Skip to content
Part 46 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Minti ɗaya, biyu, uku, har zuwa goma ba Aunty Zubaida ba labarin fitowarta daga cikin ɗakin Khamis. Wasu azababbun mintuna masu bala’in tsawo da duk mazauna falon suke ganin kamar an ɗauki awanni masu yawan gaske. Hatta su Nauwara da basu gama fahimtar abinda yake faruwa ba duk sun ƙosa ta fito su ji abinda za ta ce, daga maganar da Sheik yayi, ba ƙaramin ruɗani zukatansu suka shiga ba. Duk da basu san me mahaifinsu yayi ba, a zuci suka fara addu’ar Allah ya taƙaita al’amarin.

Sau uku Alhaji Idris yana ɗaga ƙafa kamar zai tafi cikin ɗakin sai kuma ya tsaya a inda yake. Sheik da yake zaune ya zubawa ƙofar ɗakin ido hannunsa tallabe da kunci bai san sa’adda ya miƙe tsaye ya fara safa da marwa ba, hannayensa duk biyu goye a baya.

Sauran tawagar saboda tsananin zaƙuwa da fargabar amsar da za su samu idan ta fito daga tsayuwa sulalewa suka yi suka zauna akan kafet, idanunsu zube a ƙofar ɗakin.

Agogo yana buga minti goma sha bakwai Zubaida ta murɗa ƙofar ɗakin daga ciki, ita ta fara bayyana, kafin Nana Bilkisu ta bayyana a gefenta, tana tallabe da ita ne saboda har lokacin buguwar da tayi bai sake ta ba. Abinku da wacce bata saba buguwa ba.

Wani abun ban tsoro a gare su shi ne, duk da Idanun Bilkisu na rufewa yana buɗewa ne, hawaye ke kwaranya a idanunta. Ita kuwa Aunty Zubaida idanunta sun kaɗa sunyi jajur! alamun ta ci kuka ta ƙoshi a cikin ɗakin.

Tsakanin Sheik, Alhaji Idris, matasan ƴaƴansa biyu ban san wanda ya riga isa gurinsu ba. Da saurin gaske suka tallabo Bilkisu suna rige-rigen tambayarta lafiya? Me yake damunta? Me aka yi mata?

“Baaba… Wallahi ba ni da laifi… ban san sadda saurayin Sauda ya sato ni zuwa nan ba… Don girman Allah ka yafe min…”
Bilkisu tayi maganar a rarrabe, cikin kuka. Duk da juya mata da falon ke yi haka ta ƙwace a hannun ƴan’uwanta tasa gwuiyawunta a ƙasa tana rusa kuka, hannayenta duk biyu rirriƙe da ƙafafun uban.

“Zubaida, Ya ya? Ya ake ciki? Ya batun duba min ita da nace kiyi?”
Sheik ya tambayi Zubaida ba tare da ya bi ta kan Bilkisu da ke rusa kuka tana riƙe da ƙafafunsa ba.

“Alhamdulillah! Allah ya tsare ta daga sharrinsa Baba. Tabbas! Allah ne ya tsare ta… Amma da yanzu wani zancen akr yi ba wannan ba. In da Allah ya taƙaita afkuwar mummunan abu shi ne tana cikin yanayin da in dai ba dabba bane bazai iya kusantarta a wannan halin ba…”

“Alhamdulillah!”
Suka haɗa baki gurin faɗin haka gaba ɗayansu. Suna jin wani nutsuwa da kwanciyar hankali yana ratsa zukatansu.

Sai a wannan lokacin, Sheik ya iya fuskantar ƴar tasa. Hannuwa biyu yasa ya ɗago ta tsaye sannan ya ruƙunƙumeta a ƙirjinsa yana sassauke ajiyar zuciya a jejjere.

Sannu a hankali yana riƙe da ita suka ƙarasa tsakiyar falon, har zuwa inda Khamis yake kwance yana rarraba idanu cikin mawuyacin hali, ƴaƴansa na biye da su a baya.

“Da irin wannan mummunan halin naka kake so ni in ɗauki ɗiyata in aura maka? Allah ya tsari gatari da sarar shuka. Duk da baka keta alfarmar yarinyata ba, ka kafa min mummunar tarihin da kwatan-kwacinsa bai taɓa faruwa a cikin ire-iren zuri’ata ba. Tsakanina da kai… Allah yayi min sakayya. Idan abu mai kyau ka aikata, za ka gani a ƙwaryarka, haka zalika idan mummuna ne sannu a hankali komai daɗewan Lokaci za ka girbi abinda ka shuka…”

A galabaice Khamis ya katse shi ya fara magana cikin rawar murya, hankalinsa a tashe ganin an fito da Bilkisu suna ƙoƙarin tafiya da ita.
“Sheik kayi haƙuri… Wallahi ina tsananin son Bilkisu… Ban ɗauke ta don in tozarta ka ba, sai don tunanin idan nayi haka za ka sassauto ka bani aurenta… Itama wallahi tana so na, ka tambayeta ka ji daga bakinta. Na yi alƙawarin Idan za ka bani aurenta zan daina duk wasu munanan halaye da nake aikatawa. Don Allah kar ka raba ni da ita…”

Bagagatan ɗaya daga cikin yayyen Bilkisu da maganganun Khamis suka ƙara fusata shi yayi tsalle ya dira akan hannun Khamis na dama da yake shimfiɗe akan Kafet, ji kake raƙaƙaƙas! Ƙarar karyewar wasu daga cikin ƙasusuwar hannun Khamis.

A wahalce Khamis ya saki wani gigitaccen ihu saboda tsananin azaban da yake ratsa cikin hannunsa da aka taka.

Nauwara da Mannira a tare suka fashe da ƙaƙƙarfan kuka saboda tsananin tausayin mahaifinsu, duk da yadda suke son zuwa su ruƙunƙume shi sun kasa motsawa daga inda suke, don tsoron abinda zai je yazo. Ƙarara yanzu sun fahimci abinda yake faruwa, Daddynsu ne bashi da gaskiya. Ko yana da gaskiya ma a matsayinsu na ƴaƴa mata masu rauni ba su da abinda za su iya yi a gaban waɗannan matasa majiya ƙarfi.

“Baaba, irin waɗannan shaiɗanun mutanen barinsu a doron ƙasa suna aikata abinda suka ga dama ba tare da ɗaukar mataki ba shi ke sa kullum suke ƙara dulmiya wajen cin karensu babu babbaka. Duk da babu abinda yayi mata, sakawa da yayi aka ɗauko ta ba tare da izinin iyayenta ba shi kaɗai babban laifi ne a hukumance. Ka bari in kira Ƴan sanda su tafi da shi, ya kamata a koya mishi hankali sosai ta yadda ko can gaba idan ya samu fitowa bazai ƙara gangancin aikata irin wannan abin ba…”

“Ƙyale shi Idris! Ku ƙyale shi. Duk hukuncin da hukuma za tayi masa bazai goge mummunar baƙin tabon da ya dasa a zuciyata ba. Sakayyar Allah ta fi ta mutum. Daga yau zan fara kai ƙararshi gurin Mahaliccin sammai da ƙassai, shi zai yi sakayya tsakanina da shi. Mu je.”

Haka suka fice gaba ɗaya daga cikin falon, hatta Falalu da ya kasance abokin Khamis na kurkusa ko juyawa ya kasa yi balle tunanin ya taimaka masa. Shi kanshi yana cikin matsanancin tashin hankalin hukuncin da zai karɓa daga gurin mahaifinsa idan sun koma gida.

Bai taɓa aikata abu daga baya yazo ya shiga cikin mummunar nadama irin wannan aikin ba. Tun ma kafin asirinshi ya tonu, tun da ya damƙa Bilkisu a hannun Khamis hankalinsa ya gaza kwanciya, wayarsa a kashe take, amma cike yake da fargabar abinda zai je yazo. Sai ga shi tun ba’a je ko ina ba asirinsa yayi mummunar tonuwa, a gaban mahaifin budurwar da yake yi ma matsanancin so, a gaban budurwar tasa da yake masifar so, a gaban babban malamin garinsu da ƴaƴansa da ba garin zaria kaɗai ba, ko ina ana girmama Sheik AbulFatahi. A gaban mahaifinsa da duk irin munanan ayyukan da yake aikatawa a bayan fage bai taɓa sani ba.

Da rarrafe suka ƙarasa inda mahaifinsu ke kwance magashiyyan, kuka suke rusawa kamar za su haɗiye zuciya. Tsananin ruɗewa da tashin hankali ma yasa suka rasa wane irin taimakon gaggawa ya kamata su fara bashi? Shi kuwa da yake gurmususu cikin azaban raɗaɗi ya rasa inda zai saka kansa, ba baka sai kunne. Duk yadda ihun kukan da suke yi ke ƙara mishi ƙunci da raɗaɗi ya kasa buɗe baki ya ce musu su tsahirta da kukan.

“Ku… ku… ku kira min Jamilu mai kemis.”
Ya ƙwato maganar daƙyar daga cikin bakinsa ya faɗa musu bayan tsawon lokacin da ya ɗauka ba tare da ya iya magana ba.

Firgigit suka yi, sai a lokacin suka ankara ashe fa ba kuka ne ya kamata su tasa shi a gaba suna yi ba. Mannirah ce tayi ƙarfin halin miƙewa tana rangaji saboda tashin hankali da uban kukan da suka ci ta shige ɗakinsu, hijabinta ta sako ta fice daga gidan don kiran Dr. Jamilu, wanda bayan kasancewarsa likita mai bada taimakon gaggawa a layin abokin mahaifinsu ne.

Har ta dawo gidan Dr. Jamilu na biye da ita hankali tashe da kayan aikinsa na gaggawa saboda Mannirah ta faɗa mishi halin da Daddyn ke ciki Nauwara tana inda ta barta, kuma har lokacin kukan da take yi bai tsaya ba. Damuwa ne ya haɗe mata goma da ashirin, ga fargabar halin da Daddy ke ciki, ga tunanin inda Mummy ta shiga har zuwa yammacinnan da ake kiran magrib a wasu masallatai ga tunanin inda ƙannensu suka shiga.

Daƙyar ta iya muskutawa ta matsa gefe ɗaya domin ba Likitan damar yin aikinshi cikin nutsuwa.

Hankali tashe Jamilu yake duba hannun Khamis da duk inda aka taɓa sai ya ce wash! yana fidda wasu ƙananun ƙwallah a idanunshi.
“Subhanallahi! Me ya faru da kai haka Khamis? Wannan hannun naka ai kamar karaya ce a ciki. Wasu marasa imanin ne suka yi maka irin wannan mummunan dukan na zalunci?”

Tsakanin Khamis, Nauwara da Mannirah an rasa wanda zai buɗe baki ya ce mishi ga abinda ya faru. Ƴaƴan sai sunkuyar da kawunansu ƙasa suka yi, fuskokinsu damalmale da matsanancin damuwa.

“Ɗazu da rana ina zaune a shago naga wucewar Mummynku da su Batula a cikin keke napep. Ina suka je har yanzu bata dawo ba?”
Ya sake jefa musu tambayar a karo na biyu.

Sai a lokacin suka ɗaga idanu da sauri suna kallonshi.
“Bamu san inda taje ba, muna makaranta… Dawowarmu ne muka tarar da Daddy cikin wannan tashin hankalin.”
Mannirah ta amsa mishi da sanyin murya, zuciyarta cike da tunanin inda Mummy ta tafi da ƙannensu ba tare da Daddy ya san ta tafi da yaran ba.

“Uhmmm! Allah ya kyauta gaba. Wannan hannun nashi gaskiya bazai yiwu in barshi a gida har zuwa safe ba. Tunda dai ba’a san takamaimai wace matsala ya samu a cikin ƙashin hannun ba. Dole sai dai mu tafi asibiti a darennan, ku ku zauna a gida. Tunda Mummynku bata nan bazai yiwu in tafi da ɗaya abar ɗaya a gida ba, duk yadda ake ciki zan kira ta a waya. Na san duk inda taje yanzu tana hanyar dawowa.”

“Tam! Mun gode. Daddy Allah ya baka lafiya.”
Suka faɗa a tare.

Saboda yanayin jikin Khamis ɗin duk inda aka taɓa ciwo dole sai da aka matsa da motar har kusa da ƙofar falon sannan aka tarairayo shi a hankali aka saka a cikin mota.

Yaran basu koma ciki ba sai da suka ga fitar motar daga cikin gidan. Nan falo suka zauna, suka dasa kiran Mummy a waya amma duk kiran da suka yi mata ba ta ɗagawa. Daga bisani ma idan suka kira na’ura ke faɗa musu wayar a kashe take.

*****

“Daddy ya ƙarfin jiki?

Suka haɗa baki gurin tambayarsa, muryarsu a tausashe.

Shi ma da sanyin murya mai nuna kulawa da tsananin ƙauna ya amsa musu. Cikin nutsuwa Mannirah ta matsa gefe guda ta ajiye kwandon abincin da ke riƙe a hannunta.

Daga irin kallon da suke mishi, sun fahimci yanayin sauƙi sosai da ya ƙara samuwa a jikinsa. Yau kwanansa bakwai kenan a asibitin, sosai jikinsa yayi sauƙi in aka ɗauke karayar da ke hannunsa, wannan kuma dole sai a hankali.

Tabbas! Dr. Jamilu ya cika aboki nagari. Da farko ya so ya sanar da Yaya Yusuf halin da Khamis yake ciki, sai Khamis ɗin ya dakatar da shi. Cikin nutsuwa da sanyin murya ya faɗa mishi silar afkawarsa a wannan halin da yake ciki, bai ɓpye mishi komai ba.

Bayan ya gama faɗa mishi ya ƙara da roƙonshi don girman Allah ya rufa mishi asiri, ba ya so kowa daga cikin ƴan’uwansa yasan labarin halin jinyar da yake ciki.
“Idan ka fahimci labarin dakyau za ka fahimci ni na ja ma kaina. Tun farko Yaya ya gargaɗe ni, Kawu da muka tafi tare aka ce baza a aura min ita ba nasiha mai tsawo yayi min kan inyi haƙuri in rungumi ƙaddara. In ƙyale musu ƴarsu. Da banji bari ba shi ne nake karɓar gashi a yanzu. Don Allah ka rufa min asiri aboki.”

Bayan faɗa da nuna ɓacin rai sosai akan nunar ma Khamis kuskuren da yayi na saurin sakin Ziyada, bai ƙi rufa mishi asiri kamar yadda ya nema ba.

Su Nauwara mata ne, bazai yiwu suyi zaman jinyar mahaifinsu a asibiti ba. Don haka Ƙaninsa ya ɗakko yake jinyar Khamis ɗin, su Nauwara suna gida amma su suke jigilar kai abinci da safe kafin su wuce makaranta da kuma yamma idan sun koma gida.

Saboda yadda yake ganin ƴaƴan cikin rashin walwala ba ya mishi daɗi, da kwaskwarimar zance ya zaunar da su ya faɗa musu babban kuskuren da ya tafka na sakin mahaifiyarsu.
“Kuyi haƙuri. Don Allah ku yafe min. Na san ban kyauta muku ba. Ni da kaina zan gyara kuskurena, ina jin sauƙi duk inda Ziyada ta tafi zan bita in rarraso ta ta dawo ɗakinta. Ko a yanzu ina so ku zama shaida, na mayar da ita ɗakinta.”

Bayan kukan da suka sha a dole suka yi haƙuri, tunda ba su da yadda za suyi da shi. Mahaifinsu ne, ko a turu yake kuma duk irin munanan halayenshi dole suyi haƙuri da shi.

Babbar damuwarsu rashin samunta a waya ne, kuma sun kira duk ƴan’uwanta inda suke tunanin za ta je an tabbatar musu bata je can ba. Wannan abin yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa duk yadda Daddy ke samun sauƙi sun kasa sakin jiki suyi walwala kamar da.

Saboda ya gargaɗesu akan sanarwa Yaya Yusuf halin da yake ciki babu ɗaya a cikinsu da tayi gigin tuntuɓarsa da batun cigiyar mahaifiyarsu.

Sannu a hankali zamansu a gida su kaɗai ya ba ko wacce damar cin karenta babu babbaka. Ada, duk da ɗakinsu ɗaya suna matuƙar kiyayewa gurin bayyana sirrin halin da suke ciki, ta ɓangaren harkokin social media, samarinsu, yanayin yadda suke waya da samarin, Nauwara mai tarin ƙawaye barkatai ba ta iya sakin jiki ta amsa wayar ko wacce ƙawa a cikin gidansu.

A yanzu da suke su kaɗai sannu a hankali suke sakin jiki suna harkokinsu ba tare da fargaba sosai ba. Da yake akwai banbanci na lokacin karatun Mannirah ƴar sakandire da Nauwara ƴar Jami’a. Sosai Mannirah take sakin jiki ta amsa wayar masoyinta a cikin gidansu ako ina, ba ma kamar idan ta riga Nauwara dawowa makaranta.

Kamar misalin yanzu, tana tsaye ne a gaban cabinet ɗin kicin da waya maƙale a kunnenta, fuskarta damalmale da damuwa saboda Muhsin ɗin ta ba shi da lafiya, tun jiya ya faɗa mata kanshi na matsanancin ciwo, a yanzu kuma har a wayar take jin makyarkyatan sanyin da yake yi.

“Ƙalb, wai har yanzu ciwon kan ne ko wani abu daban?”

Ta tambayeshi da damuwa sosai a muryarta kamar za ta ɗora hannu aka ta fasa ihu…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 45Lokaci 47 >>

1 thought on “Lokaci 46”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×