Misalin ƙarfe sha uku da rabi na rana Nauwara ta shiga cikin gidan cin abincin A&M da ke kallon makarantarsu. Ƙayataccen wajen cin abinci ne da ya zama matattara ta 'yan gayu da wayayyun mutane, musamman matasa masu ji da kansu da ƴaƴan masu hannu da shuni.
"Idan kin isa"
Kirarin da wasu matasa ke yiwa wajen cin abincin kenan saboda tsadar kayayyaki a gurin. In dai ba yaro ko yarinya na da wadataccen guzuri ba ɗan tattalin arzikinki rankatakaf za ki ƙarar da shi a gurin, da cin abinci na kwanaki uku kacal.
Tana shiga tayi. . .