Skip to content
Part 35 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Misalin ƙarfe sha uku da rabi na rana Nauwara ta shiga cikin gidan cin abincin A&M da ke kallon makarantarsu. Ƙayataccen wajen cin abinci ne da ya zama matattara ta ‘yan gayu da wayayyun mutane, musamman matasa masu ji da kansu da ƴaƴan masu hannu da shuni.

“Idan kin isa”

Kirarin da wasu matasa ke yiwa wajen cin abincin kenan saboda tsadar kayayyaki a gurin. In dai ba yaro ko yarinya na da wadataccen guzuri ba ɗan tattalin arzikinki rankatakaf za ki ƙarar da shi a gurin, da cin abinci na kwanaki uku kacal.

Tana shiga tayi gam da katar, haɗuwa tayi da Aminiyarta Amina da suka daɗe basu haɗu ba.

‘Asalin haɗuwarsu da Amina a facebook ne, da hira tayi hira a tsakaninsu sai suka gane duk su biyun ƴan gari ɗaya ne. Wannan shi ne mafarin shaƙuwarsu a media. Lura da yadda rawar kai da son gwallinsu ya zo ɗaya, yasa duk group ɗin da Aminar ke ciki tayi magana wa admins aka yi adding ɗin Nauwara a ciki. Saboda ita Amina ta kwana biyu da fara harkar social media ita kuma Nauwara sabon shiga ce.

Kasancewarta baƙuwar shiga yanar gizo ce yasa Amina bata sha wahala ba wajen tsunduma Nauwara cikin duniyar chatting ɗin banza da samari ƴan bana bakwai.

Daman a lokacin tana ganiyar rawar kai da jin itama fa ta kai wata haɗaɗɗiyar budurwa, Duk da account ɗinta na facebook ba asalin sunanta bane amma hoton da ta ɗora asalin hotonta ne. Sai abin ya haɗe mata biyu, ga tashen budurci tana cikin shekara sha huɗu sha biyar, ga matasa ƴan bana bakwai ƴan ƙarya da suke ta bin hotunanta da Waw, waw, waw! suna cika mata inbox da saƙonnin soyayya. Tun tana sharewa tana ɗauke kai da zugar Amina har ta fara saurarensu, har ya zamana tana ɗaukar hotunanta da wasu sassa na jikinta suka ɗan fito tana tura ma samarin da ta aminta da zaƙaƙan kalamansu, su kuma suna cigaba da kururutata da kalaman da suka lura ta fi so, a haka har ta dulmiya ta yi nisa sosai a rayuwar da babu wanda ya taɓa ramfo ta a gidansu.

Amina ita ta haɗata da saurayin da ya taka muhimmiyar rawa gurin ƙarasa canza mata rayuwa gaba-ɗaya. Domin tun suna chatting kaɗai, suka koma yin waya a ɓoye da musayar saƙonni ba tare da iyayenta sun ankara ba.

Har suka kai matakin da yasa tsananin son ta da yake yi da yadda yake ji bazai iya ci gaba da rayuwa ba tare da sun haɗu ido da ido ba yasa shi tasowa takanas-ta kano tun daga garin Abuja inda yake zaune da iyayenshi, har zuwa Kaduna gurin Nauwara.

Da farko hankalinta ya tashi sosai da jin ga shi a garin kaduna. Ta san dai ko giyar wake take sha bata isa ta kawo shi gidansu ba, bisa shawarar Amina ta tsaida ƙaryar da za ta faɗa ma Mummy ta fita ba tare da an hana ta ba. Babbar sa’ar da ta taka a lokacin shi ne mahaifinta ba ya nan, ta gilla ma Mummy ƙaryar za suyi haɗakar zuwa dubiyar malamarsu ita da sauran ƴan Ajinsu, karo na farko da Amina ta fara zuwa gidansu a lokacin, ta je da matsayin ƴar ajinsu Nauwara ne za su biya ma sauran ƙawayen daga can za su wuce gidan malamarsu.

Da yanayin ɓacin rai da rashin kwanciyar hankali a fuskar Mummy ta kirtawa Nauwara kashaidi gaf da za su bar gidan.

“Nauwara kar ki kuskura ki daɗe fa, kin dai san halin Daddynku baya son irin waɗannan gaishe-gaishen. Ki dawo da wuri. In banda ma an biyo miki wallahi babu inda za ki je.”

“To Mummy. In Allah ya yarda baza mu daɗe ba.”

Su biyun suka amsa kashaidin a ladabce. Suka fice da zumbula-zumbulan hijabansu har yana share ƙasa, kamar da gaske dubiyar za su je.

Suna fita daga gidan suka yi canjen ƙananun hijabai, suka ɗaura niƙaf don ɓadda kama. Suka tari a daidaita sahu har zuwa gidan Abokin Habib ɗin, inda ya sanar da su yayi masauki. Shi daman Abdul mai masaukin Habib saurayin Amina ne, don haka ko da suka je gidan ko wanne a cikin samarin budurwarshi yaja suka shige cikin ɗaki, har suna yi ma junansu tsiyar hira tsakanin budurwa da saurayi babban sirri ne tsakanin zukata biyu, idan ba dole ba ko ƙuda ba’a so ya ji zaƙaƙan kalaman da za’a furta ma juna balle har ya kwasa zuwa gaba.

Hadith ne ingantacce a duk sa’ilin da namiji da mace suka keɓe na ukunsu shaiɗan ne, a wannan haɗuwar bayan ƴan wasanni da daɗin bakin baza’a zarce haka ba har mai aukuwa ta auku, inda Habib yayi nasarar amshe budurcin Nauwara ba tare da duk su biyun sun ankara ba, bayan ya kai matakin da bazai iya dakatar da kanshi ba ita kuma ko da tayi yunƙurin hanawa sai ya gwada mata ƙarfin namiji da mace ba ɗaya bane.

Hankali tashe ta dinga rusa ihun kuka, tun yana rarrashinta shi kaɗai a dole ya fice ya kira mata Amina. Abu ɗaya da ya ɗan kwantar mata da hankali shi ne yadda Amina tayi ta nunar mata wannan ai ba komai bane. Hasalima abinda ake yayi kenan tsakanin samari da ƴan matan da suke tsananin son junansu.

Da wannan huɗubar da ta din ga yi mata, da yadda Habib ya dinga tarairayarta da zaƙaƙan kalamai da manyan alƙawurra daban-daban, har yana ba ta kyautar waya mai girman da ya zarce na ta, sai ga ta ɗororo ta miƙe bisa hanyar da suke so babu batun da-na sani. Duk irin ciwon da take ji haka ta maze Amina ta taya ta ta gargasa jiki, ta sha maganin kashe zugin da abokin Habib ya kawo mata, ta lallaɓa suka yi sallama ta koma gida bisa rakiyar Amina da wata ƙawar Aminan da suka biya gidansu suka ɗauko ta don ƙara ɗauke hankalin Mummy.

Idan Allah ya tashi jarabtar bawa duk sa’ido da wayau da tsarewa sadda wani zaiyi dogon ɓarna a gonar da ake killacewa baza’a taɓa ankarewa ba. Da matuƙar mamaki ƙwarai na yadda Nauwara ta dinga aikata abubuwan da take so ba tare da Iyayenta sun ankara da halin da take ciki ba.

Habib, saurayinta na farko haka ya mayar da ita kamar wata farkarsa. Duk sadda ya bushi iska kewarta ya taso masa haka ya cigaba da kai mata ziyara akai-akai, ita kuma tana satar jiki tana zuwa gurinshi. Kwatsam! Ba ta ankare ba sai ga ta da ciki, tsabar tashin hankali sai ta rasa me ma zata yi.

Ta kira Amina tana mata ihun kuka da kururuwa, ita kuma ta dinga kwantar mata da hankali suka yi mahaɗa a hanyarta na zuwa makaranta ta jata zuwa wajen likitan da ya zubar mata da cikin.

Jikinta ya ɗanyi sanyi sosai bayan faruwar al’amarin, suka rabu da Habib ba da son ranshi ba, tun yana mata zarya da magiya tana ƙin ɗaga kiranshi har dai ya gaji ya ƙyaleta.

Ita kuwa Amina tana ta ƙara shige mata jiki da ƙara zugata da tana cigaba da kaɗa mata gangar shaiɗan. Har dai tayi nasarar ƙara tsundumata ruwa tsundum. Amina ta girmi Nauwara nesa ba kusa ba, ta fi ta wayewa da iya tanƙwasa harshe. Don haka daɗin bakin da Amina take mata yasa take jin abinda take aikatawa ai ba komai bane. Tun tana ɗan jin rashin daɗin abinda take aikatawa a wasu lokutan, har ya riga ya bi mata jiki ta daina damuwa ko kaɗan.

Banbancinsu Kawai ita Nauwara abin nata bai girmama ba kamar na Amina, wadda ita har garuruwa take bi da manyan ƙusoshi, ita kuwa tun bayan rabuwarta da Habib bata ƙara bin wani ba. Illa iyaka dai ta dinga amfani da jikinta tana bin Malaman makarantarsu suna ƙara gyara mata takardu.

Daga baya kuma ta fara biyewa samarin ajinsu sama-sama. Abunne kamar wani ƙaddara da asiri, duk yadda taso ta daina abinda take yi abin ya ci tura. Daga baya dai da taga duk ƙoƙarin da take yi haƙanta ya kasa cimma ruwa, sai kawai ta watsar da komi ta cigaba da harkokinta.’

Kafin ta ƙarasa gurin Aminar, ita har ta hangi shigowarta, don haka ta ɗaga mata hannu ta yafito ta, alamun ta je. Lallausan murmushi ta saki ta ƙarasa inda Aminar take, kai tsaye Kujera ta ja ta zauna tana ba tare da jiran ayi mata izinin zama ba.

Gorar lemun coke da take ajiye gaban Amina ta buɗe ta kafa a baki ta fara sha cikim nutsuwa, sanyin da yake ratsata yasa lokaci bayan lokaci take lumshe ido haɗe da sauke ajiyar zuciya.

“Da alama dai kin kwaso ƙishirwa, daga ina kike haka Ƴan mata?”
Amina ta tambaye ta tana kallon yadda bata cire gorar daga bakinta ba sai da ta kusa shanyewa.

“Uhmmm! Ke dai bari. Yau gaba ɗaya yini muka yi muna lakca, ga wannan rana da ake zubawa ga zafi, ba dole bawa ya ji ƙishi ba?!”

Dariya Amina ta saki mai sauti har sai da ta sanya mutane suka fara juyawa suna kallonsu.

“Shegiyata ƙawata! Kin ga da ma kenan kin fara shiga class? Yaushe kika fara haka ba ni da labari?”

Ta yatsine fuska tayi haɗe da mele baki gefe ɗaya sannan ta ce,

“To ya zanyi Ami? Na gaji da halin wancan ɗan akuyan ne Wallahi. Na gama fahimtar dai amfani kawai yake yi dani ba wani abu ba, sai faman kwashe min kuɗaɗe yake yi ga garar da yake kwasa a jikina, abin ya fara isa ta. Shi yasa nace bari kawai inyi ƙoƙari in din ga shiga ajin ina maida hankali nima in huta! Tunda daman can da ƙwaƙwalwata, shiriritar da na sakawa kaina yasa na zama koma baya…”

“Ai dama ina ta faɗa miki, ke ce dai ba kya ji. Kin biye ma waɗannan sakarkarun ƙawayen naki da ko a harkar ba su da class. Ni ina zan iya zama wani gardi yana juya ni yadda yake so? Ƴan mata ki shigo birni ki ga yadda ake kashewa ƴan shiloli irinki makuɗan kuɗaɗe Wallahi. Wani kallonshi kawai idan kika yi sai ya watsa miki daloli a jiki balle ayi zancen babban abin. Amma kin ƙi, kin zauna kina ciyar da wani tsohon najadu a banza a wofi!”

Jiki a sanyaye Nauwara ta kalleta.

“Baza ki gane bane Wallahi Amina, yanzu ba ni da wadatattun lokuta kamar da, Daddy ya ƙara ninninka tsaron da yake mana ne, kuma yanzu tafiye-tafiyen da yake yi ba kamar da bane…!”

Tayi gaggawar katseta,

“Kin san Allah? Kawai dai baki yi niyya bane. Amma don ta Daddynki ai ba wani abu bane. Abin nan fa iya taku ne kawai ba wani abu. Idan kika san ya zaki bi da harkarki sai ki ga babu wanda zai ramfo ki. Ni yanzu gidanmu Yayuna maza biyu ba yan sanda bane? Amma ya aka yi har yanzu babu wanda yasan halin da nake ciki? Iya takune Big girl, da kuma saka ma rai za ki iya!!”

Nauwara tayi yar dariya

“Ke fa daman tun tale-tale ai barikancin naki ya dame nawa ya shanye! Ni dai yanzu kiyi mana order din chips in ci yunwa nake ji, ga account ɗina da jakata karaf suke kamar anyi sata. Daman shigowa nayi na san bazan rasa gayun da za su ci da kyakkyawar ɗaliba kamata ba.”

Ta ƙarasa maganar haɗe da kashe ma Amina ido ɗaya. A tare su biyun suka ƙyalƙyale da dariya haɗe da tafawa.

“Kina ɗiyar Daddy guda! Ki mishi waya ya turo miki kuɗi mana?”

Ta dafe baki da murmushi a fuskarta

“Wai! Rufani ki sayani don Allaj. Duka-duka yaushe ya turo min kudi na bi ta kansu ba tare da na yi wani muhimmin abu ba? Dama ya fara damuwa da irin kashe-kashen kuɗin da nake yi. Shi yasa nace miki fa na daina biyewa wancan ɗan iskan da yake cinye min kuɗi. Yanzu dai daga farkon semester ɗin wannan zuwa yanzu wallahi ya ci min kudi sun kai dubu ɗari, to ina dalili?”

Ta taɓe baki tana harararta ƙasa-ƙasa

“Ai ke kika ga zaki iya. Da kin bi shawarata tun farko ai da duk hakan bata faru ba. Cikin biyu sai dai ka zaɓi ɗaya, kuɗi ko kayan kuɗi. Kuma da kina haɗa karatun da ƴan buga-buga ba sai dai kawai ki ji ana ta miki ambaliyar ruwan kuɗi ta ko wane ɓangare ba.”

“Uhmm! Idan nayi hakan kamar na raina ƙoƙarin da Daddy yake yi a kaina ne! Tunda dai har ga Allah ban nemi abu a wajenshi na rasa ba. In banda gangar da shaiɗan yake buga min a wasu lokutan wannan hanyar da nake bi ai bata dace da ni ba…”

“Ai sai kiyi, ana nuna miki halin da duniya take ciki kina runtse idanu.!”

Ba tare da ɓata lokaci ba Amina ta musu odar chips ɗin dankalin turawa da sauce din hanta da kwai.

Har suka gama cin abincin basu ƙara taɓo maganar da suka yi ba, sai wata da suka fara. Ko da suka gama, basu sake ɓata lokaci a cikin gurin ba suka fita.

Amina tana rataye da designer hand bag ɗin ta ta Chanel a kafaɗa, kai tsaye ta nufi wata galleliyar BMW take wadda wani matashi yake zaune a ciki yana jiranta, ta juya tana kallon Nauwara ta ce,

“To ni zan shige, sai yaushe kuma?”

Nauwara tana ƙare ma motar kallo da santin haɗuwarta a zuciyarta ta amsa da
“Zan yi ƙokari in shigo gidan naku cikin weekend ɗinnan, sai mu ƙarasa maganar da muka fara.”

“Ba matsala. Sai kin zo!”

Ta ɗaga mata yatsu biyu alamun bye, ta shige mota saurayin yaja suka tafi.

Ko bayan wucewarsu Nauwara ta daɗe a tsaye, tana bin motar da kallo har ta ɓace a idanunta. Dai-dai lokacin kuma ɗalibai suka fara fitowa daga makarantar tasu alamun an tashi, tunda dama ƙin shiga lakcar ƙarshe tayi.

Don haka ta tsallaka zuwa inda suke ta bi jerin waɗanda ke jiran aje a daukesu.

***

“I love you too my angel. Muahh!!”

Muhsin ya faɗa ta cikin wayar da ke kare a gefen kunnenshi. Ƴar dariya ya saki a tausashe bayan ya gama turawa Mannira sumbata a cikin iska, ya kashe wayar yana murmushin yadda tayi saurin katse wayar ta can ɓangarenta, alamun ya jefa ta cikin kunya mai tsanani.

Abokinshi da ke zaune tuntuni a gefenshi yana saurarenshi baki a buɗe tunda ya fara wayar, ya kwashe da dariya har yana tafa hannuwa.

“Kai mutumin! Wannan duk ƙauna ce da soyayya haka? Da alama dai Allah Ya kama ka a wannan karon!”

Wani irin tsaki ya saki yana hararar abokin na shi. Bai ce mishi komi ba sai da ya buɗe fridge ɗin da ke ajiye a gefensa ya ɗauki kwalbar whiskey ya buɗe, ƙaramin kofi ya ɗauka ya tsiyaya a ciki ya kafa a baki yana sha, sai da ya shanye wanda ya zuba tas sannan ya juya ga abokin nashi ya ce,

“Ba na son rashin mutunci Bilal. Kada ka ƙara yi mun wannan mugun fatan ba na so!”

Da mamaki sosai a fuskar abokin ya ce,

“Kamar ya mugun fata? Ka kuwa ga yadda kake magana kana ta wani tanƙwasa harshe da lanƙwasa murya? Tunda nake ban taba jin ka yiwa mace magana irin haka ba! Ka ga kuwa dole inyi tunanin ko Allah ya haɗa ka da kalar aure ne”

Yayi wani miskilin murmushi

“Habawa Malam! Ai ba yanzu ba tukun. Wannan dai tana ɗaya daga cikin kyawawan kifayen da ke a cikin komata. Ta kamu ta kowane ɓangare, ni kuwa lallaɓawa nake ina ƙara kiwata ta har zuwa lokacin da zanyi mata kwaf ɗaya.”

Shi da abokin suka kwashe da wata irin dariya suna kashewa. Anan gidan shaƙatawar da ya kasance mallakinshi ne, suka zauna suna shan giya da busa sigari da shisha abinsu. Zuwa lokacin da suka gama, su duka sun bugu sunyi mankas. Anan tsakiyar falon suka baje suna shirme da shiririta har barci ya ɗaukesu hankalinsu kwance.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 34Lokaci 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×