Fitowarshi kenan daga banɗakin hotel ɗin da ya yini a ɓagas ba tare da ya kashe ko sisin kwabo ba. Babban tawul ne ɗaure a ƙugunshi, wani ƙaramin tawul ɗin kuma yana riƙe a hannunshi yana goge ruwan da ke ɗiga a kanshi zuwa fuska da kafaɗarshi.
Kwance akan makeken gadon da ya mamaye fiye da rabin ɗakin, Kankana ce. Kwance take shame-shame haihuwar gyatumarta, idanunta ƙur akan Khamis tana ƙare ma ƙirar jikinshi kallo.
'Shege Kham ya san sirrin gyaran jiki. Yadda wankan tarwaɗar fatarshi ke sheƙi da laushi a hannu ko na. . .