Shiru yayi na wasu daƙiƙu kamar bazai amsa ba, sai da ya ɗan ja fasali kafin ya amsa da muryarshi a sanyaye irin ta marasa lafiya "Yanzu kuma zazzaɓi ne Babe, ciwon kan kaɗan ne."
Ya ɗanyi shiru kafin ta amsa ya cigaba da cewa.
"Amma kar ki damu, zazzaɓin bai yi wani ƙarfi sosai ba, kawai dai ina ɗan jin sanyi ne. Amma na san tunda na sha magani zai sauka yanzu, in... sha... Allah...!"Ya ƙarasa maganar a rarrabe, muryarsa na rawa.
Hankalinta ne ya ƙara ɗugunzuma, amma duba da yadda yake ƙo. . .