Skip to content
Part 4 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

“‘Eh! Nawa za’a ciro maka?”

Sai da ya zaro Atm ɗinsa daga cikin wallet ya miƙa ma jami’in. 

“A ciro min dubu ɗari biyu, su cire cherges a cikin acc ɗin.”

Ya faɗa musu pin ɗinshi sannan ya sake mayar da hankali kan Alhaji Lukhman, wanda har lokacin bai samu sararin ɗago da kanshi ba.

Ko da ya mayar da idanunshi kan Khamis da wani masifaffen haushinshi da yake ji, sai yaga idanunshi a buɗe, shi kaɗai yana ta ƴan harare-harare. Babu alamun damuwa da halin da aka fice da Firdausi ko kaɗan a fuskarsa.

Ya sake aika mishi da wani mugun kallo, ƙasa-ƙasa yayi ƙwafa. Ya cije gefen bakinshi na dama zuciyarsa cike da tunanin ƙwaƙƙwaran matakin da yake niyyar ɗauka yanzunnan kan Khamis.

In Allah ya yarda a wannan karon zai ladaftar da shi fiye da yadda yake tsammani, zaiyi maganinsa. Zai aje duk wani tausayi da ƙaunar ƙanin nasa a gefe ɗaya ya nuna masa kuskurensa. 

Ba’a daɗe ba wanda yaje ciro kuɗin ya kawo, godiya yayi mishi sannan ya karɓi kuɗin. A karo na biyu ya sake saka gwuiyawunshi biyu a ƙasa gaban Alhaji Lukhman.

Ya ɗora mishi dubu ɗari biyun kan cinyarsa. Ya haɗa hannaye biyu alamar roƙo ya fara magana a tausashe.

“Alhaji, kayi haƙuri. Don girman Allah ka kwantar da hankalinka. In Allah ya yarda a wannan karon matsalar nan ta zo ƙarshe.

Ka karɓi kuɗinnan a matsayin kuɗin gaisuwa, kuɗin saka ranar aure, sadakin aure tsakanin Khamis da Firdausi.”

A matuƙar firgice da jin kalaman da suke fita daga bakin ɗan’uwansa ya buɗe idanunsa, duk da halin da yake ciki na matsanancin ciwon jiki bai hana shi miƙewa tsaye ba, hankalinsa a tashe ya ɗora hannu biyu akai kamar zai fashe da kuka. Da raunataccen murya ya buɗe baki ya ce,

“Yaya…”

“Khamis! A matsayina na Yayanka da yake ta ɗaukar ɗawainiyarka tun kana ɗan ƙarami ka san idan na tsine maka zai kama ka ko?”

Wani jiri ne ya nemi kwasarsa ya zubar a ƙasa saboda tsananin firgici da tashin hankalin kalaman da yaji yana fita a bakin ɗan’uwansa. Da saurin gaske yasa hannu biyu ya dafe kujerar gabansa da a idanunsa yake ganin ta rarrabu huɗu. 

Ya kasa amsa maganar ɗan’uwansa. Da lalube kamar makaho ya koma ya zauna kan kujerar da ya tashi. Ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana hawaye. 

Wani mugun tsanar Firdausi na ƙara cika zuciyarsa. Tunda har akanta Yayansa da yake kamar mahaifinsa yana ikirarin zai iya tsine mishi, lallai abu ya girmama.

Tsinuwa dai? mummunar kalmar da duk iskancin da yake yi ko a suɓutar baki Yaya bai taɓa furtawa ba.

Sai a kanta? bayan wannan a karon banza Yayan ya mare shi har sau biyu. 

Aka yi mishi tsinannen duka kamar an samu jaki, ko kuma waɗanda Allah ya aiko su mishi hukunci tun a duniya.

‘Shi kam me zaiyi da Firdausi? Wallahi tallahi idan za ta mutu bazai aure ta ba. Aure tsakaninshi da ita haihata haihata. Abu ne da ko a mugun mafarki bazai taɓa faruwa ba balle a rayuwa ta zahiri. Allah dai ya fitar da shi daga gurinnan lafiya, dukansu zai shayar da su ruwan mamaki mai yawan gaske.

Alhaji Yusuf ya kawar da kanshi daga gurin Khamis ya dawo da shi gurin Alhaji Lukhman, cikin sanyin murya ya cigaba da magana.

“A matsayina na Yayan Khamis idan ina da hali kuma zan duba ƙarfin zumuncin da yake tsakaninmu ni nake da ikon yi mishi duk wata hidima ta aurenshi. Na yi mishi a karon farko, a wannan lokacinma na yi alƙawarin jan ragamar komai bakin gwargwadon ƙarfina.

Idan da hali kuma ka amince ina roƙon alfarma a saka lokacin bikin nan da sati biyu masu zuwa. Kafin lokacin na gama gyara inda za su zauna da Firdausi.

Kuma wani albishir da zanyi maka shi ne da yaddar Allah zanyi iyakar ƙoƙarina gurin saka idanu akan yanayin zamantakewar aurensu. Kamar ƴar da na haifa a cikina haka zan dinga bibiyarta, don in tabbatar bai ɗauki salon zalunci da musgunawa a gareta ba.”

Wannan abu da Alhaji Yusuf yayi da kuma kalaman da ya furta ba ƙaramin farin ciki ya saka a zuciyar Alhaji Lukhman ba. Fuskarsa ta gaza ɓoye halin da zuciyarsa ke ciki. Hannayen Alhaji Yusuf ya damƙo da dariya da ƙwalla a idanunsa ya ce,

“Yusuf na gode, na gode! Yadda ka tsara haka za’ayi in Allah ya yarda. Ina roƙon Allah yadda ka faranta min Allah ya faranta maka.

Allah ya kare iyalai da ƴaƴanka daga sharrin lokacin yanzu da mai zuwa nan gaba, Allah ya shirya yayi musu albarka.”

“Ameen ya Allah”

Yaya da sauran jami’an tsaron suka amsa gaba ɗaya. Zukatansu cike da jinjina karamci da halin dattako irin na Alhaji Yusuf. Lallai yayi hankali, yayi hangen nesa, tabbas yayi abin a yaba masa, 

Gurin zamansa ya koma ya zauna, a zuciyarsa yake jin ya samu sauƙin damuwa kashi talatin da biyar cikin ɗari, kwanciyar hankali da murnar da dattijon ya nuna ya saka shi fara jin nutsuwa. 

Da ɗan murmushi a fuskarsa ya mayar da hankalinshi kan babban jami’in mai suna Labaran ya ce,

“Ranka ya daɗe ga mai laifi a zaune. Don Allah kuyi amfani da wannan damar ba tare da ɗaga ƙafa ko tausasawa ba ku tambayeshi yanzunnan ya biya kuɗaɗen da yarinya ta kashe gurin neman maganin da za ta karya asirin da yayi mata.”

Gyaɗa kai Labaran yayi, alamun gamsuwa da maganar. Amma ko da ya juya ya tambayi Khamis sai ya mutsuke idanu ya ce a yanzu dai ba shi da kuɗi.

Fuskarsa a ɗaure cikin zafin rai ya ce,

“Ina roƙon alfarma a ɗaga min ƙafa zuwa nan gaba. Zan dinga kawo dubu ashirin duk sati har in gama biya…”

“Dubu ashirin?”

Yaya ya katse shi da mamaki. Bai jira ya amsa tambayar ba cikin zafin rai ya cigaba da cewa,

“Me yasa baza ka biya su gaba ɗaya a wuce gurin ba? Ka rasa kuɗin ne ko kuwa tsabar rashin hankali ne? Ko kana buƙatar su ƙara saita ka ne ta hanyar sake lakaɗa maka wani tsinannen dukan?”

Kawar da kanshi gefe yayi ya cigaba da dagewa kan maganarsa.

“Yaya ni fa da gaske nake ba ni da kuɗi. Wallahi da gaske nake yi, to menene ma na matsawa? Ko a kotu ai ana ba wanda zai biya bashi dama ne ya dinga kawo yadda zai iya kaɗan-kaɗan har zuwa sa’adda zai gama biy…”

“Nan ai ba kotu bane.”

Labaran ya katse shi cikin fushi.

“Kai? Ka san Allah? Wallahi sai ka biya kuɗinnan a yau, a yanzu, babu ɗagin ƙafa ko na zuwa anjima ballantana gobe.

Idan kuma ba ka da kuɗi sai ka bada kadara ya fanshi tsabar kuɗin. Ko wayar hannunka na ga babba ce ai, Iphone 11pro. 

Sai mu cire maka layukan ka da memory mu buga gwanjonta a gurin…”

“Wallahi Tallahi duk wanda yayi kuskuren taɓa min waya sai yayi da-na sani mai tsanani, kar ka taɓa min wata, ina gargaɗinka kar ka kuskura ko da wasa ka sake tunanin taɓa min wayata.”

Ya faɗa cikin tashin hankali, sai aika ma da Labaran wani fusataccen kallo yake yi, kamar ya manta luguden dukan da ya saka ƙananan ma’aikatan gurin suka yi mishi ɗazun.

“Hmmm! Lallai ma yaron nan, in dai kana son wayarka ka biya kuɗaɗen. Na lura har yanzu kana ji da sauran zafin kai.

Idan ka biya za mu bada belinka, albarkacin ɗan’uwanka mai mutunci, zurfin hankali da tunani, ba don kai ɗan’iska tantiri mara mutunci ba.

Kuma sati ɗaya za mu baka ka tabbatar ka warware asirin da kayi ma yarinyar nan, idan ba haka ba wallahi sai na ɗaure ka har igiya tayi rara. Zan nuna maka kai ƙaramin ɗan iska ne, baka isa ka ja da hukuma ba.”

Ƙoƙarin sassauta fusatarsa yayi, tunanin idan bai aje duk wani tsiya a gefe ya kwantar da kanshi ba baza su rabu lafiya da mutanennan ba. A raunane ya kalli Yayansa ya ce,

“Yaya, don Allah ka ɗaukar min lamuni. Da gaske nake, babu kuɗinnan. A yanzu kuɗin cikin akawun ɗina basu wuce dubu tamanin ba. Ka biya kuɗaɗen, nan gaba kaɗan zan dawo maka da su…”

“Khamis! Ina tabbatar maka a wannan gaɓar ƙwandalata baza tayi ciwon kai ba. Bazan taɓa biya maka kuɗi akan zunubin da ka aikata wanda son zuciya ne yaja gorarka gurin aikatawa. Ka biya su kuɗinnan su sallameka mu tafi, idan babu kuɗi ka basu kayan kuɗi. Idan ba ka so a taɓa maka wayarka sai ka basu makullin motarka. Ko gobe idan ka kawo kuɗin ka karɓi makullinka.”

A yadda yake ji, saboda zafin zuciya da matsanancin ɓacin rai kamar ya ɗora hannu biyu akai yai ta rusa ihu. Amma ya san ko ya aikata hakan babu ɗaya daga cikin abubuwan da suka faru ko kuma waɗanda suke shirin faruwa da zai canza.

Yana ji yana gani haka ya miƙa makullin motarsa. Motarsa da a ababensa masu matuƙar muhimmanci a rayuwansa daga waya sai ita. Wayarsa ita ce tsananin farko da yake takawa gurin tsara harkar ɓoyayyiyar sana’arsa da babu wanda ya sanshi da ita.

Motarsa kuwa ita ce mai muhimmanci lamba ta biyu, da ita yake kutsawa ko ina a faɗin jihar kaduna da maƙwafta yana ɗauko kadarorin da suka zame masa manyan jarin sana’arsa.

Rabuwa da ɗaya daga cikin ababe biyunnan a daidai wannan loikaci da harkokinsa suka kankama ba abu ne mai sauƙi ba. Duk inda zai nemo kuɗi dole ya nemo ya fanshi motarsa.

Tun kafin la’asar Alhaji Yusuf ya isa gurinnan, basu gama ba har ga shi yanzu ana kiran sallar magrib. Alfarma ya nema aka gaggauta gama komai, bayan sun kawo wasu takardu biyu Khamis ya saka hannu. Takarda ta farko sharaɗi ne da aka gindaya masa ta lallai ya karya asirin da yayi ma Firdausi cikin sati ɗaya. Takarda ta biyu kuma ta beli ce, ya saka hannu Yayansa ya saka hannu. Saboda sharaɗin sai ya karya asirinnan shi yasa ba’a kashe case ɗin a wannan dare ba.

*****

Tunda suka fita daga State CID a hanyarsu ta komawa gida babu kalmar da ta shiga tsakanin su biyun.

A yadda Khamis yayi tsammani, suna shiga mota Yaya zai rufe shi da faɗa a zafafe kamar zai dake shi, haka yake masa a baya idan ya ɓallo wata rigimar har ta kaishi ga zuwa ofishin ƴan sanda.

Sunkuyar da kanshi yake yi ya cigaba da sauraren Yayan nasa, daga bisani bayan faɗan sai kuma nasiha ya biyo baya a tausashe. Daga nan sai ya bayar da haƙuri, ya kuma ɗauki alƙawari da rantsuwar bazai sake ba. Amma ba ya hana shi ya sake.

Yau dai Yaya shiru yayi, bai ce masa ko ‘a’ ba. Hankalinsa ya tattara ne gaba ɗaya kan tuƙin da yake yi.

Wannan halin ko in kulan kuma sai ya ƙara jefa ƙanin cikin wasu-wasi da damuwa. Ya daɗe yana satar kallon Yayan, daƙyar dai ya buɗe baki da murya mai rauni ya kawar da shirun da yake tsakaninsu ta hanyar cewa, 

“Yaya, don Allah kayi haƙuri ka yafe min.”

Shiru yayi mishi, kamar ba da shi yake magana ba. A madadin ya amsa ma sai ya ƙara mayar da hankalinshi kan tuƙin da yake yi a gaggauce. Burinsa ya isa gidan Khamis ya aje shi cikin iyalansa, shi kuma ya wuce nasa gidan yayi sallolin da ake bin shi a nutse. Tunawa da jam’in  sallolin da ya rasa haka kawai akan aikin banza yasa shi jan tsaki ƙasa-ƙasa.

Shagwargwaɓe fuska yayi ya sake cewa,

“Yaya don Allah ka ce wani abu mana…”

“Saurara Khamis!!! Ka tsahirta min tun kafin in sauke ka anan inyi tafiyata. A wannan gaɓar ba ni da wani abu da zan ce maka, duk abinda kake so ka cigaba da yi.

In dai duniya ce ga ka ga ta nan! Ta fi bagaruwa iya jima. Wanda bai zo bama jiransa take yi. Amma kar ka manta, abinda kayi shi za’ayi maka. Wannan faɗi ne na Allah SWT. Kar ka manta, ka haifa, a cikin ƴaƴanka biyar mata ne guda huɗu namiji ɗaya.

Me kake tunani idan juyin juya hali irin na Lokaci ya zo maka da baƙin al’amuran da baka taɓa tsammani ba? Da dai ace kai ɗin mai jin shawara ne, sai in ce maka ka tuba, ka hankalta, ka gyara kura-kuranka tun kafin Lokaci ya ƙure maka!!!”

Har suka isa gidan Khamis babu wanda ya sake cewa uffan!

“Na gode Yaya, Allah ya ƙara zumunci. Allah ya mayar da kai gida lafiya.”

Saboda takaici da baƙin halayen Khamis ɗin ya kasa amsa addu’o’in a fili. A zuciyarsa ya amsa, yaja motarsa yayi gaba. Har ya bar unguwar yana kallon ƙanin nasa tsaye a inda ya barshi, hannuwansa naɗe a ƙirji yana kallon motarsa.

“Hmmm! Allah ya shirye ka.”

Ya bishi da kyakkyawar addu’a bayan ya sauke ajiyar zuciya.

Bayan ɓacewar motar Yaya a idanunsa cikin nutsuwa yana ɗingishi saboda dukan da suka yi mishi ya taka a hankali zuwa ƙofar gidansa. Daf da zai shiga ciki ya ƙara takwarkwashewa sosai, alamu mai bayyana ba ƙaramin jin jiki yake yi ba.

Ya cigaba da tafiya zuwa cikin gidan hannunsa dafe da bango, sai wani irin numfashi mai ƙarfi yake ja kuma sama-sama, kamar wanda mala’ikan mutuwa ke gaf da zare masa rai.

Nishin da yake yi ne ya fara ratsowa cikin kunnuwanta, tana tsaye a ƙofar kicin, a hannayenta riƙe da ɗan madaidaicin kular abinci.

Tsuru tayi guri ɗaya fuskarta na bayyana tsoro, cikin dakiya ta ƙara saurarawa tana tunanin nishin menene wannan?

Bayyanar Khamis da irin halin da ta ganshi a ciki yasa cikin tashin hankali ta saki kular hannunta a ƙasa.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Daddy me ya same ka? Ka yi hatsari ne?”

Ta tambayeshi hankalinta a tashe, kular abincin ta tsallake a gaggauce ta ƙarasa gare shi, ganin yana ƙoƙarin zubewa a ƙasa daga dafa bangon da yake yi.

Da sauri ta tallabe shi a jikinta sai suka zube a dandaryar simintin tsakar gidan. Ganin irin manyan ciwukan da suke jikinsa yasa idanunta ciccikowa da hawaye, lokaci ɗaya suka fara zuba da sauri kamar ab buɗe famfo. Hawayen da ke bayyana tausayi haɗe da ƙauna wacce ke cakuɗe da matsananciyar soyayya.

Salati da maganganun uwar da suka biyo baya shi ya janyo hankalin babbar ƴarsu Munauwara da ƙannenta biyu, da gudu suka fito don ganin abinda yake faruwa. 

Arba da mahaifinsu cikin mawuyacin hali yasa suka tsaya turus a guri ɗaya, kamar waɗanda basu tabbatar da ganin idanunsu ba.

Ko tunanin me suka yi kuma da gudu suka ƙarasa gurin iyayen suna tambayar me ya sami Daddynsu? Da suka rasa amsa a bakin ɗaya daga cikin iyayen sai suka bi sahun uwar wurin fashewa da kuka. Munauwara da tafi duk sauran ƴaƴan shaƙuwa da uban sai tumami take yi a ƙasa tana ƙara ƙarfin kukanta.

Ihun da take yi ya janyo ƴan ƙananan ƴaƴan biyu da suke cikin ɗaki suna kallo fitowa waje da sauri. Duk da basu da wayau ganin halin da mahaifinsu ke ciki da irin kukan da Mahaiyarsu da yayyin ke yi yasa suma suka sa kuka. 

Jin da yayi kukansu na neman hawa mishi kai yasa shi ɗan motsawa kaɗan, saɓanin da da ya kwanta lankaf kamar wanda ya suma.

Asalinsa ba mutum bane mai son hayaniya ko kaɗan. Ko da Allah ya bashi tarin ƴaƴa da ƙuruciyarsa in dai yana gida da uwar da ƴaƴan har wani nutsuwa suke ƙarawa a cikin wanda suke da shi.

Mar-mar ya fara yi da idanunsa kamar zai tashi aljanu. Ya mele baki gefe ɗaya, sai kuma ya ɗan buɗe bakin kaɗan ya ce

“Ku…yi… haƙuri… Na sami ɗan… ƙaramin hatsari ne.. Ba.. na son kuka…”

Yayi maganar a rarrabe. Sai cije baki yake yi yana runtse idanu da ƙyaƙƙyaftawa.

Daƙyar Ziyada matar Khamis wacce yaransu suke kira da Mummy ta iya tsayar da hawayenta. Ta rarrashi yaran suka yi shiru. 

Sai kuma suka fara tarairayarsa da nuna masa kulawa, kamar za su cire ciwon su dawo da shi jikinsu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 3Lokaci 5 >>

2 thoughts on “Lokaci 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.