"Kuɗi... ƙare magana."
Wayarsa ya ɗauka ya buɗe saƙonnin da ke ciki, kai tsaye ya shiga gurin seaching ya lalubo lambar ƙanin mahaifinsa. Kafin ya kira shi a waya, musayar saƙonnin da suka yi ya dinga bibiya har zuwa kan saƙon da Kawun ya turo mishi mai ɗauke da Akawun ɗin shi na banki yana umartar Khamis ɗin ya tura mishi dubu ashirin. Ko a yanzu, dubu talatin ya tura mishi, sai da ya tabbatar kuɗaɗen sun shiga kafin ya danna masa kira.
Da gaske fa kuɗi ƙare magana ce. Bayan musayar. . .