Da maɗaukakin ɓacin rai a fuskarsa yake kallon Yaya, sai sakin zafafan numfarfashi yake yi kamar mai shirin haɗiyar zuciya. Yadda kasan zai fashe da kuka haka ƙirjinshi ke hawa da sauka, muryarshi na rawa saboda ɓacin rai ya ce,
"Yanzu Yaya saboda Allah me kake nufi da maganganunka? Kai da kanka kake min zancen in nemo wata matar in aura bayan ka san abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba? Na zaci kai da Jamilu kuka tsara zantuttukan da sukai tasiri a zuciyata na sallami Ziyada? So kake inyi ta zama cikin ƙunci da kaɗaici. . .
Oh oh Khamisu wannan jaraban ina zaka da shi?? Allah ya shirya
Samira kuwa na ji dadin yadda komi na tafiya dai dai