"Wai tsoro take ji ne?"
Mummy ta tambaya, tana rarraba idanunta a tsakanin su biyun.
Kamar haɗin baki duk sai suka ɗanyi dariyar yaƙe kawai, ba tare da sun amsa mata ba.
"Ki kwantar da hankalinki ƴanmata. Martabarki za'a kankaro miki. Ciwon ƴa mace na ƴa mace ne mu nan baza mu taɓa cutarki ba. Da ace harka da Mummy ba gaskiya da ƙawarki bata kawo ki gidana ba. Gyara ne likita zai miki mai suna gyara, idan kika ji maida tsohuwa yarinya to shi ake nufi. Duk yadda kika banzatar da kanki a baya tsaf. . .