Skip to content
Part 45 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

“Subhanallah! Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Sheik, Allah ya huci zuciyarka. Wallahi Tallahi ko kaɗan ban san me yake faruwa ba. Kuma yanzunnan muka rabu da Falalu, na aike shi kasuwa ya karɓo min saƙo a gurin Sarkin Fawa… Bari in je kasuwar in same shi. Ga mu nan tahowa gidan yanzunnan…”

“Alhaji, kayi haƙuri baza mu jira zuwanka ba. In dai tunanin da muke yi gaskiya ne. Falalu abokin Khamis ne, zai iya yiwuwa Khamis ne yasa shi aikata wannan abun domin ya samu nasarar guduwa da Nana Bilkisu tunda mun hana shi auren ta.

Yanzu abinda za kayi mana guda ɗaya ne, ka kira Falalu ya dawo gida. Amma don Allah kar ka sanar da shi halin da ake ciki, ga mu nan zuwa gidan naka.”

Alhaji Idris ne ya kora ma mahaifin Falalu wannan bayanin, bayan samun amsar gamsuwa daga bakin Alhaji Yahaya sai ya katse wayar Sheik ɗin.

Ya mayar da idanunsa ga ƴan’uwansa da Sheik ya ce,

“Baaba kai ka zauna a gida. Bari muje gidansu Falalun…”

“Bazan zauna ba Idris. Ko na zauna hankalina bazai taɓa kwanciya ba in dai ba na san halin da take ciki bane. Mu tafi gaba ɗaya.”

Malam da ƴaƴansa uku, mahaifin Sauda da ita kanta Sauda suka shiga mota zuwa gidansu Falalu. Har lokacin Sauda bata daina kuka ba. Duk yadda Sheik yayi nacin mahaifin Sauda ya wuce da ita gida ya ƙi, ya ce babu inda za taje matuƙar ba Nana Bilkisu ce aka dawo da ita gida cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali ba.

Suna hanyar tafiya Alhaji Idris ya buƙaci a shigo da ƴan sanda cikin al’amarin, saboda tsoron kar Falalu ya kawo musu taurin kai gurin bayyana in da Bilkisu take.

“A dakata tukuna Idris, ba na buƙatar shigo da ƴan sanda cikin maganar nan matuƙar ba mafita aka rasa gaba ɗaya ba. Ko iyayenku mata, ba na fatan ku sanar da su halin da ake ciki.”

Sheik ya faɗa a sanyaye.

Ko da suka isa, kwarjininsu Sheik da ganin idanun mahaifinsa ya hana Falalu yi musu taurin kai. Bai ɓoye musu ba ya faɗa musu duk yadda suka yi da Khamis da kuma inda Bilkisu take a halin yanzu.

In da Allah ya sauƙaƙa al’amarin shi ne Khamis bai ɓoye ma Falalu in da zai kai Bilkisu bayan ya ɗauketa ba.

“Fale gidana zan kai ta in ɓoye ta. Na san gidana ne guri na ƙarshe da ko da al’amarin ya faru baza’a taɓa tunanin zan kai ta gidana ba. Ina tsoron kai ta hotel saboda gudun abinda zai je yazo. Akwai ƙwaƙƙwaran haɗin kai da soyayya tsakanina da Ziyada, na san za ta fahimce ni idan nayi mata bayanin wacece Bilkisu.”

Ya faɗa musu kamar yadda Khamis ya faɗa mishi.

Kyawawan zafafan azababbun maruka huɗu mahaifinsa ya sauke masa a kumatunsa hagu da dama bayan ya faɗa musu ya samu nasarar shigar da Bilkisu cikin motarsa ne bayan ya maƙureta ya shaƙa mata garin hodar Iblis…

“Na rantse da Allah babu abinda zai hana in tsine maka matuƙar muka je gidan Khamis muka tarar ya keta alfarmar yarinyar nan.”
Alhaji Yahaya ya faɗi haka ga Falalu bakinsa na rawa. Hankalinsa a tashe, tsananin kunyar Sheik ya ma kasa ɗaga idanu ya kalle shi cikin ido.

Saboda sun ƙara yawa, a dole tafiyar ta zama motoci biyu. Ƙarfe huɗu da minti hamsin suka kama hanyar zuwa Kaduna daga Zariya da wani balaƴaƴƴen gudu kamar masu shirin barin duniya.

Saboda tashin hankali da fargaban da zukatan iyayen ke ciki duk yadda Malam ya tsani gudu a mota ya kasa yima Alhaji Idris maganar ya rage gudu. A yadda yake gani ma kamar ba gudu suke yi ba, ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya buɗe idanu yaga Nana Bilkisu a gabanshi.
Nutsattsiyar yarinyarsa, Hasbunallahu wa ni’imal wakeel. Ya ma kasa kwatanta irin mummunan halin da zai shiga idan wani abu ya samu Nana Bilkisu… Tsakaninshi da Khamis sai dai Allah ya saka mishi, ya samar da mummunar tabo ga zuri’arsa, irin tabon da ko a mugun mafarki bai taɓa hasashen zai faru da ire-iren zuri’arsa ba.

******

Ƙarfe shida saura minti goma na yammaci Nauwara da Mannirah suka yi sallama a ƙofar falonsu. Rangaɗaɗau suka ji muryar Daddynsu ya amsa sallamar.

Yanayin mamaki ne ya ɗan bayyana a fuskokinsu, saboda a saninsu bai da lafiya. Ba kasafai ya cika son ya buɗe baki yayi magana ba a cikin kwanakin.

“Nauwara ku shigo mana? Tsayuwar me kuke yi a bakin ƙofa?”

A karo na biyu suka sake jiyo muryarsa daga can cikin falon yana faɗin haka.

Da sauri suka cire takalmansu haɗe da kutsa kai cikin falon
“Daddy sannu da hutawa. Ya ƙarfin jiki?”
Suka haɗa baki gurin tambayarsa.

“Ina ƙannen naku?”
Ya tambayesu bayan ya amsa gaisuwar da sukai masa.

Da mamaki suka haɗa idanunsu, sai kuma suka sake haɗa baki gurin cewa
“Ai sun dawo tun da rana.”

Mannirah ce tayi mishi ƙarin bayani da cewa
“Saboda rehazal ɗin Musabaƙa da ake yi shi yasa yau ba’a tashe su ƙarfe ɗaya da rabi kamar yadda aka saba ba. Biyu da kwata daidai aka tashe su, kuma ni da kaina na kai su bakin titi na saka su a cikin keke napep. Basu dawo ba?”

Ya kasa amsa tambayar, a maimakon yayi magana ma shiru yayi yana rarraba idanu tsakanin su biyun. Kansa a kulle, ya ma rasa wane irin tunani ya kamata yayi.

“Ku shiga cikin ɗakinku kuyi wanka.”

Ya finciko maganar daƙyar daga cikin bakinsa.

Kamar za su sake magana, amma ganin yanayin fuskarsa ba walwala yasa su shigewa ɗakinsu jiki duk a sanyaye. Ga bala’in gajiya da yunwar da suka kwaso a makaranta, zuciyarsu cike da tunanin ina ƙannensu suka tsaya? A gefe guda kuma suna tunanin ina Mummy da basu ganta a cikin falo ba?

A tare suka faɗi magana mabanbanta da juna.

Nauwara ta ce
“Kila Mummy ta shiga wanka ne shi yasa bamu ganta ba…”

Ita kuma Mannirah cewa tayi
“Ina su Batula suka tsaya da basu dawo gida ba?”

Rashin sanin amsoshin tambayoyinsu yasa a gaggauce Nauwara ta shige banɗaki don watsa ruwa, mintuna uku ta fito ita ma Mannirah ta shige bayin. Sauri-sauri suke shiryawa don su fita zuwa falo su samu amsoshin tambayoyinsu a bakin Daddy.

****

A karo na barkatai tun bayan ficewar Ziyadah daga gidan, cikin ɗakinsa ya shige domin duba ko Bilkisu ta tashi. Wani abin mamaki shi ne har lokacin tana nan a yadda ya barta.

Sai dai ba kamar yadda ya shiga da ita cikin gidan har Ziyadah ta ganta ba, bayan fitar Ziyadah babu irin saƙar da shaiɗaniyar zuciyarsa bata yi masa ba. Ga zafi da raɗaɗin kalaman Ziyadah a gare shi, duk da yana ƙoƙarin shanye damuwar sakin da yayi mata ba ƙaramin dukan zuciyarsa maganar rabuwar tasu yake yi ba. Har yanzu yana son Ziyadah, son Bilkisu ne kawai ya danne nata.

Abubuwa da yawa ne suka haɗu suka caja mishi ƙwaƙwalwa. Ya kai ya kawo a cikin mummunan tunani har zuwa lokacin da shaiɗaniyar zuciyarsa ta tsaya akan ya keta alfarmar Bilkisu kafin buguwar abinda aka shaƙa mata ya sake ta. A ganinshi idan yayi haka, ko bayan farkawarta a bazai fuskanci turjiya ko taurin kai daga gare ta ba.

Tun da sun riga sun zama ɗaya. Ya gama da ita, ba ta da wani sauran mafita illah ta bashi haɗin kai su nema ma kansu hanya mai ɓullewa har zuwa cimma burinsu na auran juna.

A taƙaice dai, tarihi ne yaso maimaitawa kan Nana Bilkisu kamar yadda ya aikata ga uwar ƴaƴanshi Ziyadah.

Da ƙwarin jiki da na zuciya ya faɗa banɗakinsa ya sallo wanka, ya saka gajeren wando ya bulbula ma jikinsa turare ya haye kan gadon. Ya ɗauki tsawon mintuna goma yana rungume da ita a ƙirjinsa, daga ko ina yake jin nutsuwa na musammman yana ratsa sassan jikinsa.

Kamar ƙwai, haka ya dinga lallaɓata yana juya ta har ya cire mata manyan kayan jikinta, saura inner wears, abu ɗaya da ya dakatar da shi shi ne yana taɓa ƙasanta ya ji ƙunzugu, ƙirjinsa ne ya buga daram! Domin iya kunnuwa ya gama kunna kansa, ya gigice ya ɗimauce da ganin irin cikar halittar da Allah yayi mata.

Daƙyar ya iya dakatar da kansa bayan ya duba ra’ayil ayni ya tabbatar ba ta da tsarki. Duk da haka bai ƙyaleta ta sauƙi ba, sai da ya gama jagwalgwalata ya ɗan samu nutsuwa kafin ya janye jikinsa daga nata, a sanyaye ya shige banɗaki ya sake yin wanka a karo na biyu.

Ko da ya barta, bai mayar mata da kayan jikinta ba illa bargo da ya lulluɓa mata. Da yayi wanka kuma ya fice zuwa kicin domin nema ma kansa abinda zai sa a cikinsa, domin yunwa yake ji ba kaɗan ba.

In da Allah ya taimakeshi Ziyada ba ta rabo da ƴan kayayyakin ciye-ciye. Cake ya gani ya ɗibi wanda zai ishe shi, ya ɗauki gorar Sprite a cikin frij ya fice zuwa falo. Yana ci yana kallon T.v, shaf ya mance da batun dawowar yaranshi ƙananun da rana.

Wani tunani da ya ɗarsu a zuciyarshi yasa shi miƙewa tsaye zumbur ya fara safa da marwa a tsakar falon.

“Lallai ma Ziyada. Na rantse da Allah zan nuna mata ƙaryar iskanci take yi. Wato ko da ta fice a gidannan, tsayawa tayi a ƙofar gida su Batula suka ƙaraso ta kwashe su ta tafi da su ba tare da izini na ba ko?”

Ya jefa ma kansa tambayar a fili, rashin samun amsar tambayarsa yasa shi cigaba da saƙe-saƙe da tunanin in da zai samu Ziyada a halin yanzu.

“Ba ta so na. Don haka ƴaƴana sun haramta a gare ta har abada.”

Ya sake faɗa a fili haɗe da ɗaukar wayarsa da ke ajiye a hannun kujera.

Sauri-sauri yake scrolling har ya lalubo lambarta ya danna mata kira, cikin sa’a wayar ta shiga. Amma wani abin ban takaici da ɓacin rai a gare shi shi ne wayar tana fara ringing aka datse kiran daga can ɓangaren. Ko kafin ya sake danna kiran lambar har ta yi blocking ɗin shi.

“Daddy Mummy…”

“Nauwara ina wayarki?”
Ya katse ta daga niyyar tambayarshi inda uwar take da sauri.

Ƙirjinta ne ya buga daram! Duk da tana ɓoye abubuwa da yawa da suke cikin wayar amma ta kwana biyu bata binciki wayar ta ɓoye sabbin abubuwan da ba ta so idan binciken ƙwaƙwaf ɗin Daddy ya tashi ya rutsa da su a cikin wayarta ba.

“Tana, tana ɗaki.”

Ta amsa muryarta na ɗan rawa.

“Je ki ɗakko maza ki kira min Mummyn ku.”
Ya umarce ta a gaggauce.

“Daddy, Mummy ba ta nan ne?”
Mannirah da take tsaye ƙofar ɗakin Mummy tana ta murɗa hannun ƙofar ta ji shi a rufe ta jefa mishi tambayar.

“Ba ta…”

Shigowar Falalu cikin falon afujajan kamar an jefo shi ya hana shi ƙarasa maganar da ya fara. A tsorace ya miƙe tsaye, idanunshi warwaje akan Falalu ya buɗe baki daƙyar ya ce
“Fale…”

Da kumburarren bakinshi ya katse Khamis da cewa,

“An yanka ta tashi…”

“Daman bata yanku ba.”
Alhaji Idris da shigarsa cikin falon kenan ya faɗi haka fuskarsa a ɗaure tamau.

Cikin daƙiƙun da basu wuce biyar ba gaba ɗaya tawagar su Sheik suka shiga cikin falon, da ɗaurarrun fuskoki mai ɗauke da bayyanannen ɓacin rai da fushi sosai suke kallon Khamis.

Nan take ƙwaƙwalwarsa ta haɗa ɗaya bisa biyu ya fahimci abinda yake faruwa. Ko kafin yayi tunanin abinda zaiyi don tserar da kansa Yayyin Bilkisu biyu samari majiya ƙarfi sun rufe shi da azababben duka kamar Allah ya aiko su.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Su waye ku? Ku ƙyale mana Daddyn mu. Me yayi muku? Don girman Allah kuyi haƙuri…”

Ire-iren kalaman da ke fita daga bakin Nauwara da Mannirah kenan suna ruƙumƙume da juna a tsorace suna rusa kuka, zuciyarsu cike da tausayin mahaifinsu.

Tausayinsu ne ya kama Sheik, daga yadda suke kiran Daddy wayyo Daddy ya fahimci ƴaƴan Khamis ne. Mamaki ne ya kama shi ta yadda matashi kamar Khamis yake da waɗannan ƴanmata a matsayin ƴaƴanshi. Duk da tausayin da suka bashi bai bayar da umarnin yaran su ƙyale Khamis ba sai da ya tabbatar sun mishi ligi-ligi.

Hannu yasa ya yafito su Nauwara ya ƙara da cewa
“Ku zo nan”

A tsorace jikinsu babu inda ba ya rawa suka ƙarasa gaban Sheik suka zube a ƙasa.

“Waye wannan a gare ku?”
Yayi musu tambayar haɗe da nuna musu Kham da ke yashe a ƙasa da yatsarsa manuniya.

“Mahaifi… Mahaifinmu ne.”
Suka haɗa baki gurin amsawa da rawar murya.

Da mamaki ya sake ce musu.
“Mahaifinku? Kuna nufin duk ku biyunnan ƴaƴansa ne ba na ƴan’uwansa ba?”

A yanzu ba su da zaɓin da ya wuce ɗaga kai, alamar haka ne.

“Ina mahaifiyarku?”
Ya sake tambayarsu.

“Mintuna bakwai da suka wuce muka dawo daga islamiya. Bamu tarar da ita a gida ba.”
Nauwara ta amsa da sanyin murya, har lokacin idanunta bai daina tsiyayar da hawaye ba.

“Ina ne ɗakin mahaifinku?”

Jin wannan tambayar yasa Khamis ɗago kanshi a firgice, da shaƙaƙƙiyar murya ya fara magana yana cewa
“A’a! Nauwara a’a! Mannirah a’a! Kar ku nuna musu…”

Basu nuna ba, amma kuma idanun Mannirah na tsaye kyam a saitin ƙofar ɗakin Daddyn. Hakan yasa suka fahimci ga ɗakin nashi can.

Alh Idris, ƙannensa biyu da Aunty Zubaida Yar Bilkisu da take aure a cikin garin kaduna har sun ɗaga ƙafa da sauri za su nufi ɗakin Sheik ya dakatar da su. A ƙagauce suka tsaya suna kallon Sheik.

“Menene amfanin zuwa gidan Zubaida mu taho da ita?”
Duk shiru sukai suna kallonsa. Saboda ba su da amsar tambayarsa.

Sai shi ne ya cigaba da cewa
“Amfanin tahowa da ita shi ne a matsayinta na ƴar’uwarta mace, kuma ma’aikaciyar jinya ta shiga ciki ta duba mana a wane hali Nana Bilkisu take ciki? Idan muka samu saɓanin alkhairi a lokacin ne za mu ɗauki duk wani mataki da ya kamata wanda addini ya tanada don karɓar ma yarinya ƴancin ke ta mata haddi da yayi. Zubaida shiga ki duba mana halin da ƴar’uwarki take ciki.”

“To Baaba.”
Ta amsa a sanyaye.

Har ta kusa isa ƙofar ɗakin ya kira sunanta, a sanyaye ya sake cewa
“Ina fatan kin fahimci irin dubawar da nake nufi?”

“Na fahimta Baba.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 44Lokaci 46 >>

1 thought on “Lokaci 45”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×