Skip to content
Part 38 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

“Wai tsoro take ji ne?”

Mummy ta tambaya, tana rarraba idanunta a tsakanin su biyun.

Kamar haɗin baki duk sai suka ɗanyi dariyar yaƙe kawai, ba tare da sun amsa mata ba.

“Ki kwantar da hankalinki ƴanmata. Martabarki za’a kankaro miki. Ciwon ƴa mace na ƴa mace ne mu nan baza mu taɓa cutarki ba. Da ace harka da Mummy ba gaskiya da ƙawarki bata kawo ki gidana ba. Gyara ne likita zai miki mai suna gyara, idan kika ji maida tsohuwa yarinya to shi ake nufi. Duk yadda kika banzatar da kanki a baya tsaf za’a ɗinke ki ta yadda idan ba ƙwararren namijin da ya saba gogayya da mata barkatai ba babu yadda za’a gane ke ba budurwa bace. Kin gane ko?”

A kasalance ta ɗaga kai, alamar eh! Ta kasa buɗe baki ta amsa, Domin maganganun basu ƙara mata komai ba sai tashin hankali da fargaba.

“Yauwa! Bayan nan za’a haɗa ki da zafafan magungunan da za kije gida kiyi amfani da su. Kashaidi ƙwaƙƙwara guda ɗaya da zanyi miki shi ne, bayan wannan aikin aka yi miki, duk yadda za ki ji ki a wani hali na sha’awa kar ki kuskura ki bayar da kanki ga wani banzan-banza da bai san darajarki ba. In dai ba ni ce na samar miki appointment ba kar ki kuskura ki saki kanki. Kina ji na?”
Ta ƙarasa da tambayar muryarta a ɗage da ɗan tsawa-tsawa.

A karo na biyu a tsorace Nauwara ta sake ɗaga kai. Ta ƙara da
“Eh! Na gane. Zan kiyaye in Allah ya yarda.”

“Yauwa! Ku ci abinci kafin ƙarasowar likita.”
Tinƙis-tinƙis ta miƙe da takunta na ƙasaita ba tare da ta jira cewar ɗaya daga cikinsu ba ta shige kicin, ta ba mai aiki umarnin a haɗa abinci mai rai da lafiya da abin sha a kai ma su Nauwara falo, sannan ta wuce sama inda ɗakinta yake.

Idan bawa bai mutu ba lallai bai gama ganin kallo ba. Haka zalika tuwo labarin wuta yake ji tsire shi yaga zahiri. Duk yadda Nauwara take a tsorace, da yadda take ɗari-ɗari. Haka dai tana ji tana gani bayan zagawa bayi sau biyu a dole ta sauya kayan jikinta zuwa wata sassauƙar doguwar riga da aka bata, suka shige cikin keɓantaccen ɗakin da ɗan tsamurmurin likitan yayi mata umarni. Da alamun daɗaɗɗen likita ne da ya daɗe kuma ya gwanance akan irin wannan aikin, duba da yadda yake komai kansa tsaye.

Hankalin Nauwara a tashe kamar wacce za’a zare mata rai. Ta kasa tsayawa ayi mata allura, duk da yadda likitan ke ta faɗa mata kalamai na kwantar da hankali. A ƙarshe dai sai Amina ya kira mata bayan ita da kanta ta nemi haka sannan ta sadaƙar, ta haƙurƙurtar da zuciyarta ta tsaya aka tsira mata alluran masu bala’in zafin tsiya…

Duk abinda ya biyo bayan nan baza ta ce ga shi ba. Bayan ɗan siririn labulen da likitan yasa ya raba tsakanin cibiyarta zuwa ƙasanta ji take kamar ba jikinta ake taɓawa ba. Awa biyu cur likitan ya shafe kafin ya faɗa mata an gama. Bayan dokokin da ya karanta mata na shiga ruwan zafi-zafi akai akai da wasu ƴan ƙwayoyin magungana da ya bata da bata san ko na menene ba sai yayi mata umarnin tashi zaune.

“Zan iya tafiya?”
Ta jefa mishi tambayar fuskarta na bayyana tsoro da taraddadi.

“Ƙwarai kuwa. Sai dai ba da sauri sosai ba.”
Ya amsa bayan ya jefe ta da ɗan murmushi.

Bayan ficewar likitan Maltina da madarar ruwa Amina ta haɗo mata a cikin kofi ta umarci ta shanye. Sannan ta shige cikin banɗakin da yake gurin ta haɗa mata ruwa mai ɗumi sosai a babban bokiti ta ce taje ta kama ruwa ta yi wanka.
“Kin ga lokaci ya fara tafiya. Gara kiyi hanzarin komawa gida kafin Mummy ta fara zargin wani abu. Kuma ma de don tuwon gobe ake wanke tukunya.”

A tare suka saki murmushi sannan ta sauka daga gadon a hankali. Da yake aiki ne aka yi mata na gwanancewa, kaɗan kaɗan take jin canji a jikinta ba irin canjin da zai saka ta a gaggarumin damuwa ba. Wanka tayi a gaggauce, ko kafin ta fito har Amina ta kawo mata kayanta da kayan kwalliya.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta taya ta shiryawa sannan suka fice daga ɗakin. A falon suka tarar da Mummy zaune. Nauwara sai bin ta da kallo da idanun burgewa take yi ganin a ɗan tsakankanin awoyin har ta sake wanka ta canja suturar da ke jikinta, a yanzu ma ƙayataccen kwalliya ke shimfiɗe a fuskarta kamar ba babbar mace ba.

Wasu ƴan ƙananun goruka da kwalaben magunguna ke ajiye a kan teburin gabanta. Da fara’a sosai a fuskarta ta tarbesu, har tana tsokanar Nauwara da cewa
“Ina tsoron da kike ji? A yanzu dai kin tabbatar ba wani mugun abun za’ayi miki ba ko?”

A kunyace ta rufe fuska haɗe da ɗaga kai, fuskarta da murmushi.

“Yauwa to kin ga, dawo nan kusa da ni ki zauna in nuna miki magungunan da za ki tafi da su da yadda za kiyi amfani da su.”

A kunyace ta zauna kusa da Mummyn, wani daddaɗa kuma tattausan ƙamshin turaren humra da ya daki hancinta yasa ta lumshe idanu. Buɗe hanci tayi ta shaƙi ƙamshin sosai, a zuciyarta take ayyana in Allah ya yarda idan tayi kuɗi gayu da ƙamshi bazai yanke a jikinta ba.

Babu ɓata lokaci Mummy ta nuna mata duk magungunan da za ta dinga sha a gida. Magungunan mata ne amma na turawa sun fi yawa, na sha da na shafawa, da wanda za ta matsa idan ta warke sannan wanda za ta dinga hayaƙi. Sai da ta gama nuna mata ta tabbatar ta gane yadda za tayi amfani da su sannan ta mayar da kayan cikin wani ɗan ƙaramin jaka mai kyau da ban sha’awa ta miƙa mata.

Bayan ta karɓa wani babban leda da yake ajiye a gefenta ta sake ɗakkowa ta miƙa mata.
“Ga wannan ki riƙa ma ƙannenki. Sweet baby ta faɗa min a gida cewa kika yi za kije bikin sauka. Snacks ne a cikin ledar, ki tafi musu da shi a matsayin abin sauka da ƙawarki ta baki. Kin san mu duk wani hanya na ɓoyen taku mun sani.”

A wannan karon, duk yadda ta so ɓoye dariyarta ta kasa, a tare su ukun suka kwashe da dariya. Mummy har da miƙa ma Nauwara hannu alamun su kashe, daƙyar ta iya ɗaga hannu ta miƙa mata tana jin kamar ƙasa za ta tsage ta shige don kunya.

A wannan karon Amina bata hana ta ba, tun a nan cikin falon Mummy ta mayar da hijabin jikinta, ta maƙala face mask ɗin.

“In haɗa ku da direba ya mayar da ku gida ne…?”

Da sauri Amina ta katse ta da cewar
“A’a Mummy. Wanda ya kawo mu tun ɗazu yana waje yana jira. Za mu wuce. Mu saurari kiranki kenan ko?”

“Eh! Amma kafin nan kin san sai ta warke gaba ɗaya magunguna sun kama jikinta.”
Sai kuma ta mayar da idanunta kan Nauwara ta ce.
“Ƴanmata bani lambar wayarki. Sannan daga yau kar ki sake amfani da sunanki a gidannan. Binafa, Binafa zan ke kiranki daga yau. Ta ɓangare na da duk waɗanda zan haɗa ki da su idan aka tambayi sunanki ki ce Binafa. Kin fahimta ko? Harkar bariki sai da ɓad-da kama.”

“To Mummy. Na gane. Na gode. Zan kiyaye in Allah ya yarda.”
Ta amsa da zazzaƙar muryarta.

Basu sake ɓata wani dogon lokaci ba suka fice daga gidan. Suna shiga mota direban ya figeta a guje suka bar unguwar.

Hankalin Nauwara raba da rabi ne a jikinta. Babban burinta su isa gida ta ganta a gaban Mummy, zuciyarta cike da addu’ar Allah yasa Daddy bai dawo ba, Allah yasa kar ta fuskanci kallon zargi ko kuma wasu tuhume-tuhume daga Mummynta.


"Yaya dan Allah..."

“Khamis, zancen gaskiya kenan bazan samu zuwa ba.”

A kasalance ya ɗaga idanu ya kalli ɗan’uwan nasa. Sai kuma ya gyara zama sosai akan kafet ɗin da ya malale falon, saɓanin farko da yake a tsugune, gwuiyawunsa gurfane a ƙasa.

“Yaya! Yarinyar nan ƴar gidan manyan mutane ce. Ba komai yasa nake so mu je tare ba sai don nasabarta, Allah ya sani da gaske ina son Bilkisu. Babanta shi ne Sheik Abulfatahi Abdullahi…”

Da saurin gaske idanu a waje Alh Yusuf ya ɗaga fuskarsa yana kallon Khamis. Ƙarara maɗaukakin mamaki ke shimfiɗe a fuskarsa. Don kore tantama sai ya ce
“Sheik Abulfatahi dai da nake kallon Tafseer da wa’azinsa a gidan T.V?”

“Ƙwarai kuwa Yaya. Shi yasa nake so mu tafi tare…”

“Ka ga dakata Khamis! Na rantse da Allah da ƙafafuna bazan taka har garin Zaria nema maka auren wannan yarinyar ba.”

Ɗif ! Khamis ya ɗauke wuta. Ya daɗe idanunsa a ƙasa. Ya san halin Yayan kamar yunwar cikinsa, tunda ya rantse, abu ne mawuyaci ya karya rantsuwarsa. A raunane ya ɗaga idanunsa da suka kaɗa suka yi jaa lokaci ɗaya yana kallon ɗan’uwan nasa.
“A zato na, a duniya babu abinda zan zo da shi ka kasa goya min baya…”

“Da kenan Khamis. A yanzu kam na daɗe da dawowa daga rakiyarka. Kaje ka nemi aurenka, idan ta kama dole sai ka je da wani babba to ka nemi Ƙannin Abba ko na Ummee su rufa maka baya. Ni kam idan Allah ya tabbatar ko ta waya ka sanar da ni, za mu haɗu a can ranar ɗaurin aure.”

Wato da gaske ne da ake cewa idan baƙin ciki da takaici yayi yawa kasa magana ake yi. Irin hakan ce ta faru da Khamis, wani ɗaci-ɗaci bakinsa ya ɗauka kamar wanda ya rasa ɗanɗano. Wani dunƙulallen abu mai kama da ƙwallon mangwaro ya tokare mishi a ƙahon zucci. Da ya tabbatar bazai iya buɗe baki yayi magana ba, sai kawai ya daddafa ya miƙe tsaye, bai ƙara kallon Yayan ba ya fice daga falon.

Ko da ya ƙarasa cikin motarsa da ya faka a ƙofar gidan ya daɗe a zaune, bai iya tayar da motar a gaggauce ba saboda yadda ranshi ke ɓace. Bai taɓa tsammanin Yaya zai iya watsa mishi ƙasa a ido haka. A zatonshi, nemo aure a irin wannan gidan na manyan malamai babban abin alfahari ne da ahalinsa za su karɓa da hannu bibiyu. Sai ga shi tun a karon farko da babban malamin ya buƙaci ganinsa Yayan ya gwaɓe masa gwuiwa.
‘To ko dai yana tunanin irin shirmen da na saba aikatawa a baya ne zan maimaita a wannan karon?’
Ya tambayi kansa a zuciya.

“Allah ya kiyaye. Duk iskancina na san kalar aure. Bilkisu kalar aure ce. Kuma in Allah ya yarda sai na aure ta. Ƴan baƙin ciki sai dai su mutu.”
Ya amsa ma kansa a fili ya ƙara da kalaman ƙarfafa ma kansa gwuiwa.

Lokaci ɗaya kamannin Bilkisu ya dawo a idanunsa. Tuno Sarauniyar zuciyarsa da kyakkyawar surar da take ɗauke da shi yasa shi sakar ma kansa wani tattausan murmushi. Lokaci ɗaya duk wani ƙarfin gwuiwa da ya rasa ya dawo mishi. Da ƙarfin jiki da na zuciya ya tayar da motar, yayi revers ya bar unguwar.

A zuciyarsa yake tunanin masu siffar kamala mutane biyu cikin Amintattunsa da za su take masa baya don zuwa amsa kiran da Mahaifin Bilkisu yayi mishi a gobe lahadi. Kiran da shi ne dalilin dawowarsa garin kaduna afujajan a yau, ba tare da ya shirya dawowa ayau ɗin ko gobe ba.

‘Haɗuwarsa da Bilkisu arashi ne, ko kuma ya ce babban rabo. Idan ya juya ya kalli lamarin ta wata fuskar kuma tabbas haɗuwar tasu Zanen ƙaddara ne daga cikin kundin ƙaddarorinsu. Abu ne da ko kusa bai taɓa tsammanin faruwarsa a lokacin da ya faru ba.

A gurin saukar karatun Alƙur’ani mai girma ya haɗu da ita, saukar da sai da aka kai ruwa rana tsakaninshi da abokinshi Falalu kafin daƙyar ya amince zai raka shi halartar saukar budurwarsa, ashe rabon ya haɗu da matar aurensa ne.

“Falal, ni fa na ga matar aure?”
Ya faɗa ga abokin nasa a lokacin da yake sake ƙure ƴanmatan da kallo, su goma ne cif. Suna tsaye a tsakiyar filin makarantar sun zagaye lasifika suna rera karatun Alƙur’ani mai girma da zaƙaƙan muryoyinsu.

“Kai fa mayen mata ne Kham! Don ubanka nima tawa matar tana ciki, ina fatan dai ba wancan ƴar baƙar kyakkyawar yarinyar da take tsaye kusa da na biyun ƙarshe bane…”

“Ko kusa ma idanuna bai kai kanta ba. Kana ganin zinariya a tsakiyarsu wa yake ta azurfan da suke zagaye da ita? Wancan fara tas ɗin yarinyar nake magana.”

Mafari kenan. A shige-shige da iya bugar ruwan ciki irinna Khamis, kafin su bar filin makarantar sai da ya san cikakken sunanta, shekarunta, mahaifinta, hatta ƴan’uwanta sai da aka nuna mishi. Muhimmin abu da samunshi ya fi komai yi mishi daɗi shi ne lambar wayarta da aka damƙa mishi, bayan an sanar da shi ƙa’idar Bilkisu da irin lokacin da idan aka kira ta a waya take ɗauka. Saboda kaso saba’in da biyar cikin ɗari na tsarin rayuwar da mahaifinsu ya ɗora duk ƴaƴanshi kan hidimar karatu ne.

Duk gane-ganen ƴan mata kala daban-daban da zazzafar soyayyar da yasha yi da mata masu ɗumbin yawan da shi kanshi bazai ce ga iyakarsu ba bai taɓa ji a zuciyarsa ya samu yarinyar da zai ƙara aura da zuciya ɗaya ba sai Bilkisu. Wani ƙaƙƙarfan so ne ya kamu a zuciyarsa, idan ba ya manta ba ma zai iya rantsewa ko Ziyada bai ji yana mata irin wannan soyayyar ba.

Awoyi uku cur da suka ɗauka a gurin saukar shi dai ya ɓata nashi wajen bibiyar Bilkisu da neman sanin WACECE ITA? Duk inda ta bi da ƴan’uwa ko ƙawayenta a fakaice yake bibiyarsu, duk inda ya samu dama da saurin gaske yake ɗaukarta hoto da wayarsa. Kafin barinta makarantar ya ɗauketa hotuna sun fi kala hamsin, masu kyau da marasa kyau.

Wayar hannu. Idan bata zo ta ɗaya ba tabbas za ta zo ta biyu a abubuwan da suke taka muhimmiyar rawa gurin lalata ginanniyar tarbiyar da aka ɓata shekaru masu yawa ana gina ta da kyakkyawar Tubali. A wannan LOKACI Mafi ban tsoro da muke ciki, waya ita ce tsani na farko da mayaudaran samari suke amfani da ita gurin samun damar damƙar zuciyar duk yarinyar da suka kafawa ƙahon zuƙa. Sai dai Allah ya tsare mana zuri’a ya shirya mana.

Baiwa ce ta musamman da Allah yaba Khamis, wasu abokanansa kuma suna ganin asiri yake da, duk aji da kwarjini da ji da kan Yarinya in dai ya tare ta ko kuma ya kira ta a waya ta ji muryarsa dole ne ma sai ta saurare shi.

Bai fara zuwa gurin Bilkisu ba, sai da yayi amfani da waya ya kafawa kansa ƙwaƙƙwaran tubali a zuciyarta. Ita da kanta ta nemi ganinsa a gidan Yayarta da take aure a garin kaduna, a lokacin Yar tata ta haihu daƙyar mahaifinsu ya bari ta zo mata aikin bakwai.

Mataki na biyu kenan. Kwanaki goma sha huɗu da tayi a gidan Auntynta zuwanshi gurinta sau biyar. Tun a ganin farko da tayi masa taji a ranta kuma ta bayyana masa a fili yayi mata ɗari bisa ɗari.

Wani abin burgewa ga Khamis ɗin shi ne bai ɓoye mata yana da mata da ƴan yara ba. Ya faɗa mata shi ɗan kasuwa ne, sannan ya ɗaukar mata alƙawarin gidanta daban za ta zauna da uwar ƴaƴansa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 37Lokaci 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.