Minti ɗaya, biyu, uku, har zuwa goma ba Aunty Zubaida ba labarin fitowarta daga cikin ɗakin Khamis. Wasu azababbun mintuna masu bala'in tsawo da duk mazauna falon suke ganin kamar an ɗauki awanni masu yawan gaske. Hatta su Nauwara da basu gama fahimtar abinda yake faruwa ba duk sun ƙosa ta fito su ji abinda za ta ce, daga maganar da Sheik yayi, ba ƙaramin ruɗani zukatansu suka shiga ba. Duk da basu san me mahaifinsu yayi ba, a zuci suka fara addu'ar Allah ya taƙaita al'amarin.
Sau uku Alhaji Idris yana ɗaga ƙafa kamar. . .
Lallai komi lokaci ne kam
Mu je zuwa