Skip to content
Part 40 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

“Kuɗi… ƙare magana.”

Wayarsa ya ɗauka ya buɗe saƙonnin da ke ciki, kai tsaye ya shiga gurin seaching ya lalubo lambar ƙanin mahaifinsa. Kafin ya kira shi a waya, musayar saƙonnin da suka yi ya dinga bibiya har zuwa kan saƙon da Kawun ya turo mishi mai ɗauke da Akawun ɗin shi na banki yana umartar Khamis ɗin ya tura mishi dubu ashirin. Ko a yanzu, dubu talatin ya tura mishi, sai da ya tabbatar kuɗaɗen sun shiga kafin ya danna masa kira.

Da gaske fa kuɗi ƙare magana ce. Bayan musayar gaisuwa a tsakani, da tambayan lafiyar iyalai ta ko wane ɓangare, abinda ya fara cewa shi ne,

“Kawu ka ga saƙo?”

“Eh! Na gani Khamisu. Ina shirin in kira ne sai ka kira. Wani abun za’ayi da su ne?”

“A’a Kawu. Na turo maka ne kawai ka ɗanyi cefane…”

Tun kafin ya aje numfashin maganarsa Kawun ya fara jero addu’o’in fatan alkhairi da fatan Allah ya ƙara buɗi. A bayyane da matsananciyar jin daɗi a muryarsa yake kiran sunan Iyayen Khamis da addu’ar Allah ya gafarta musu.

Bayan ya gama jero addu’o’in, a ladabce Khamis ya shigar masa da buƙatarsa wacce ita ce ainahin dalilin da yasa yayi mishi kyautan kuɗaɗen.

“Ma sha Allah tubarakallah! Yanzu Hamisu kana nufin ƴar gidan Sheik Abulfatahi kake neman aure? Har ma shi da kanshi ya buƙaci gobe ka je? Lallai wannan abin alfahari ne a kafatanin zuri’armu gaba ɗaya. Allah ya tabbatar mana da alkhairi.”

“Amin ya Allah”

Ya amsa addu’ar yana jin wani matsanancin daɗi da farin ciki a zuciyarsa, ganin yadda Kawu ya karɓi maganar hannu bibiyu har ma ya yaba da al’amarin sosai da sosai. Kalaman da yaso ji daga bakin ɗan’uwansa bai samu ba sai ga su ya same su daga bakin Kawu. Da gaskiyar bahaushe da ya ce idan wani ya ƙi ka da yini wani zai so ka da kwana.

“Gobe da ƙarfe nawa ne za muyi tafiyar?”
Kawu ya sake tambayarsa daga can ɓangaren.

“Ko zuwa ƙarfe tara da rabi de Kawu. Yadda sha ɗaya na safe za tayi mana acan. Duk dai yadda ake ciki in Allah ya yarda zuwa la’asar mun gama komai sai mu juyo kaduna.”
Ya amsa yana mai sake jin tabbaci a zuciyarsa, yadda ya gama tsara komai haka zai faru.

“To shi kenan! Babu matsala. Goben in Allah ya yarda zan fito da wuri, idan na fito zan kira ka sai muyi mahaɗa a bakin titi. Kana ganin in taho ni kaɗai ko in samu Mal Sani mu taho tare?”

“A’a! Kai kaɗai ma ka isa Kawu. Idan mun isa Zaria akwai Baban abokina da tun farko shi na tura tambayar izini, da shi za mu haɗu sai mu tafi mu uku.”

“To shi kenan”

Da haka suka rabu. Zukatansu cike da farin cikin samun abinda basu tsammata ba. Kawu ya samu maƙudan kuɗaɗe babu cas babu as! Shi kuma Khamis ya samu amincewar Kawu zai masa rakiya cikin ruwan sanyi ba tare da wani ja’in-ja ko ƙorafi ba.

Bai ɓata lokaci a tunani ba, tea da yace zai sha ma bai fita falo ba balle ya sha. Daga nan kayan barci kawai ya zura a jikinsa yabi lafiyar gado. Zuciyarsa cike da fatan a gobe a gama komai na neman auren Bilkisu, idan so samu ne, shi har sadakinta zai biya a goben. Domin kuɗi, ba matsalarsa bace.

*****

Tsawon daƙiƙu talatin bayan musayar gaisuwa a tsakaninsu babban malamin ya ɗauka yana ƙare musu kallo. A idanunshi sosai yake ganin girman dattijan da suka yi ma yaron rakiya gurin amsa kiran da yayi masa.

Har ma yake ayyanawa a zuciyarsa da abin zai iya yiwuwa tabbas da ya sauƙaƙa. Amma lamarin abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba. Ko kusa haɗin bai shiga ba, yaron ba irin wanda ko a mugun mafarki yake tunanin zai iya haɗa zuri’a da mai irin halayenshi bane.
“Kuyi Alhaji. Na ji daɗi sosai da kuka yiwa Khamis rakiya gurin amsa kiran da nayi mishi. Wannan shi ya sake tabbatar min da karin maganar nan ta Mal Bahaushe da yake cewa hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar.

Amma ina so ku tuna wani abu guda ɗaya. Ingantaccen hadith ne na fiyayyen halitta SAW ya ce, idan mutumin da kuka yarda da Addininsa da ɗabi’unsa ya zo neman auren ƴarku, ku aura masa, idan kun ƙi za ku sabbabar da fitina a doron ƙasa. Da wannan dalilin nake mai ba ku haƙuri…”

A firgice Khamis da tun fara wannan sharar fagen na Sheik ya haɗa zufa yayi sharkaf, idanunsa warwaje ya ƙura ma shehin idanu, ƙirjinsa sai bugun tara-tara yake yi. Bakinsa sai mar-mar yake yi kamar mai shirin cewa wani abu, amma ko uhumm ya kasa ƙwatowa daga cikin bakinsa.

“Duk wasu bincike da ya kamata in saka ayi na sa anyi, kuma ba mutum ɗaya ba ba biyu ba. Bincike ne sahihi na adalci akan halaye, mu’amalat, sana’a, tarbiya, iyalan Khamis. Zancen gaskiya shi ne bayan tattara duk wasu bayanai na yanke shawarar bazan iya aurar da ƴata ga matashi mai halayen Khamis ba….”

Wani irin daka – tsalle da Khamis yayi zuwa gaban Sheik sai da ya ba duk mazauna falon tsoro. Yayyin Bilkisu maza biyu da suke zaune a ƙasa kusa da ƙafafun Sheik har sun miƙe za su janye shi Sheik ya ɗaga musu hannu alamar dakatarwa.

Khamis da sam hankalinshi ba shi akan abinda yake faruwa a firgice ya damƙi ƙafar Sheik na dama, kamar ƙaramin yaro ya fashe da ƙaƙƙarfan kuka. Bakinsa na ruwa, fuskarsa na bayyana matsanancin tashin hankalin da zuciyarsa take ciki, a kiɗime, da wani in-ina da sam babu a muryarsa ya fara magana a ɗimauce.
“Inna lillahi… Na shiga uku!! Malam! Sheik! Akaramakallahu… Don girman Allah SWT… Don darajar Fiyayyen Halitta SAW kar ka hana min auren Bilkisu… Na rantse da Allah da gaske nake son ta. Zan daina aikata duk munanan halayen da nake aikatawa matuƙar za ka bani aurenta…”

“Bazan aura maka ita ba Khamis! Idan za ka tuba kayi tuba taubatun Nasuha ba don a aura maka Bilkisu ba. Magana ta ƙarshe kenan! Ina mai baka haƙuri.”
Shehin malamin ya sake faɗa da dakakkiyar muryar da ke nuna tabbas fa wannan hukuncin tasa ita ce ƙarshe.

Kawun Khamis, Alhaji Yahaya, da Amininsa Alh Ibrahim an rasa wanda zaiyi yunƙurin yin karan-tsaye ko bada haƙuri ga maganar Malam ɗin. Duk kuwa da yadda kukan da Khamis ke rusawa yana jan numfarfashi sama-sama kamar mai shirin suma ya tsaya musu a ƙahon zuci. Amma Malam ɗin yayi musu kwarjinin da baza su iya ja’inja da maganarshi ba.

“Kuyi haƙuri Alhaji. Don Allah kar ku ɗauki wannan al’amari a matsayin tozarci ko cin fuska. Rayuwarmu ɗungurun-gun Ubangiji bai bar mu sake ba. A komai sai da Allah da Manzonsa SAW suka saka mana hukunce-hukunce da hanyar da za mubi don cimma matsaya ingantacciya. Khamis bai cancanci auren Nana Bilkisu ba, amma ina mishi addu’ar Allah ya shirye shi, idan ya shiryu ina mishi fatan Allah ya haɗa shi da nagartacciyar yarinya da ta fi Nana Bilkisu ta ko wane ɓangare. Assalamu alaikum!”

Da bismillah a bakinsa ya yunƙura zai miƙe tsaye don ficewa daga falon kawai sai Khamis ya sake ƙanƙame shi yana kuka.

Girgiza kai kawai Sheik yayi, a hankali ya fara yunƙurin ɓanɓare ƙafafunsa, amma duk yadda ya so ya ƙwace ƙafafunshi ya kasa saboda riƙo ne Khamis yayi mishi ba na wasa ba. Kuma ya kasa cewa komai, sai kuka yake rusawa yana sake ƙwaƙumo ƙafafun Sheik ɗin, kamar dai wanda aka raɗawa riƙe ƙafafun shi zai sa Shehin ya canza ra’ayinshi.

A wannan karon, babu yadda Sheik ya iya. Da hannu yayi ma ƴaƴansa umarni suka ɓamɓare hannuwan Khamis daga ƙafafunshi, bayan ɓamɓarewar basu ƙyale shi haka ba, sai da suka fice da shi daga falon ganawar yana ihu yana kururuwa da ƙoƙarin zillewa amma basu sake shi ba sai da suka kai shi cikin motarsu suka hurga shi ciki a wulaƙance kamar kayan wanki.

“Ka shiga taitayinka fa, kar ka kuskura kayi yunƙurin kawo mana tantiranci anan gidan. Ka ƙara gaba da mummunar sana’arka ta kawalci da neman mata. Bilkisu ta fi ƙarfin auren ɗan’iska irin ka. Idan kuma kayi yunƙurin fitowa na rantse da Allah sai mun naɗa maka matsiyacin duka a gurinnan.”
Ɗaya daga cikinsu biyun wanda da alamu ya fi ɗan’uwansa rashin haƙuri ya faɗi haka ga Khamis fuskarsa a ɗaure tamau.

Acan cikin falon baƙin, jiki a sanyaye suka qarasa sallama a tsakaninsu. Suka fice daga falon gwuiyawu a sake kamar waɗanda suka yi amai da gudawa. Haka suka shige mota duk cikinsu an rasa mai ƙwarin gwuiwar da zai iya ɗaga idanu ya ƙare ma harabar gidan Malam ɗin da ke cike da ɗalibansa kallo, a muzance suke. Gani suke kamar kowa kallonsu yake yi, kuma duk an gama sanin abinda suka zo nema basu samu ba.

A ɗazu da suke hanyar tahowa gidan, Khamis ne yake tuƙa motar. Fuskarsa ɗauke da yalwataccen farin ciki yana karanta musu irin matsanancin farin ciki da alfaharin da zaiyi idan aka mallaka mishi Nana Bilkisu.

A yanzu kam dole tsarin ya canza, zaune Khamis yake a kujeran baya na motar kamar mutum-mutumi. Ya ƙura ma guri ɗaya idanu, duk yadda Kawunsa ya dinga kiran sunansa yana umartarsa ya miƙo makullin motar ko motsi baiyi ba. Sai Kawun ne ya zagaya ya buɗe baya ɓangaren da Khamis ɗin ke zaune ya laluba aljihunsa ya ɗauki makullin motar. Ya shiga mazaunin direba yaja motar sannu a hankali suka fice daga gidan.

Zaman ƙuda ne ya gudana tsakaninsu har suka ƙarasa ƙofar gidan Alhaji Yahaya suka sauka. Kamar wanda ya haɗiyi ƙashi, daƙyar Kawu ya iya buɗe baki yayi musu godiya yaja motar suka kama hanyar komawa Kaduna, har lokacin ko ƙwaƙƙwaran motsi Khamis baiyi ba balle asa ran zai tanka ko ya buɗe baki ya furta A domin samun sauƙin ƙuncin da ke danƙare da zuciyarsa.

*****

Durƙushe gwuiyawu bibiyu kamar masu neman gafara a gaban malamin tsubbun da Ramlatu ta raka Samira a karo na farko. Bayan Samirar ta shafe kwanaki huɗu tana zarya gidansu Ramlatun safe da yamma.

Nutsuwa sosai suka yi a gaban malamin, kacokan suka mayar da hankulansu gare shi suna sauraren bayanan da yake faɗa musu kamar wasu masu ɗaukar darasi. Bayan tsawon lokacin da ya shafe yana rubutu a cikin farantin da ke cike da yashi a gabansa yana yi yana gogewa.

Kamar saukar aradu, haka maganarsa ta dira a kunnuwan Samira. Hankalinta a tashe ta nemi zama daga durƙushen da take, da saurin gaske Ramlatu wacce suke yiwa inkiya da Lovina ta ankarar da ita mafi munin kuskuren da take shirin aikatawa.

“Aure fa babu fashi a tsakanin waɗannan masoya biyu. Dolen-dole sai an yi shi. Ga shi nan na gani, rabone na zuri’a ba ɗaya ba ba biyu ba a tsakaninsu, idan kuwa har mutum yace zai yi kuskuren ratsawa tsakanin wannan rabon, to lallai zai iya rasa ransa!”
A karo na biyu ya sake maimaita mata maganganun da suke tamkar saukar ruwan dalma a kunnuwanta. Ba tare da damuwa da yanayin ɗimuwa da tashin hankalin da take ciki ba.

A zabure, hannuwa bibiyu dafe da ƙirji, idanunta ciccike da hawaye da murya mai bayyana maɗaukakin tashin hankali tace,
“Shi kenan! Na shiga uku na lalace! Yanzu don Allah don Annabi Malam menene mafita? Don Allah ka taimaka min, ka tallafa min ka hana yiwuwar auren nan! Idan aka yi auren nan zuciyata bugawa za tayi.”

Ƙura mata idanu ɗan kututturen Malamin yayi na wasu daƙiƙu, can kuma sai ya kece da wata mahaukaciyar dariya mai cike da firgitarwa. Can kuma ɗif! Ya tsayar da dariyar kamar ɗaukewar ruwan sama.

Ya ɗauko wani ƙatoton carbi mai tsayi wanda aka yi da wasu irin abubuwa da a iya tsawon rayuwar Samira bata taɓa ganin irin carbin ba. Ya fara ja yana furta wasu irin kalamai idanuwanshi a rufe. Ya ɗauki a kalla mintuna uku cikakku kafin ya buɗe idanun, ya jefa mata carbin a gabanta tare da umartarta da ta zaɓi ɗaya.

Cikin rawar hannu da tsoro ta ɗauka kamar yadda ya umarceta. A karo na biyu ya ƙara jan carbin na tsawon wasu daƙiƙu ya sake ce mata ta zaɓa, sai da suka yi hakan sau shida, kafin ya ƙura ma zaɓinta na ƙarshe idanu sai kuma ya mayar da carbin ya ajiye.

Ya ɗauko wani fai-fai da yake cike da rairayi saɓanin wanda yake aiki da farko ya hau zane a kai, daƙyar ta iya gane sunan Rahma da Salim da ya rubuta, sauran kuwa wasu irin jagwalgwalon rubutu ne masu kama da siddabaru.

Nan ma sai da ya jima yana yi kafin ya ɗaga kai ya kalleta fuska ɗauke da yanayi mai kama da jimami da tausayi ya ce
“Wannan aiki naki abu ne mai matuƙar wahala. Duk wata hanya da nake gani zamu ɓullowa wannan al’amari babu wata mafita mai yiwuwa sai ɗaya tal… Amma fa da matuƙar wahala.”

“Zan yi duk abinda ake so Ranka Ya dade. Na rantse da Allah, komai wahalar aikin da za’a bani zan aikata shi. Don Allah ka taimaka min, ni dai fata da burina shi ne a raba batun auren nan, ko da kuwa ni da ita za muyi biyu babu!”
Ta katse shi da sauri, bakinta na rawa.

Tsawon wasu daƙiƙu yana kallonta, a zuciyarsa yake ƙara jinjina yadda take ƙiyayya ga wannan al’amarin aure. Can sai ya ce
“Kamar yadda na fada miki wannan aure dole ne sai anyi shi saboda rabon da ke tsakaninsu. Amma za mu iya yin aikin da za’a sa komai na maganar auren ya dawo kanki. Wato ma’ana, ke ki auri Salim ɗin, a matsayin ita Rahma.”

Tun kafin ya kai ƙarshen maganganunsa, ta fara sakin wani ƙayataccen murmushi kamar bakinta zai yage
“Malam ai ni daman babban burina kenan. Ko ma menene sharaɗin aikin, tun kafin ka faɗa ina mai sake baka tabbacin zan yi komai wahalarshi. In dai zan auri Salim, to zan iya yin komai akan hakan, na rantse da Allah Wallahi!”

“Aikin ki aiki ne marar wahala a wajena kenan. Amma ke a wajenki, wataƙila ki ga wahalarsa. Da farko dai, za ki kawo mana baƙin muzuru wanda ya shekara aƙalla biyar a duniya. Za ki kawo mana zuciyar tsohuwar kyanwa wadda itama ta shekara biyar. Za ki kawo mana auren baƙaƙen tantabaru guda uku, da jajayen gashin dawisu guda bakwai. Zaki kawo mana gashin gaban jikin gawa mace da aka binne kwanaki uku da suka wuce. Na ƙarshe kuma, za ki kawo mana gashin kan Rahma da farcenta. Zamu haɗe waɗannan kayayyakin duka muyi aiki da su, wasu kuma zamu haɗa miki kwalli wanda zaki yi tozali da shi. Da zarar kun haɗa ido da Salim, to shi kenan, duk wata soyayya da yake yiwa Rahma zata dawo kanki, haka ƴaƴan da zata haifar mishi zasu dawo ke zaki haife su!”

Duk da yadda ƙarshen maganarsa ta faranta mata rai, bata saki jiki da murna ba saboda ƙalubalen da ke tattare da biyan buƙatar aikin. Burinta maganganunsa na ƙarshe su tabbata, sai dai ba anan gizo yake saƙar ba.

<< Lokaci 39Lokaci 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×