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Gaf da za’a sauke su Mannira a makaranta Nauwara ta juya tana kallon Daddy, fuskarta a kumbure, cike da shagwaɓa tana turo baki ta ce
“Daddy!! Har yanzu fa baka turo min 50k dinnan ba. Kuma ka ga har yau Monday.

Da mamaki sosai a fuskarsa ya juya a kaikaice yana kallonta, shi har ga Allah ya ma manta da wani batun kuɗi da tayi mishi tun ranar alhamis
“Nauwara? Wai ni duka-duka yaushe ne na tura miki kuɗi masu yawa da za su ishe ki buƙatu na yau da kullum? Me yasa ki ke da kashe-kashen kuɗi na banza da wofi ne? Idan wani muhimmin abu kike so ki faɗa min in siyo miki mana…”

A shagwaɓe sosai ta katse shi tana dire-diren ƙafa da jijjaga jiki kamar ƙaramar yarinya
“Allah Daddy ni fa amfani nake yi da su. Ka san dai haka kawai bazan dinga kashe kuɗi a banza da wofi don taƙamar kana bani ba. Yanzu haka kuɗin practical ne zamu bayar da na su hand outs. Tun last week duk ƴan ajinmu sun biya ni ce kawai ban biya ba. Bayan haka kuma ina da wasu ƙananun buƙatun da zanyi da kuɗi, kuma duk akan hidimar makaranta ne. Ka san jami’a ba kamar Sakandire bane kusan komai sai an ce mu biya kuɗi, wallahi a hakan ma ba komai nake cewa ka bani ba.”

Da yake ba sanin ta kan hidimar karatun jami’ar yayi ba, duk sadda ta buƙaci kuɗi ta fake da hidimar makaranta ko baiyi niyya ba da gaggawa yake ba ta. Ko kaɗan ba ya so ace ta nemi wani abu ta rasa, daga haka ne yarinya take fara ƴar murya tsakaninta da lakcarori.
“To shikenan Nauwara, bari in turo miki yanzu. Ni dai fatana shi ne kar ki kuskura wata buƙata ta makaranta ko ta buƙatun yau da kullum tasa ki ƙulla alaƙa da wani namiji da ban sani ba. Ki kula sosai da sosai, ba ke ɗaya ba, har ƙannenki su Mannira kuna ji na ko?”

“Eh Daddy!”
Suka amsa gaba ɗayansu.

“Yauwa! Samarin yanzu da kuke gani kaso casa’in da tara da ɗigo tara da za kuga suna yiwa ƴanmata hidima duk ba don Allah suke yi ba. Don haka ku kiyaye su. Ba ma kamar ke Nauwara da kike da farin jinin jama’a, ina ƙara jaddada miki abinda ya kai ki makarantar nan ki mayar da hankali kiyi, kar ki kuskura samari ƴan ƙarya da basu aje komai ba ko malamanku suyi miki barazana da faɗuwar jarabawa ki fara sakar musu fuska. Ko da wasa tsakanin malamai da ɗalibai duk wanda ya tunkaro ki da wata maganar banza kiyi gaggawar faɗa min. Ko waye shi a ƙasar nan kuma ko ɗan gidan uban waye zan ɗauki mataki a kanshi, kina ji na?”

“Eh Daddy”
Ta amsa da sanyin murya.

“Bari in tura miki da 70k”

Dariyar murna ta ƙyalƙyale da shi ta ƙara
“Thank you Daddy! I love you so much!! Allah ya ƙara buɗi na alkhairi.”

“Amin.”
Ya amsa yana ɗan murmushi.

A hankali ya ɗan juya yana kallon Mannirah da Mabruka ya ce
“Ku kuma fa? Babu abinda kike buƙata ne?”

A tare suka girgiza kai. Suka haɗa baki gurin faɗin
“Ba ma buƙatar komai Daddy. Allah ya ƙara buɗi.”

“Amin. Duk da haka dai zan tura ma Yayarku dubu goma. Idan kun zauna sai kuyi list na abubuwan da kuke buƙata ta siyo muku.”

Godiya suka sake yi mishi, ba wai don sun so ya tura ma Nauwara kuɗin ba. Don kuwa a ƙarshe dai wannan dubu goman duk zai zama Mallakin Nauwara ne. Sun san ko sama da ƙasa za su haɗe baza ta taɓa basu kuɗin ko ta siyo musu abinda suke so ba. Idan ana faɗin cinye du to Nauwara ce, duk yawan kuɗi a akawunta na banki cikin ƙanƙanin lokaci take ƙarar da su ba tare da sanin takamaimai abinda take yi da kuɗi ba.

Ire-iren abubuwan da take yi musu kenan da yake sanyawa a lokuta da dama suke jin haushin ƴar’uwar tasu. Gara ma ita Mabruka da take shekaru goma sha biyu har yanzu bata kai ƴanmata sosai ba.

Ita kuwa Mannira mai shekaru goma sha shida gab da cika sha bakwai tsiransu da Nauwara bai kai shekaru biyu ba, tana buƙatar duk wasu muhimman abubuwa na amfanin ƴa mace budurwa kamar yadda Nauwara ke buƙata.

Amma Nauwara ta cika son kanta da yawa, idan ba ita ne don ra’ayin kanta tayi niyyar ba su abu ba idan za su mutu su dawo baza ta basu ba. Kuma tun kafin ta kai haka, haka halinta yake.

Son kuɗi ne da ita na masifa, kuma idan ta samu ta kashe su a banza ce, ga shegen roƙo na fitar hayyaci. Haka za ka jiyota wajen su Aunty Ruqayya da Aunty Kareema yayun Mommy tana roƙon su mata abu ko wajen Uncle Yusuf Yayan Daddyn.

Da abin ya fara yawa ne Ziyada ta mata fata-fata sannan ta shiga taitayinta.
Roƙon sai ya koma jefi-jefi, kuma a ɓoye ba tare da sanin Mummy ba…

“Aunty Mannee tunanin me kike yi? Mun iso fa”
Mabruka ta faɗi haka tana ɗan girgiza ta.

Firgigit ta dawo daga zuzzurfan tunanin da ta faɗa, ko da ta kalli ɓangaren da take zaune sai ta ga har Daddy ya faka a ƙofar get ɗin makarantarsu. Da sauri ta sunkuci jakarta tana niyyar fita ya dakatar da ita.

“Tunanin me kike yi?”
Ya jefa mata tambayar fuskarsa ba walwala.

“Laaa… Babu komai Daddy.”
Ta faɗa da sauri tana zazzare idanu.
“Wani darasin lissafi da aka yi mana ranar juma’a mai bala’in wahala nake tuna misalan da aka bamu. Yau malamin ya ce zaiyi mana test akan darasin.”
Ta ƙara da faɗin haka sanin halinshi na bin diddigi kan abinda bai gamsu da shi ba.

“Ok! Ki dai rage zurfafa tunani irin wannan kar ki janyo ma kanki wani matsalar. Allah ya bada sa’a.”

“To Daddy! Zan kiyaye in Allah ya yarda. Amin”

Fita suka yi ita da ƴar’uwarta bayan sun yi ma Daddy da Nauwara sallama. Da sauri suka shige cikin makarantar don lokaci fara tare latti ya kusa, kuma tana cikin ɗalibai masu muƙami, idan suka kuskure hukuncinsu yana fin na sauran ɗalibai.

Cikin sa’a suna shiga ta hangi Fadila ita da Muhsin sun fito daga Ofishin Principal, lokaci ɗaya wani matsanancin farin ciki ya lulluɓe ta. Cak! Taja ta tsaya guri ɗaya tana jin yadda zuciyarta ke bugawa sauri-sauri, shauƙin soyayya na ɗibarta kamar taje ta ruƙunƙume shi saboda tsananin kewarsa da tayi. Daman yau ɗin ta tashi ne zuciyarta cike da kewa da tunaninsa.

Ko da ta ɗaga ƙafarta a hankali tana ƙarasawa gare su su ma suna nufo ta kamar za ta ƙarasa gurin Muhsin ta rungume shi sai ta zame ta wuce wajen Fadila ta rungumeta.

A sace ta kalli Muhsin da ya tsaya kamar mutum-mutumi yana kallonsu ta kanne mishi idanu tana jifanshi da wani lallausan murmushin soyayya.

Da farko ɗan ɓata fuska yayi yana mata magana da ido kan yadda ta nuna kewar Fadila shi bata nuna tana kewarshi ba, sai kuma ya mayar mata da martanin murmushi tare da buɗe baki a hankali kuma ƙasa-ƙasa sosai ya ce
“Good morning love”

Murmushi ta ƙara sakar mishi a karo na biyu, ta amsa gaisuwarsa a hankali sannan ta ja hannun Fadila da sauri suka shige cikin makaranta ganin wani malami ya nufo inda suke tsaye.

*****

Itama Nauwara, a ƙofar makarantarsu ya ajiyeta, a lokacin ne kuma ya ɗauki wayarsa ya tura mata kuɗaɗen da yayi alƙawari. Sosai ya ƙara ƙwanƙwasar kanta da zancen duk wani buƙata nata kar ta tunkari kowa ta tunkaro shi.

Ta ɗaukar mishi alƙawarin ta ji ta gani, za ta kiyaye in Allah ya yarda.

Ya tsaye a ƙofar makarantar yana kallonta har ta shiga ciki, sannan ya tashi motar ya fige ta a guje ya bar gurin.

Tana maƙale a ciki tana leƙensa, sai da ta tabbatar ya wuce sannan ta shige cikin makarantar, kai tsaye ofishin D. G ta nufa maimakon ajin ɗaukar karatu kamar yanda taga sauran abokan karatunta suna yi.

“Nauwara sai ina? Minti biyar fa ya rage a shiga lecture.”
Ƙawarta Nailah ta tambayeta lokacin da take daf da shigewa Ofishin.

“Yanzu zan fito. Saƙo Daddy ya bani in miƙa ma D.G. Ki je ga ninan ƙarasowa.”

Tana shiga ofis ɗin babu kowa a ɗan ɗakin da Secretary ɗin shi take zaune don yi ma mutane ison ganawa da shi, don haka kai tsaye ta tura ƙofar ofis ɗin ta shige ciki tare da maida ƙofar ta rufe ta ciki.

A fusace ya ɗaga kai daga kallon laptop ɗin da yake dannawa don ganin waye ya mishi shigan burtu ba tare da neman izini ba? Murmushi ne ya maye gurbin fushin lokacin da yayi arba da kyakkyawar fuskarta.
“My baby girl! Har kin shigo kenan?”

Kujeran da ke fuskantar teburinsa ta ja ta zauna tana kallonshi cikin ido. Martanin murmushinshi ta fara mayar mishi, kafin ta amsa da
“Eh wallahi, zuwa na kenan. Sannu da aiki. Na zaƙu in ji ya ake ciki? Shi yasa kai tsaye nayo nan don jin inda aka kwana.”

Laptop ɗin hannunshi ya juya mata don ta duba aikin da yake yi, ƙura idanu tayi da kyau, sai taga sakamakonta na exams ɗin da suka yi ne yake aiki akai. Duk wani course da bata ci ba wanda daga farko D ne da F, duk an canza mata su da A+ da AB.

Lokaci ɗaya ta saki lallausan murmushi.
‘Tsananin munin da sakamakonta yayi a wannan karon ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba. Dai-dai gwargwado a baya tana da ƙoƙari sosai, amma tsananin shiriritar da ta saka a gaba da haɗuwa da wasu ƴan iskan ƙawayenta uku yasa ta zama daƙiƙiyar ƙarfi da yaji. Sam ba ta karatu ko kaɗan, ba ta shiga aji sai taga dama.

Ganin yadda hankalinta ya tashi sosai da ganin sakamakon yasa ƙawayenta suka buɗe mata ƙofar cin nasararsu. Ƙarara suka faɗa mata faɗuwa jarabawa a jami’a sai dai idan ita ta so.

Kamar yadda lakcarorin suke faɗar da ɗalibi ko ɗaliba da gangar haka za su bata maki mai kyau in dai za ta basu abinda suke so. Da yake daman kamar ƙiris take jira, mafita take nema ta yadda Daddy bazai taɓa gane ba karatu take yi ba. Ba tare da wani ja’inja ba ta fara gwada bin hanyar da suka nuna mata, sai taga kaso saba’in cikin ɗari tana samun yadda take so.

Kaso talatin na Malaman da suka ƙi bata haɗin kai saboda tsantseni da gaskiyarsu sai ta bi ta hannun D. G da ya kasance kamar bunsuru. Idanunshi idon kyakkyawar mace kuma ɗanya shataf, to kamar raƙumi da akala haka za ta dinga juya shi ta hanyar aikata duk abinda take so ita kuma tana ba shi abinda yake so.’

A karo na barkatai ta sake sakin murmushi, zuciyarta cike da gamsuwa na yadda mummunan sakamakon ya koma mai tsananin kyau abin alfaharin ko wace ɗaliba.
“Hakan yayi Sweety na. Lallai ka cancanci gwaggwaɓar sakamako.”

“Na gode my baby girl. Girmanki ne ai. Yanzu me zan samu?”
Ya ƙarasa tambayar haɗe da kashe mata ido ɗaya kamar ƙaramin yaro.

Fari tayi da idanu sannan ta ce
“Bani lambar akawun ɗin ka in saka maka na shan ruwa”

Dariya ya kwashe da ita ya fara karanto mata tana rubutawa a wayarta. Nan take ta tura mishi dubu arba’in.

“Wawww! Babbar yarinya, sun shigo Baby girl. Shi yasa nake bala’in son ki.”

Ta jinjina kai, da yanayin jin daɗi da alfahari ta ce
“Good. Barin tafi aji.”

Yayi saurin tashi tsaye yana dakatar da ita, ɓata fuska yayi kamar wani matashi bayan ya yi sa’ar kakanta ya ce
“Haba Sweet baby! Ke fa nake jira tun ɗazu, kin barni da aikin gyaran sakamakonki tsawon kwanaki biyu yanzu kuma kina so ki sake bari na cikin kewa? Tun wancan satin fa sai yawo da hankali kike min kina ja na a ƙasa, yanzu ma kuma ƙwalele za ki sake yi min?”

Ɗan yamutsa fuska tayi alamun ba haka ta so ba, amma da ta tuna ƙoƙarin da yake mata sai ta ce
“Muna da lecture da safennan, amma na baka minti goma.”

Da sauri ya kama hannunta jikinshi na rawa ya ja ta zuwa ciki yana cewa
“Na yarda! A hakan ma na gode”

Daga mintuna goma ba ita ta fita daga ofis ɗin ba sai bayan mintuna talatin. Tana fita ta samu Sakatariyarshi ta dawo, faram-faram suka gaisa da ita, Nauwara har da ɗaukar dubu biyu ta bata tace ta sayawa yara alewa.

Da fara’a sosai ta amsa tana godiya. Nauwara na fita ta bita da kallo cikin harara, a zuciyarta take Allah wadai da mummunar ɗabi’an wasu ƴanmatan na wannan zamani. Ta ƙara da jan tsaki ƙasa-ƙasa tana kwashe ma D.G albarka da ya zama tsohon najadu.

Ajinsu da suke ɗaukar darasi ta shiga. Tana shiga duk ɗaliban ajin suka zuba mata idanu, Malamin da ke musu darasi a lokacin Malam Khalid, ya juya yana kallonta fuska a haɗe tamau ya ce
“Malama daga ina?”

Tana kwarkwasa da juya jiki ta ce mishi daga clinic take, ba ta jin dadi.

Ya san ƙarya take yi, tunda ba ranar ta saba haka ba. Da da ne korarta zai yi daga cikin ajin kamar yadda ya saba ga duk ɗalibin da ya riga shiga cikin aji.

Yana ɗa ya daga cikin ɗaiɗaikun Malamai da kuɗi ko surar mace ba sa ruɗarsu balle a juya su yadda ake so.

To shima tunda D. G ya kira shi satin da ya wuce ya mishi gargaɗi na ƙarshe a kan ya bata F a course ɗinshi da yanda yake yawan hantararta idan tayi latti jikinshi yayi sanyi, don kuwa aikin shi ne gatanshi da na iyayenshi. Idan ya rasa shi bai san ya zai yi ba.

Ya ga manyan makaranta ma basu damu da abinda take yi ba, ina ga shi ɗan karere? Don haka yace mata taje ta zauna amma ya mata kashedi na karshe.

Ta yi wucewarta cikin kawayenta ta zauna.
Rabin yan ajin sunyi mamakin hakan, duk sunyi zaton korata zai yi kamar yadda yake yi. Ransu duk bai so ba, sai harara suke ta jefa mata cike da tsana ita kuwa ko a jikinta. Wayarta ma take dannawa sam hankalinta baya kan malamin balle darasin da yake gabatarwa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 31Lokaci 33 >>

2 thoughts on “Lokaci 32”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×