Skip to content
Part 47 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Shiru yayi na wasu daƙiƙu kamar bazai amsa ba, sai da ya ɗan ja fasali kafin ya amsa da muryarshi a sanyaye irin ta marasa lafiya
“Yanzu kuma zazzaɓi ne Babe, ciwon kan kaɗan ne.”

Ya ɗanyi shiru kafin ta amsa ya cigaba da cewa.

“Amma kar ki damu, zazzaɓin bai yi wani ƙarfi sosai ba, kawai dai ina ɗan jin sanyi ne. Amma na san tunda na sha magani zai sauka yanzu, in… sha… Allah…!”
Ya ƙarasa maganar a rarrabe, muryarsa na rawa.

Hankalinta ne ya ƙara ɗugunzuma, amma duba da yadda yake ƙoƙarin kwantar mata da hankali sai tayi ƙoƙarin danne damuwarta. Muryarta a shaƙe da damuwa a ƙoƙarinta na hana kanta fashewa da kuka ta ce
“To shi kenan Ƙalb. Allah Ya baka lafiya da gaggawa. Get well soon ka ji Habeebee?”

“In sha Allah Habeebtee, Thank you.”
Ya amsa mata da ɗan sautin murmushi a muryarshi.

A tare suka kashe wayar. Ta daɗe tsaye a gurin tana matsar ƙwallah na damuwa da halin da ta ji masoyinta a ciki. Daga yadda take jin muryarsa, ta san ƙarfin hali kawai yake yi. A jikinta take ji yana jin jiki. Sai da ta gama sharɓan kuka kafin tayi ƙarfin halin fara harhaɗa kayayyakin da za tayi amfani da su don yin girki.

A zuciyarta take ayyana in banda Daddy da yake asibiti, kuma har lokacin Nauwara bata dawo ba babu abinda zai saka ta yin girki a wannan halin da zuciyarta take ciki. Duk da Daddy bai cika son taliya matsayin abinci ba taliyar ta fara haramar dafawa, domin ita ce abu mai sauƙi-sauƙi da za tayi ta gama nan da nan ta shige ɗaki jinyar zuciyarta. Tana aikin amma rabin hankalinta na can tunanin halin da Muhsin yake ciki.

*****

“Umma? Ni? In sha wannan abin? menene wannan ɗin?”
Samira ta jerawa uwar tambayoyin tana yamutsa fuska kamar ta ga kashi, a fakaice take kallon ƙwaryar da baƙin ruwa mai ɗauke da garin maganin a fakaice take gallah ma ƙwaryar harara.

Zuciyarta a ƙuntace, ranta a ɓace da irin abubuwan da Umman take mata cikin kwanakin nan wanda da can baya ba haka take mata ba.

Kafin ta ce uffan sai da ta ƙara haɗe girar sama da ƙasa tayi murtuk da fuska. Sanin hali ya fi sanin kamanni, ta san halin ƴar tata zuma ce sai da wuta. Shi yasa ko da wasa bata ɗauki aniyar lallaɓata ko yi mata sakwa-sakwa akan muhimmin al’amarin da ta shafe kwanaki masu yawa tana addu’a akan tabbatuwar abu mafificin alkhairi a cikin al’amarin ba.

“Wannan ɗin da kike gani magani ne, kuma tabbas ke za ki sha. Yanzunnan ma kuwa.”
Ta sake gyara riƙon ƙwaryar a hannunta kafin ta cigaba da cewa,

“Karɓi, maza yanzunnan ki shanye kafin in ɓata miki rai.”

Narai-narai tayi da idanu ciccike da hawaye, ta buɗe baki za tayi magana Umma ta daka mata wani gigitaccen tsawa da yasa hawayen fuskarta ɓallewa kamar an kunna famfo.

“Na rantse da Allah Samira idan baki karɓi maganinnan kin shanye ba zan danne ki a cikin ɗakinnan inyi miki ɗure, kin san zan iya abinda yafi haka ko?”

Umma ta sake faɗa da murya mai bayyana kaiwa ƙololuwa a cikin ɓacin rai.

Ta san halin Ummanta. Fiye da haka ma za ta iya, a tsaye take dirarriyar mace ga tsawo ga ƙiba, tsananin wahalar wankau da aikin awara baisa ta samu tasgaro a lafiyar jikinta ba. Lafiyayyiyar macece har gobe.

A lalace ta miƙa hannu ta karɓi ƙwaryar, wata zuciyar na ziga ta ta saki ƙwaryar a ƙasa ruwan maganin ya watse a tsakar ɗakin.

“Na rantse da Allah kika zubar da maganinnan sai na miki mugun dukan da tunda Allah ya halicce ki ba’a taɓa yi miki rabinsa ba.”

Umma ta sake faɗa cikin hargagi kamar ta san tunanin da Samira take yi.

Runtse idanu tayi, ta sadaƙar ta ɗaga ƙwaryar a fusace ta kai bakinta.

“Ki tabbata kinyi Basmala kafin ki sha.”
A karo na barkatai Umma ta sake faɗin haka.

Tsabar fushi da ɓacin rai a zuciya tayi Bismillar, tunda ta kafa ƙwaryar a bakinta bata cire ba sai da ta shanye ruwan rubutu da maganin tas! Sannan ta miƙa ma Umma ƙwaryar tana yamutsa fuska, ko kaɗan babu ɗaci maganin. Daga irin kallon da tayi ma maganin a farko ta zaci za ta ji ɗanɗano mare daɗi a ciki, sai taji akasin haka. Salaf yake, ba ɗaci ba hamami.

Hannu tasa ta goge laɓɓanta da take jin ɗan tsaki-tsakin garin da ke cikin maganin, ba tare da ta ce ma Umma komai ba ta ɗaga ƙafa za ta fice daga cikin ɗakin, tana sake gyara zaman siririn mayafin da ke rataye a kafaɗarta.

“Uwata ina za ki? Dawo!”
Umma ta sake faɗa har lokacin yanayin fuskarta bai koma dai-dai ba.

Bubbuga ƙafafu ta fara yi a ƙasa cikin shagwaɓa kamar wata ƙaramar yarinya.
“Ayya Umma Ayya… don Allah kiyi haƙuri, yau dai ɗaya ki barni in fita. Wallahi ba wani guri zan je ba sai gidansu Rahma. Kin san bikinta ya kusa, idan ba na ɓata lissafi ba yau saura kwanaki huɗu, kuma ni ce a matsayin babbar ƙawa. Duk wasu shirye-shirye da za’a yi akwai buƙatar in kasance gaba-gaba gurin gabatarwa, don ma dai banga wayata ba… Na san da tuni ta addabeni da kira…”

“Allah ya sanya alkhairi. Amma fa babu inda za ki je.”

“Babu inda zan je? To saboda me Umma?”
Ta tambaya hankalinta a bala’in tashe.

“Saboda kin fara Istibra’i. Daga yau, in Allah ya yarda ke da sake fita a gidannan in dai halin lafiya ne sai idan za’a kai ki ɗakin aurenki. Kina gama istibra’i da sati ɗaya za’a ɗaura aurenki da Inusa. Idan kuma kina ganin ban isa ba, ki saka ƙafa ki fita a gidannan, daga ranar da hakan ya faru kuma ki tabbata na cire ki daga jerin ƴaƴa biyar da na haifa a duniya. A taƙaice ina nufin ki nemi wata uwar ba ni ba.”

Kamar wata mutum-mutumi, haka Samira ta bi Umma da kallo baki da hanci buɗe har ta fice daga cikin ɗakin. Taka-maimai baza ta ce ga halin da take ciki ba ko kuma ga tunanin da take yi, abu ɗaya da ke ta amsa kuwwa a kunnuwanta shi ne saɗarar kalaman Umma na ƙarshe.

‘Ki nemi wata uwar ba ni ba.’

******

A wannan dare mai masifar tsawo a gurin Mannirah, sunan barcin da tayi shi ne raba da rabi. Wani irin barci mare daɗi mai cike da mugayen mafarkai, hankalinta a tashe tayi ta farkawa. A cikin daren, ta kira Muhsin fiye da sau hamsin amma ta kasa samunsa a waya, abinda ya ƙara ɗaukaka tashin hankalin da take ciki, saboda duk munanan mafarkan da take yi a kansa ne.

Da safe ta kasa hassala komai a ayyukan cikin gidan, kai tsaye ta ce ma Nauwara kanta na ciwo. Ta ɓalli paracetamol guda biyu tasha ta cigaba da kwanciya. Nauwara ce tayi hidimar abin karyawarsu sannan ta gyara gidan, a gurguje ta gama tayi shirin makaranta, har lokacin Mannirah tana kwance tana ta juye-juye, fuskarta damalmale da damuwa.

“Ko dai baza ki iya zuwa makarantar bane?”
Nauwara ta tambayeta cikin kulawa.

A kasale ta ɗaga kai ta kalli ƴar’uwartata. Idanunta sun canja kala saboda rashin barci da damuwa, daƙyar ta iya buɗe bakinta da yayi nauyi sosai ta ce
“Zan je.”

“Idan baki ji sauƙi ba, ki kwanta, gobe idan Allah ya kaimu sai ki je. Lafiya ita ce gaba da komai. Uncle Jamilu ya kira ni tun ɗazu idan mun shirya zai aje mu makaranta daga can zai wuce gurin Daddy, idan baki ji dama ba ki saka hijabi muje Chemis ya baki magunguna, sai ki dawo gida ni kuma in wuce makaranta…”

“Zan je.”
Ta sake faɗa a taƙaice.

Ko da ta shiga banɗaki gudu-gudu ta watsa ruwa, saboda lokacin ya tafi sosai. Ko karyawa bata tsaya yi ba ta shirya suka fice daga gidan.

Bata san Nauwara ta haɗa mata abin karyawa ba sai da suka je makarantarsu, tana sauka taga ta miƙa mata ɗan madaidaicin basket ɗin da damuwar da zuciyarta ke ciki ya hana ta ganin basket biyu ke riƙe a hannun Nauwara sadda suka fita daga gida.

Duk da damuwar da take ciki bai hana ta sakin ƙayataccen murmushi ba.
“Na gode Auntyna.”

Martanin murmushin ta mayar mata sannan ta amsa da
“Allah ya ƙara miki lafiya Sis.”

Ɗan duƙawa tayi ta sake yi ma Uncle Jamilu sallama, ta bashi saƙon ya gaida Daddy da jiki sannan ta matsa gefe tana kallon motarsu har suka ɓace a idanunta.

Kamar an ce ta waiga gefenta, karaf idanunta suka faɗa cikin na Muhsin lokacin da Fadila take sauka a cikin motar da ya saba kawo ta makaranta lokaci bayan lokaci. A haukace, ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, kafin ƙiftawa da bismillah kuma idanunta suka cicciko da hawaye. Musayar kallo suka yi da shi na tsawon wasu daƙiƙu kafin ya sakar mata wani lallausan murmushi.

Saboda raunin da zuciyarta yayi, ta kasa mayar mishi da martanin murmushinshi. A madadin murmushin ma hawayen idanunta ne suka samu damar silalawo zuwa kan kumatunta.

Ya ɗaga ƙafa zai ƙaraso gurinta kenan ɗaya daga cikin malaman makarantar ya fito, idanunsa kan Mannirah ya fara zazzaga mata faɗan me ta tsaya yi a waje a matsayinta na Head girl har lokacin tare latti yayi?

Da sauri ta mayar da hankalinta kan Malamin tana bashi haƙuri, da sassarfa ta ɗaga ƙafa za ta shige cikin makarantar sai ta sake kallon Muhsin a fakaice.

Da hannu yayi mata alamun zai dawo idan an tashi, a karo na biyu ta sake sauke ajiyar zuciya tana jin wani nutsuwa na saukar mata a jikinta har zuwa sadda ta shige cikin makarantar.

Sai dai ko da aka tashi, wani abu da ya ɗaga mata hankali shi ne ba shi ya koma ya ɗauki Fadila ba, direban gidansu ne. Raɓewa tayi can gefe jikin katangar makaranta inda babu yawaitar ɗalibai taci kuka ta gode Allah, kafin ta tari napep ta wuce gida. Jikinta a sanyaye, tana jin yadda kan ta ke bugawa gaf-gaf-gaf kamar ana buga mata guduma.

Duk da mawuyacin halin da take ciki na ciwon kai bata zauna ta huta ba, daƙyar tayi sallah zuciyarta rarrabe da tunanin dalilin da ya hana Muhsin dawowa ɗaukar Fadila kamar yadda ya alƙarwarta mata.

Tana idarwa bata nemi abinda za ta ci ba, waya ta ɗauko ta hau danna mishi kira ba ƙaƙƙautawa, wani abun mamaki da ƙarin ɗaga hankali a gare ta shi ne, kiran yana shiga, amma baya ɗaga wa.

Nauwara ta koma gidan da ƙurarren yammaci ne ta tarar da Mannira ba yadda take, zazzaɓi ya rufe ta ruf. Bata zauna ba haka ta sake ficewa zuwa Chemis ɗin Uncle Jamilu ta sanar da shi halin da ƴar’uwarta take ciki. Baiyi ƙasa a gwuiwa ba, ya tattaro kayan aikinsa yabi bayanta zuwa gidan.

“Ta ci abinci kuwa?”
Tambayar farko da ya fara yi ma Nauwara bayan ya ɓata lokaci akan Mannira yana mata gwaje-gwaje.

“Ban sani ba Uncle, dawowa na kenan na tarar da ita a wannan halin.”
Ta amsa jikinta a sanyaye.

“Haɗo mata Tea ta sha, allura zanyi mata.”

Cikin ƙanƙanin lokaci ya gama yi ma Mannira duk abinda ya kamata sannan ya fice daga gidan. Haka Nauwara ta ƙarasa daren jikinta a sanyaye, zuciyarta cike da damuwar halin da ƙanwarta ke ciki, ga damuwar Mummy da har yanzu wayarta bai shiga, kuma babu wanda ya san inda ta tafi, ga damuwar Daddy da har yanzu yake kwance a asibiti saboda karayar hannunsa da bai gama haɗewa ba.

Cikin hukuncin Allah zuwa can cikin dare bayan tayi barci sosai zazzaɓin ya sauka ma Mannirah, sai ɗan abinda baza’a rasa ba na daga ciwon kai, shi ma ba kamar da rana ba. Sallolin da ke kanta ta fara ramawa, ta yi wanka da ruwa mai zafi-zafi, sannan ta fice falo ta zuba abinci kaɗan ta ci. Duk abinda take yi sannu a hankali take komai don kar ta tashi Nauwara da take barci, har zuwa lokacin da ta gama komai ta haɗiye magungunanta ta sake kwanciya, zuciyarta cike da saƙe-saƙe da tunanin Muhsin, duk kiran da ta jera mishi da rana fiye da talatin ko misscall ɗin shi ɗaya bata gani ba, bai aika mata da saƙon kar ta kwana ba, ko da ta sake danna kiran lambarshi ba ta shiga.

Babbar damuwa da fargabarta ɗaya ne, Allah yasa ba ciwo ne yayi ma Muhsin tsananin da har ya kasa amsa kira ba. , Tunanin nata baiyi tsawo ba barci yayi awon gaba da ita, saboda cikin magungunan da Uncle ya bata akwai mai saka barci.

Washe-gari da ta kasance Laraba, ta tashi ne garas kamar ba ita ba. Da wannan dalilin yasa ko da ta ce za ta je makaranta Nauwarah bata hana ta ba. Da wurwuri suka shirya suka fice daga gidan zuwa asibiti gurin Daddy, basu daɗe ba suka kama hanyar zuwa makaranta.

A yau ko da ta isa makarantar, fakewa tayi da tare latti ta tsaya a bakin get tana kallon motocin da suke kawo ɗalibai, amma har aka buga shiga aji ba motar Muhsin balle Fadila da yake kawowa. Da yake ta je a ɗan makare ne, sai tayi tunanin ko Fadilar ta riga ta zuwa ne, duk da sanin lafiyar Muhsin shi ne abu na farko da take burin ji sai bata nemi Fadilar a cikin makaranta ba, a ganinta, cikin makaranta ba muhallin yin irin hirar nan bane. Ana kaɗa musu ƙararrawar tashi tayi wuf ta warci jakar makarantarta ta fice daga cikin ajinsu.

Sauri take yi kamar za ta tashi sama, har haɗawa take yi da gudu-gudu ta fita bakin gate a sukwane. Sai dai tuni ta ja tayi turus a bakin gate ɗin saboda rashin yin tozali da wanda idanunta suka so gani. Ranta yai baƙiƙiririn.

Ta ja tunga a kusa da motar gidansu Fadila da taga direba ya faka yana jiran fitowarta.
Babu jimawa sai ga Fadila ta fito cikin zugar ƙawayenta suna hira da ƙyalƙyala dariya. Mannirah tana tsaye tana kallonsu har suka yi sallama ko wacce ta kama gabanta.

“Fadila? Wai ni yau ina Yayanki ya shiga ne? Na ga ba shi ya kawoki ba, kuma jiya ya ce min shi zai dawo ɗaukarki amma bai samu zuwa ba.”
Ta jefa mata tambayoyin da sauri ba tare da jiran gaisuwa ya shiga tsakaninsu ba.

Daga farko Fadila baki ta sake tana kallonta kamar bata gane inda maganganun Mannirah suka dosa ba, domin share tantama sai ta ce
“Wane Yayan…?”
Sai kuma tayi saurin gyara kalamanta da cewa
“Wai Yaya Muhsin kike magana?”

A sanyaye Mannirah ta gyaɗa mata kai alamar eh! Sai kallonta take yi kamar ita ce Muhsin ɗin.

<< Lokaci 46Lokaci 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×