Sa kai ya fi bauta ciwo. Ranar Asabar tun da duku-duku Nauwara ta katse barcin da take bala'in jin daɗinshi. Daman tana fashin sallah, don haka ido kawai ta wanke, ta goge baki, ta fice daga cikin ɗakinsu ta kama aikin gida, abinda sam ba shi daga cikin halayenta.
Ko kafin ma Mommynsu ta fito daga ɗakinta har ta share falo, ta yi mopping, ta share farfajiyar gidan. Baki kawai Mummy ta kama tana bin Nauwarar da kallo, ta ma rasa ta cewa.
Da ɗan murmushi a fuskarta ta duƙa har ƙasa tana gaida Mommyn, sai. . .