Har gida aka kai ma Umma labarinta. Abu ɗaya da yaso sanyayar mata da jiki shi ne jin aikin Hajja Falmata da tsada, domin sati ɗaya kacal a sauƙaƙe tana karɓan naira dubu arba'in ne. Amma jin irin kyawun ayyukan da take yi, da turbar shawarwarin zaman aure da iya gogayya ako wace kalar rayuwa ta zaman duniya yasa zuciyar Umma kwaɗaituwa da aikin.
Ba tare da sanin Samira ba ta saida duk ɗan tanadinta na auren ta biya kuɗin aikin gyaran jiki a gurin Hajja Falmata na sati huɗu, a sauƙa. . .
Allah sarki Rahma mai kyakkyawan hali
Allah ya hada mu da mutanen arziqi da zuciya mai kyau
Allah ya sa muma mu kasan ce masu Hali da zuciya mai kyau