"Subhanallah! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Sheik, Allah ya huci zuciyarka. Wallahi Tallahi ko kaɗan ban san me yake faruwa ba. Kuma yanzunnan muka rabu da Falalu, na aike shi kasuwa ya karɓo min saƙo a gurin Sarkin Fawa... Bari in je kasuwar in same shi. Ga mu nan tahowa gidan yanzunnan..."
"Alhaji, kayi haƙuri baza mu jira zuwanka ba. In dai tunanin da muke yi gaskiya ne. Falalu abokin Khamis ne, zai iya yiwuwa Khamis ne yasa shi aikata wannan abun domin ya samu nasarar guduwa da Nana Bilkisu tunda mun hana shi. . .
Ai shi kenan asirin ka ya tonu Khamis
Karyar ka ta kare