Skip to content
Part 33 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Fitowarshi kenan daga banɗakin hotel ɗin da ya yini a ɓagas ba tare da ya kashe ko sisin kwabo ba. Babban tawul ne ɗaure a ƙugunshi, wani ƙaramin tawul ɗin kuma yana riƙe a hannunshi yana goge ruwan da ke ɗiga a kanshi zuwa fuska da kafaɗarshi.

Kwance akan makeken gadon da ya mamaye fiye da rabin ɗakin, Kankana ce. Kwance take shame-shame haihuwar gyatumarta, idanunta ƙur akan Khamis tana ƙare ma ƙirar jikinshi kallo.

‘Shege Kham ya san sirrin gyaran jiki. Yadda wankan tarwaɗar fatarshi ke sheƙi da laushi a hannu ko na wata ƴa macen albarka.’

Ta faɗi maganganun a zuciyarta.

“Hey kallon fa? Ko na canza miki daga wanda kika sani ne?”

Ya jefa mata tambayar yana ɗan murmusawa.

Fari tayi da idanunta sannan ta watsa mishi wani kallo mai bayyana tsananin ƙwarewarta a iskanci da gogayya da maza kala daban-daban.

“Ba komai fa. Kawai dai mamaki nake yi na yadda har yanzu fatar jikinka bata fara sauyawa ba. A kullum muka haɗu sai inga kamar ana ƙara maka yarinta ne da gayu…”

Dariyar da ya kwashe da ita ya hana ta ajiye numfashin maganar dai-dai.

Bayan gama dariyar bai ce komai ba, gyaɗa kai yayi ya ƙarasa inda kayanshi ke ajiye ya saki duka tawul biyun da suke jikinsa a ƙasa. Ba tare da kunyar idanunta ba ya ɗauki kayanshi ya fara sakawa ɗaya bayan ɗaya.

Tana kallonshi har ya kusa gama shiryawa bata ce mishi komai ba.

Yana ɗaura agogo a tsintsiyar hannunshi ya kalleta cike da kulawa ya ce,

“Kankana kin sanni na sanki, kuma kin san sanin da nayi miki ba sanin shanu bane balle ki ninke ni a baibai. Tun shigowata ɗakinnan na lura magana ce fal a bakinki. Ke ɗin misalin Ungulu ce da ba ta jelar banza. Me ne ne? Kin kira ni na amsa kira tun safe, ki faɗa min ko menene kuma kin tsaya kina ta kwana-kwana?

Ni zan wuce ne, yanzu ba kamar da bane. Idan kin san lokaci za ki ƙara ɓata min gara in san inda dare yayi min, a yanzu babu abinda nake mutuntawa ina tattalawa sama da Lokacina.”

Tsam! ta miƙe zaune daga kwamcen da take, sai karkaɗa shafaffun na shanunta da gaba ɗaya suka yi ruku’u take yi.

Shi abin ma dariya ya bashi, don haka ya kawar da kai yana ɗan murmusawa cikin basarwa. Lallai ya ƙara yarda tafiyar rayuwa irin ta ƴa mace ba ɗaya ne da na ɗa namiji ba. Dubi dai Samira, kamar ba ita ce dirarriya kuma cikakkiyar budurwarnan da manyan masu kuɗi da ƴan siyasa suke rububi a shekarun baya ba.

Gaba ɗayanta tayi wani irin yaushi kamar ganyen da ya kwana biyu babu ruwa, shi idan ma ba idanunshi ne ke gizo ba sai yaga kamar ta fara komaɗewa.

Yana da labarin halin da take ciki A to Z ta bakin ƙawarta. Ya san wannan yanƙwanewar da ta fara yi ba ya rasa nasaba da rashin hada-hadar ƴan canji a hannunta kamar da.

Amma dai wannan ba matsalarshi bane tata ce. Shi yanzu babban takaicinshi ma yadda ta sa shi ya wuni a banza ba tare da ya sharɓi romon da ya saba sharɓa daga gare ta ba. Kamar ba Samira wacce shi da kanshi ya raɗa ma suna kankana saboda tsabar ni’imar da Allah ya zuba a jikinta? Shi ji yake ma duk ta gama ɓata mishi lokaci, sai ya ji dama bai amsa kiran da tayi mishi ba balle ya amsa goron gayyatar da ita da kanta ta fara miƙo mishi. Shi fa kwata-kwata ma bai fahimci me suka yi ba, sam bai samu ko kwatan abinda ya zata zai samu ba…

“Kai ma dai ka san banza ba ta kai zomo kasuwa Kham!”

Ta katse mishi tunani da faɗin haka, muryarta ƙasa-ƙasa.

Bargon da ke ajiye akan gadon ta yayumo ta ɗan sakaya jikinta ganin yadda yake ƙare mata kallo ba tare da nuna shauƙi ko misƙala zarrah ba.

Gyara yanayin fuskarta tayi, yanayin da ke nuna za tayi magana ne mai muhimmanci. Idanunta cikin na shi ta ce,

“Ka san dai haka kawai ba zan kama ɗakin hotel mai kyau da tsada da kuɗina, in ƙona katin waya in kira ka, in ciyar da kai abinci mai tsada, ka more ni a ɓagas, kuma kayi tunanin cewa babu wani dalilin da yasa na aikata hakan ba.”

Wata yar dariya yayi da ke nuna zallar rainin wayau, kafin ya amsa mata da
“kwarai kuwa na san da hakan. Ai sanin hali ya fi sanin kama. To yanzu dai da wacce kike tafe ne? Saɓewa zan da mun gama magana.”

Sannu a hankali ta gyara zama, ta buga tagumi da hannu ɗaya

“Kham ka san dai ni da kaina ban taɓa neman wani taimako a wajenka ba, sai dai kai ka nema, kuma baka taɓa rasawa ba idan kayi hakan. To yau dai so nake ka ramawa kura aniyarta. Ka san yanzu yanayin garin ya ɗan canza ba kamar da ba. So nake yi don Allah ka taimake ni ka sama min lafiyayyar hanya, kuma bango majingini. Harkokin sun fara lafawa, Allah ya sanj ni kaina na fara gajiya da wannan yawace-yawacen na ba gaira ba sabab, abin ya fara isa ta.

Ka ga idan ka samar min wani babban kifi ko ƙusar gwamnati ko ɗan siyasa ko ɗan kasuwa, idan Allah ya taimakeni ya yankewa kakata saƙa sai ka ga yayi wuff da ni, in shige cikin gidanshi ko a ta huɗu ne in rufa ma kaina asiri. Idan kayi haka ko banza dai karo na farko a tarihin rayuwwrka za ka samu gwaggwaɓar lada na zamowa sanadiyyar haɗa sunnar ma’aiki ba sanadiyyar haɗa aikin alfasha ba…”

A wannan karon, duk yadda yaso mayar da dariyarsa ya kasa. Wata mahaukaciyar dariya ce ta kuɓce mishi, duk yadda ya so ya cije kasawa yayi sai da ya saketa, ya dinga ƙyaƙyatawa yana nuna Samira da yatsarsa manuniya kamar wani tsohon mahaukaci.

Tun tana cijewa ta tsaya ta ga iya gudun ruwanshi har sai da ta fara ƙulewa, ta galla mishi wata mahaukaciyar harara, ta ja doguwar tsaki tana girgiza ƙafafu alamu na kaiwa ƙololuwa a fusata.

Duk da haka bai daina ƙyaƙyata dariya yana nuna ta ba. Da haushin ya ƙara turnuƙeta waige-waige ta fara yi tana neman abinda za ta jefe shi da shi, daga ƙarshe da taga ba komai a kusa da ita sai jakarta da ke ajiye kan durowar gefen gado shi ta ɗauka ta jefa mishi, kuma cikin sa’a ta same shi a kafaɗa. Lokaci ɗaya kuma ta fashe da kuka irin mai cin rannan.

“Ni Khamis? Yanzu ni ce na zama wulaƙantacciya abar yasarwa a gare ka har za kana min dariya sai ka ce ka ga mahaukaciya ko? Ashe daman aminci da soyayyar da ke tsakaninmu na ƙarya ne tunda baza ka iya taimaka min a lokacin da nake tsananin buƙatar taimako ba ko?”

Ganin irin kukan da take yi ne da maganganun da take furtawa yasa daƙyar yayi ƙarfin halin tsayar da dariyar. Yasa babbar yatsarsa ya ɗauke hawayen da suka taru a idanunshi saboda dariya.

“Yi haƙuri. Allah ya huci zuciyarki Kankana uwar ruwa tawa ni na Allah. Allah ya baki haƙuri. Maganar ce tazo min a bazata shi yasa, da kuma cewar da kikai in samu ladar haɗa aure a karo na farko, waɗannan jimlolin ne kawai suka ba ni dariya. Waye ni da zan zauna ina ɓaɓɓakama babbar yarinya kamar ki dariya. Ke ce fa Kankana uwar ruwa wacce har gobe babu shegen ɗan barikin da ya isa ya ce ya daina yayinki. Ke ce fa ƴar barikin da ba ko wane kare da doki take kulawa ba, ke ce fa Karuwannan da a mafi yawancin lokuta idan ba’ayi apointment da ke ba duk kuɗin ƙwaro ba kya taɓa amsa gayyatarsa. Ko kin manta kirarin naki ne in tuna miki?”

Tun da ya fara maganganun da suke sauka a jikinta kamar allurar soja, kanta ya fara kumbura yana faɗi har tana ji kamar zai fi ƙarfin gangar jikinta. Ɗif! ta tsaya da kukan da take yi kamar ɗaukewar ruwan sama. Sai ɗan mirgina kai gefe da gefe take yi don rage nauyin da kan yayi mata, a fuskarta tana sakin wani lallausan murmushi.

Kujerar da ke ajiye gaban madubi ya ɗauka zuwa kusa da ita ya zauna. Suka fuskanci juna, fuskarshi da ɗan murmushi cakuɗe da tausayi-tausayinta da ya fara ji. Ita kuwa da murmushin da ke nuna jin daɗinta a fili, na yadda ya tunatar da ita har yanzu fa ana yayinta, kuma ita ce dai Samira Kankana yarinya mai aji da gwalli, ba wata aka canja ba.

“Yanzu dai faɗa min. Kamar wa kike so a haɗa ki da shi?”
Ya katse shirun da ke tsakaninsu ta hanyar jefa mata tambayar.

Tayi ɗan jim cikin tunani, can kuma sai ta ce,

“Matashi dai ɗanyen jini yaro da kuɗi kamar Salim, ɗan gidan Alhaji Kanta. Kai ko shi ɗin ma ka haɗa ni da shi normal ne, ni zanyi yadda zanyi cikin ƙwarewata da juya akalar namiji duk taurin kansa in shiga jikinshi. Kuma na maka alƙawarin zan yi maka biya mai tsoka bayan wanda na san shi ma zai yi maka.”

Wani birkitaccen kallon ba ma ki da hankali yayi mata. Shi da ma yasan tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi!

‘Shekarun da suka gabata, Salim Kanta wanda ya karɓi budurcin Rahma kuma ya cigaba da ƙwaƙwa yana biyayarta tun wancan lokacin. Yanzu haka ya dawo Nigeria da zama, ya gama karatunsa acan ƙasar waje ya dawo gida.

Bayan mahaukacin dukiyar da ubanshi ya sakar mishi shi kanshi yana da manyan harkokin da yake yi da suke shigo mishi da mahaukatan kuɗaɗe. Domin yanzu haka takarar kujerar Gwamnan Kaduna yake yi, kuma ga dukkan alamu zai haye saboda matashine mai jini a jika, ga kuɗi ga ilimi. Kuma sananniyar fuskar da mutane suka sanshi da ita ta taimakawa matasa ne da gajiyayyu, domin anyi ittifaki a fagen aikin alkhairi da taimakawa masu buƙatar taimako ya dame mahaifinshi ya shanye. Don haka yin shi jama’a suke yi ƙwarai da gaske.

Da yake ɗan halak ne, tun bayan rabuwarsu da Rahma a wancan shekarun bai ƙyaleta ba, lura da shi ne mutum na farko da ya fara ɓata mata rayuwa. Bayan magana da suke yi a waya yana aika mata da maƙudan kuɗaɗe, masu gadi ya zuba ba tare da ita kanta ta sani ba suna lura mishi da shige da ficenta, rahoto suke kai mishi na ta adana kanta wa shi kaɗai kawai ko kuwa ta cigaba da yawon banza?

Labari mai daɗi da yake samu na yadda take a kame guri ɗaya yasa duk sadda yazo Najeriya yana tare da ita. Ba ya ƙyashin kashe mata ko nawa ta buƙata, bayan manyan kyautuka da yake mata na abubuwa masu tsadar gaske.

Sosai da sosai ya sanyata a cikin ni’imar rayuwa. Kai da likkafa ma ta ci gaba sai da ya ɗauketa ya kai ta can ƙasar da yake karatu, satinta uku ta dawo gida nigeria da dukiya mai ɗumbin yawa.

Tun wannan zuwan da tayi gabaɗaya sai rayuwarta ta ƙara canza, tayi wani irin kyau ta kile, ta zama babbar yarinya mai aji na gasken-gaske. Jikinnan nata luwai-luwai, ta ƙara jajur, kamar a taɓa ta jini ya tsillo don tsananin yadda hutu ya nuna a jikinta. Ga iya kwalliya da ƙwainane da bala’in yanga kamar ƴar gidan shugaban ƙasa.

Tanƙamemen gida a Unguwar rimi GRA Salim ya siya ya mallaka ma Iyallu da sunanta halak-malak! Bayan sun je har gida ya gaishe ta, Rahma kuma ta ƙara kankaro mishi kima da mutunci bayan ta shirga ma Iyallu ƙaryar ai Salim ɗin shi ne wanda ta daɗe tana burin haɗuwa da shi.

Shi ne wanda ya taimaka ya biya kuɗin aikin da aka yi mata lokacin da take gaɓar mutuwa. Shi ne ya zama ja gaba gurin kama hannunta a hankali yana saka ta a harkokin sana’a har zuwa yanzu da ya tsamo su gaba ɗaya daga ƙangin talauci.

Iyallu ta yi godiya, ta saka albarka, ta yi mishi addu’o’i har ta rasa me za ta furta, daga ƙarshe ma sai ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka lokacin da ya miƙa mata takardun gidan. Idan ta tuna matsanancin ƙangin rayuwa da suka shiga a baya rabi-rabin wannan ni’imar ko a mafarki bata taɓa hasaso za su shiga cikinta ba.

Ficewa yayi ya barta kamar mutum-mutumi bayan ya faɗa mata su shirya tarewa kwanaki biyu masu zuwa. Kuma ko tsinke ba ya buƙatar su tafi da shi sabon gida.
A yanzu haka cikin sabon danƙareren gidan suke rayuwa suna cin karensu babu babbaka. Islamiyya mai kyau ta ƴaƴan gayu ƴaƴan masu kuɗi ya nema ya saka Rahma, a cewarsa takardun karatunta na boko iya sakandire sun gamsar da shi.

“Sai hali ya zo ɗaya ake abota”
Wannan kalma ɗaya ce daga cikin sanannun karin maganar Malam bahaushe. Amma a wannan ɓangaren an samu akasin haka.

A maimakon Samira ta kwantar da kai ta ci arzikin Rahma kamar yadda da can ita Rahmar ta kwantar da kai take cin arzikinta. Ƙarara take jin haushi da ƙyashin irin ni’imar da Rahma ke ciki, a mafiyawancin lokuta har cizon yatsa take yi kan wai ita wani karen hauka ne ma ya cije ta yasa tayi ma Rahma hanyar irin sana’ar da take yi?

Duk yadda ta dinga zuge Rahma da maganganun ƙage da ƙarerayi kan ta rabu da Salim, ta daina biye mishi ya mayar da ita karuwarshi ita kaɗai. Duniya faɗi ne da ita, a cikin gaggan matasa masu arziki Salim ba kowan-kowa bane sam! Rahma ta yi kunnen uwar shegu da maganganun.

Daga ƙarshe ma da suka bar unguwar sai ya zama ko a waya ba ta samun Rahma, in dai ba ita Samirar ce tayi takakkiya zuwa gidansu ba ita Rahma ta daina zuwa gidansu.

“Kiyi haƙuri Ƙawalli, wallahi ban manta da ke ba. Kin ga ni yanzu na koma makaranta, Islamiya ta ɗau zafi, ko waya ba kasafai nake riƙewa ba.”
Amsar da Rahma take ba ta kenan duk sadda ta fara mata mitar ta buɗa mata hanyar samun kuɗi amma ta yasar da ita.

Shi kuwa Khamis, da yake tsuntsu ne mai wayau. Tuni ya hango gaggarumin hadarin da zai iya zubar da gagarumin ruwa a taraiyar Rahma da Alhaji Salim, kamar yadda yake kiransa. Don haka ya kwantar da kai ƙasa sosai yana sharɓan romon democraɗiyya a gurin Salim. A gidansu Rahma gurin Iyallu kuwa tuni ya zama ɗan gidan, gabatarwa da Iyallu shi tayi a matsayin wanda yayi mata hanyar haɗuwa da Mai taimako, kamar yadda Iyallu ke kiran Salim.

Sannu a hankali Samira tayi zuciya ta fita daga hanyar Rahma, ita daman Rahma tuni ta shafe babinta a rayuwarta. Hankalinta bai ƙara tashi ba sai da taga kalanda da hoton Salim yana takarar gwamna, kuma taga yadda ake tsananin ƙaunarsa. Ko da ta bincika sai ta samu labarin har lokacin yana tare da Rahma yana hidimta mata.

Nan ta sha alwashin sai tayi duk yadda zata yi ta raba su ita ta maye gurbin Rahma, kai idan ma bata maye gurbin Rahma ma ba dai, ita dai ta raba su shi ne babban burinta.

Da fari Malamai ta fara shiga, manyan malamai da suka shahara da sunan aikinsu kamar yankan wuƙa, da taimakon Uwar ƙungiyarsu ta neman jinsi. Bata ankara ɓarnar kuɗinta take yi a banza ba sai suka ƙarasa cinye maƙudan kuɗaɗen da suke akawun ɗinta guda uku.

Daga baya dai da taga babu mafita da hanya mai ɓullewa ta wajensu, sai ta yanke shawarar kawai ta bi ta hanyar Kham. Ta san ko bai haɗa ta da Malaminshi ba shi kanshi malamin kanshi ne. A sadda suke tare bai taɓa faɗin abu taga akasin haka ba. Ta san yana tsananin son tarayya da ita, idan ta ɓata lokaci ta jiyar da shi matsanancin daɗi bazai ɓata lokaci gurin yi mata abinda take so ba.

Khamis ne ya zaɓawa Rahma ranar Laraba matsayin tabawa ranar samu, kuma da ta tashi samowa ta samo tsayayyen namiji irin Salim. Za ta kwantar da kai ta kalallame shi don wata kusan ai ta fi wata, kafin Rahma ita ya fara sani, kuma yadda za ta sakar mishi arziki ya ci Rahma baza ta taɓa sakar mishi haka ba. Don haka ko ana ha maza ha mata gara ya ture gwamnatin Rahma a zuciyar Salim ya kafa na ta.’

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 32Lokaci 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×