Skip to content
Part 36 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Sa kai ya fi bauta ciwo. Ranar Asabar tun da duku-duku Nauwara ta katse barcin da take bala’in jin daɗinshi. Daman tana fashin sallah, don haka ido kawai ta wanke, ta goge baki, ta fice daga cikin ɗakinsu ta kama aikin gida, abinda sam ba shi daga cikin halayenta.

Ko kafin ma Mommynsu ta fito daga ɗakinta har ta share falo, ta yi mopping, ta share farfajiyar gidan. Baki kawai Mummy ta kama tana bin Nauwarar da kallo, ta ma rasa ta cewa.

Da ɗan murmushi a fuskarta ta duƙa har ƙasa tana gaida Mommyn, sai sunne kai take yi irin alamun jin kunyar nan, ba sabanba.

“Nauwara? Ke ce? Ko an canja min tawa Nauwarar maƙuiyaciya da wata mai zafin nama da son aiki ce?”
Mommy ta jefa mata tambayoyin, har lokacin maɗaukakin mamakin bai bar kan fuskarta ba.

“Kai Mummyyyy”
Ta faɗa tana dariya haɗe da ƙara sunne kanta cikin jin kunya.

“Da gaske fa. Ba ni labari dai. Yau kuma me ya shigo cikin ƙwaƙwalwarki ake buga wannan sammakon aiki Nauwara?”

“Wallahi ba komai Mommy, kawai dai yau aikin nake so in taya ki shi yasa. Kuma ni nace ma Mannee tayi barcinta duk abinda take yi zan fanshe ta!”

Maganganun dai kamar basu shiga Mummy ba, amma sai bata ƙara ja da nisa ba ta ce
“To madallah! Allah ya sa da gaske kike yi. Allah kuma ya sa ki ɗore a hakan. Amma dai ni a raina sai nake ji kamar banza ba ta kai zomo kasuwa. Muje kicin ɗin.”

Tana dariya ta amsa addu’ar, sannan ta bi bayan Mummy suka shige kicin ɗin. Kamar ya da ƙanwa, Mummy Ziyada tana da kyawun jiki sosai ta yadda idan ba wanda ya sani ba baza’a taɓa cewa ita ta haifi Ziyada da Manneera ba. Kai tsaye za’a kira su da ƙanninta saboda kama da suke yi da ita.

Suna ƴan hirarrakinsu ta ke kama ma Mummy aikin. Ba kamar Manneera ba da zuwa lokacin ta gama karantar komai na aikin kicin ɗin, Nauwara kam ba sosai ta iya wasu abubuwan ba. Komai za ta yi sai ta tambayi Mommy gudun kuskure ko kuma ta cika fiye da yadda ake buƙata,
“Mommy gishirin ya isa haka? Mommy guda nawa zan zuba maggin?”

A haka dai har suka kammala girkin, suka tattara komai da za su buƙata suka kai falo aka jera kan teburin cin abinci. Da yake Khamis ba a gidan ya kwana ba, a yadda ya ce musu ya je Abuja wajen wani taro mai muhimmanci, sai washegari Lahadi zai dawo, don haka tun gurin girkin basu yi sanwa da shi ba.

Manneera da ta kusan raba dare suna musayar ba fulawa ruwa ita da Muhsin bata san wainar da suke toyawa ba sai da alarm ɗin wayarta ya buga. Sosai ta ji daɗin barcin da ta rama, daman bashin barci ne fal da idanunta, shi yasa ko da Nauwara ta ce mata ta kwanta ita za tayi ayyuka bata tankwaɓe tayin ba. Ko a yanzu daƙyar ta tashi ta shige bayi don tayi shirin islamiya.

Acan falo ko da suka gama jera kayan karin kumallon Nauwara bata zauna ba, kicin ɗin ta koma. Tas ta wanke kayan da suka ɓa ta gurin haɗa abin kari. Ɗakin Mummy ta shige, sai ta same ta fito daga wanka tana zaune a gefen gado tana waya da Aunty Kareema.

Da ganin shigowarta yasa Mummy taƙaita hirar bayan ta ba Aunty Uzurin za ta sake kiranta. Idanunta ta mayar kan Nauwara bayan ta ajiye wayar a gefenta
“Ƴanmatan Mummy? Ya aka yi?”

Ɗan shagwaɓe fuskarta tayi ta ƙarasa gefen gadon ta zauna tana kallon uwar fuskarta a marairai ce.

“Mommy, don Allah don Annabi ki barni in je wajen saukar da Ƙawata zata yi na Al-Qur’Ani mai Girma! Kin tuna ƙawata Amina wacce muka yi Sakandire tare ko? Ita ce za tayi walimar sauka yau, duk tsaffin ƙawayenmu na sakandire za su je don a haɗu a sada zumunci, don Allah Mummy ni ma ki barni in je…”

“Nauwara na san ki da masifaffen yawo na banza da wofi. In aka bibiya babu wata ƙawarki da za tayi sauka…”

“Wallahi Allah da gaske nake Mummy. Kin manta Aminar ne? Kuma wallahi gidansu kaɗai zan je, ana gama walimar zan dawo. Don Allah ki bar ni, kin ji Sweet Mummy?”

Ɗan dariya Mummy ta yi tana jinjina halin ɗan yau.
“Wato dama saboda haka ne yasa yau kika tashi da aiki tuƙuru babu ƙaƙƙautawa don toshiyar bakin Mummy ko?”

Da sauri ta girgiza kai ita ma tana dariya
“Ayya mana Mummyna. Allah ba haka bane, da gaske yau aikin nake jin yi. Kuma ko ba yau ba zan dinga fitowa ina kama aikin ba wai kullum ina sakarwa Nauwara ba. Ni dai don Allah ki bari in je, Allah idan ban je ba ba za ta ji daɗi ba. Kuma kin ga duk sauran ƙawayenmu za su haɗu za’ayi ta tambayar ina nake.”

Shiru tayi tana tunani, kamar ta bar ta kamar kuma kar ta barta ta tafi. Can sai ta ce
“Kin dai san Daddynki baya nan ko? Zai iya dawowa yau duk da ya ce sai gobe. Kuma idan ya dawo gidannam ba kya nan ba ƙaramin masifa za mu sha ba, kin sani sarai.”

Shagwaɓe fuska ta ƙara yi ta sake matsawa kusa da Mummyn ta ce,

“To ai ba lallai sai ya sani ba Mummy. Kina yanzu de ba ya garin, idan ta kama zai dawo yau ɗin ma kin san ba ya dawowar wuri, kafin ya dawo tuni na je na dawo. Don Allah kar ki ce A’a Mummy na, kiyi min alfarma pls.”

Irin yadda take yin sai ta ma bawa mahaifiyar dariya, ta ɗan murmusa tana girgiza kai ta ce
“Allah Ya shirye ki Nauwara! Har yanzu da baki san kin girma ba. To shike nan, ki je, bayan mun gama karyawa sai ki shirya ko zuwa goma da rabi ki tafi. Amma fa ki tabbatar kin dawo da wuri.”

Miƙewa tayi ta daka tsalle tana ƙyalƙyala dariya kamar ƙaramar yarinya. Sai kuma tayi ma Mummyn wata wawuyar runguma bakinta har kunne tana mata godiya, kafin ta kwasa da sauri ta fice daga ɗakin, zuciyarta cike fal da matsanancin farin ciki.

Ko da ta shiga ɗakinsu sai ta samu Mannirah a zaune tana ƙara duba littafan darasinta. Kusa da ita ta ƙarasa ta zauna tana dafa kafaɗarta, da ɗan murmushi a fuskarta murya a tausashe ta ce,

“Mannee sweet Sister. Kin tashi? Kin ga yau bazan samu zuwa Tahfeez ba. Don Allah idan kin je ki ce ma Mu’allim Aminiyata ke sauka, yau bazan samu zuwa ba. Kin ji ƴar ƙanwata?”

A lalace Manneera ta ɗaga mata kai. Ta bi Nauwarar da kallo lokacin da ta miƙe da sauri ta faɗa banɗaki. Taɓe baki tayi, ko rantsuwa tayi babu kaffara ta san ƙarya Nauwara ta shirga musu. Domin duka ire-iren ƙawayen da take gani Nauwara tana hurɗa da su, ba ta tunanin akwai wacce take zuwa islamiyya, domin sam babu a kamanni.

Littattafan da take dubawa ta rufe ta mayar da su cikin jaka, ta ɗauki gogaggen hijabinta da yake ajiye gefe ɗaya ta rataya jakar a kafaɗarta ta fice daga ɗakin.

A kan teburin cin abinci ta samu Mummy da sauran ƙannensu, har ƙasa ta durƙusa ta gaida Mummyn kafin taja kujera ta zauna tana amsa gaisuwar da ƙannenta suke mata.

“Mabruka ya jikin naki? Na ga kin yi shirin makaranta, har kin gama warwarewa?”
Ta tambayi ƙanwarta da take bi mata, ganin kwanaki uku da suka gabata yarinyar kwana take da zazzaɓi, har sai da Uncle Jamilu ya ɗaura mata ƙarin ruwa a gida.

Kafin yarinyar ta amsa Mummy ta karɓe da cewa,

“Ke ma dai kya faɗa. Ni ma kakabin da na gama yi mata kenan. Amma tun da ta ce za ta iya ai za ta iya ɗin ne, ita ba ƙaramar yarinya ba ce sosai, abinda baza ta iya ba ma baza ta tatago shi ba.”

“Haka ne Mummy. Mabru Allah ya ƙara lafiya.”

“Amin ya Allah”
Suka amsa gaba ɗaya.

Cikin nutsuwa ta Mannira ta zuba ma kowa abinda yake buƙata, sannan ta zuba ma kanta ta zauna ta fara cin abincin bayan ta yi bismillah. Suna gamawa ba tare da ɓata lokaci ba ta tattara ƙannen nata suka fice zuwa tsakar gida, inda direba ke jiran fitowarsu don ya kaisu makarantar da ba nisa sosai ke tsakaninshi da gidan nasu ba.

*****

Nauwara kuwa tsabar zumuɗi da ƙyar ta iya zama tayi karin kumallo a gurguje. Ringing tone ɗin wayarta ta dinga dannawa akai akai tana kara waya a kunne tana maganar ga ta nan tafe, a zuwan sauran ƙawayensu ke kiranta.

Haka nan dai ba da son ran Mummy ba ta barta tafiya a lokacin, ko da suka yi sallama dubu uku Mummy ta bata, ta ce dubu ɗaya tayi kuɗin mota, dubu biyu kuma ta kaiwa ƙawar tata mai sauka. Ta amsa da hannu bibiyu, har da duƙawa ƙasa tana godiya da addu’ar Allah ya ƙara buɗi.

Gudu-gudu sauri-sauri ta fice daga gida. Gidansu Amina a can Governor Road yake. Shatar Mai Napep ta ɗauka tun daga unguwarsu har ƙofar gidansu Amina.

Mintuna biyu ta ɗauka tana ƙarewa wawakeken gidansu Aminar kallo, kamar baza’a mutu ba. Ko da ta ɗan waw-waiga ta kalli gidajen unguwar sai taga gidansu Amina yana ɗaya daga cikin gidaje mafiya kyau a cikin layim. Tun da can ma da suke tashen ƙawance sau ɗaya ta taba zuwa gidansu Aminar, shima a tsaitsaye suka je bata tsaya ta ƙare ma ko ina kallo ba.

Bayan mai gadi ya tambayeta gurin wacce ta zo ta faɗi cikakken sunan Aminar kafin ya bar ta ta shiga ciki, Mai aiki ce tayi mata iso zuwa ƙatoton falon gidan na farko inda anan ne ake tarar baki, idan ka matsa gaba kuma kafin ka ƙarasa zuwa ga ɗakunan gidan, wani falon ne mai madaidaicin girma wanda aka yiwa ado fiye da na farkon. Da alama dai wannan falon shi ne na zaman masu gidan.

Ta zauna akan kujera tana yan latse-latsen waya, sai wani fisga take tana basarwa don kar masu aikin da ke shige da fice su raina mata ajawali. Ko ruwa da lemon da aka ajiye mata bata taɓa ba don kar suyi mata kallon kwaɗayayya. Fiye da mintuna goma sha biyar tana zaman jiran fitowar Amina har sai da ta fara gajiya kafin aka yi mata iso zuwa ɗakin Aminar.

Ko da ta shiga ɗakin sai ta gane ashe falon da ta zauna ba komai bane a haɗuwa. A fili ta buɗe baki tana ƙarewa ɗakin kallo cike da ƙauyanci.

Komai na ɗakin a tsare kuma a ƙayace, yadda kuka san daga wata fastar sayar da kayan ɗakine na manyan kamfanoni aka fitar da ɗakin Aminar.

Ita kuwa hakimar tana zaune akan wata luntsumemiyar kujera ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya, ko kayan barcin jikinta bata samu sararin cirewa ba, da waya kare a kunnenta tana magana a yangace, murya ƙasa-ƙasa sosai kamar baza tayi magana ba, ko Nauwara da take tsaye ɗan nesa da ita kaɗan ba ta jin me take cewa.

Don haka ta lalubi kujera ta zauna tana sake ƙrewa ɗakin kallo. Wancan lokacin da suka je gidan bata samu ta shiga har ɗakin Aminar ba, iyakarta farfajiyar gidan da falon baƙi.

Kaɗan-kaɗan take jin hirar da Amina take yi take waya, godiya take yiwa wanda suke wayar, ta jefa mishi tausasan sumbata biyu a cikin iska sannan ta katse wayar, sai kuma ta saki wani ɗan siririn tsaki ta ƙara da faɗin
“Sakarai kawai.”

Hankalinta ta mayar kan Nauwara fuska ɗauke da yalwataccen murmushi.
“Sannu da zuwa ƙawata! Ai banyi zaton yanzu za ki zo ba, gashi yau barci ya ɗaukeni shi yasa ban iya tashi da wuri ba.”

Jikin Nauwara a sanyaye ta mayar mata da martanin murmushin tana cewa
“Ba komai fa. Nima so nake yi in koma da wuri shi yasa na bugo sammako.”

Amina ta gyaɗa kai.

“Gaskiya ne kuma. Kin san irin wannan harka ta basaja, dole sai mutum ya iya takunshi”
A tare suka saki dariya, haɗe da kashe hannu.

Kayan karin kumallo mai rai da lafiya aka kawo musu har cikin ɗakin Aminar. Suka ci suka yi nak! Suna ci tana ƙara wayarwa da Nauwara kai akan sabon harkan da za ta ɗora ta akai da kuma yadda ake gudanar da wasu abubuwan.

Bayan sun gama ta bar Nauwara ta shiga wanka. Nauwara de ba baka sai kunne, hannuwa biyu tasa ta dafe da kumatu tana ƙara nanata maganganun da suka yi Amina. Wani sashe na zuciyarta yana ce mata kawai ta fasa wannan harka, ta tashi sawunta a likkafa ta koma gida. Shaiɗaniyar zuciyarta kuma tana ƙara zuga ta, tana hasko mata irin rayuwa ta bagu da bubbuɗawar da zata yi kamar dai yadda taga Amina tana yi.

Tana ƙara tuna yadda za ta shahara ta zama ɗaukakkiya cikin ƙanƙanin lokaci, ta huta da bin Daddynsu tana roƙon yayi mata wani abu da bai taka kara ya karya ba. Duk da cewa dai yana iyaka bakin ƙoƙarinshi a kanta, amma aka ce wai rai da buri, ga kuma tsananin son rayuwar fantamawa. Ta san Daddy yana mata duk abinda take buƙata, amma a ganinta hakan is not enough.

Tana so ta ƙara da wasu abubuwan a matsayinta na cikakkiyar budurwa, ta yi shiga ta azo a gani na ke ce raini, ta riƙe rantsattsiyar waya mai bala’in tsada da jakunkuna masu kyau da tsada. Ya zamana cikin ƙawaye itama ta zamo abin hira da kwatance.

Tana nan tana ta saƙa da warwara har Amina ta fito daga bayi ɗaure da tawul a jikinta. Sai ƙamshin sabulun wanka take yi mai tsananin ƙamshi. Ta zauna akan kujeran gaban madubi tana ta kanainayar jiki da shafe-shafe da goge-goge. Ƙamshi kala-kala ya haɗe da na sabulun da tayi wanka ya sake karaɗe ɗakin gaba ɗaya.

Nauwara bin ta ta dinga yi da kallo cike da alamun tambaya a fuskarta, can kuma ta kasa haƙuri ta ce,

“Wai ni ya aka yi na ji gidan shiru ne kamar babu kowa sai masu aiki? Momnynku ba ta nan ne?”

A lalace Amina ta taɓe baki, kamar baza ta amsa ba sai kuma ta ce,

“Barci take yi mana! Kin san yau weekend, ita da ta fito daga ɗakinta ma sai zuwa can bayan la’asar.”

Da mamaki sosai Nauwara ta ce
“To Daddynku fa?”

Ta ƙara taɓe baki a karo na biyu
“Last dai na ji shi kamar yana US, I don’t know! Kin san aikinshi ba ya barinsu su zauna.”

Nauwara tace,

“Ke nan dai ke kaɗai kike zama a wannan gidan mafi yawancin lokuta sai masu aiki? Tunda na ji kin ce Mommynki ai ma’aikaciyar banki ce ko?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 35Lokaci 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×