Skip to content
Part 58 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Kamar baza ta amince da kiran nashi ba, don Allah ya sani duk wani roƙo ko takurawa ba ta so ta ɓullo da shi a zamantakewar aurenta. Amma da ta tuna ƙoƙari da ƙaunar Rahma a gare ta, sai ta sake danna mishi kira. Ba tare da jin kunyar idanun Rahman ba ta ƙanƙance murya cikin salo da ladabi da biyayya ta faɗa mishi alfarmar da take nema. Sannan ta ƙara da faɗa mishi dalilin buɗewar, bata ɓoye mishi duk abinda Rahma tace mata ba.

Kai tsaye ba tare da ja’inja ko zargi ba yace ya bata izinin ta buɗe.

“Kar ki damu Matata. Ɗari bisa ɗari na amince da ke. Kanki tsaye ki aikata duk abinda kika san bai saɓa ma Addininmu ba.”
Amsar da ya bata kenan da yasa ta ƙanƙame filo ita kaɗai take ta sakin murmushi.

Har Rahma ta ɗauki wayarta da babu key ta buɗe data ta fara ƙoƙarin yi mata Register da Whatsapp bata san me take ciki ba. Zuciyarta cike da matsanancin ƙaunar mijinta.

Babban akwati Rahma ta shaƙo ma Samira da ɗinkunan atamfofi, shadda, laces, mayafai, inner wears, na cin biki. Saboda tsananin mamakin yawan kayan Samira kasa cewa komai tayi, sai duƙar da kanta ƙasa tayi tana hawaye. Zuciyarta cike da godiya ga Allah.

‘Ashe haka ne idan bawa ya dogara ga Allah ya isar masa ako wane lokaci?’

Ta tambayi kanta a zuciyarta. Bayyanar Rahma a daidai wannan gaɓar da ake tsaka da ƙaƙa-kayin sayar da filin Umma don ayi mata kayan ɗaki abu ne da bata taɓa tsammani ba. Sai ga shi cikin hukuncin Allah ya aiko musu Rahma da Mijinta, suka yi mata kayan ɗaki na gani a faɗa da duk wacce taje ta gani ta dawo yini take sambatun kyawun ɗakinta.

A ɓangaren kayan cin biki kuwa, a cikin tulin kayanta da bata saka su sosai bane ta tsinci kala goma ta wanke ta goge su ƙal, a nufinta da su za tayi fitar biki. Domin ko kusa bata saka ran kayan akwati na kece raini ba, ita da kanta ta ce ma Is’haƙ kar ya kuskura ya takura kanshi. Yayi mata duk abinda ya samu kawai, domin yayi mata alfarmar da ko babu lefe da sauran kayayyakin da ba addini ba za ta aure shi.

Sai ga shi da yake Allah Al’musawwiru ne, ba tare da sunyi maganar rashin sabbin kayan fitar biki ba, ba tare da Rahma ta tambayeta ba, kawai ta yi mata suprise na waɗannan zankaɗa-zankaɗan siturun masu tsada kaloli daban-daban har kala goma sha biyar. Bayan godiya ga Allah ita kuwa me za ta ce da Rahma?’

Ta ɗago kanta fuska jage-jage da hawaye za tayi magana da sauri Rahma ta toshe mata baki.

“Don Allah kar ki ce komai. Ba na buƙatar ki ce komai. Duk abinda kika gani na yi miki saboda Allah ne da kuma ƙaunar da take tsakaninmu.”

Duk yadda taso yin godiya sam Rahma ta hana ta magana. Sai su Umma da ƴan’uwanta na kusa ne suke ta ɗaɗɗaga kayan suna saka mata albarka da addu’ar Allah ya sauketa lafiya. Tun tana amsawa da Amin a ƙarshe ficewa daga ɗakin tayi, a ganinta duk abubuwan da tayi basu cancanci irin waɗannan kururutawar ba.

Samira ta wuce komai a gurinta, bayan ƙaunar da take mata Samirar ita ce kamar tsanin da ta zame mata matakalar takawa har zuwa inda take a yanzu. Idan bata gatanta Samira ba ai ko Allah sai ya tambaye ta.

Ganin duk abinda ake buƙata ya samu a sauƙaƙe, ya saka Umma yin shawara da ƴan’uwanta suka tattara gudummuwar da ta samu aka yi ma Samira garan abinci na gani a faɗa. Sannan dangin su snacks da ake yiwa amarya da wanda ake raba ma dangin miji haka aka yi komai a wadace, kamar ba ɗiyar talakawa ba.

******

Washe garin juma’a aka yi ƙayataccen walima ta mata, ya samu halartar nagartattun malamai mata na islamiyyun cikin unguwar, sun yi nasiha akan aure, da hakkin miji akan matarsa. Kuma cikin hikima suka nusar da mata hanyoyi da irin matakan da za su bi a addinance wurin zamowa Sarauniya a zukatan mazajensu. Walima ya ƙayatar ya ilmantar, an ci an sha, da aka tashi kuma Rahma da taimakon Inna Fatu suka bi kafatanin jama’ar da suka halarci walimar da kyautar babban bokitin wanka da kofi, a jikinsu an manna ƙayataccen stikker mai ɗauke da sunan amarya da angonta.

Ranar asabar da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe aka ɗaura auren Samira da Is’haƙ. Ɗaura auren da ya samu halartar mutane da dama daga ko wane ɓangare.

Duk da Umma ba wani gayyar mutane sosai tayi ba, gidanta ya cika danƙam da mata, har da gayyan soɗi da ƴan sa’ido. Kasancewar biki ne da aka samu amincewar iyaye da mafiyawa daga cikin dangin ko wane ɓangare shi yasa suka toshi kunnuwansu daga ƙananun maganganu, musamman ɓangaren Ango.

Anyi taro lafiya an gama lafiya. Duk yawan ƙawayen da Samira take da su a baya bata gayyaci ko ɗaya ba, su ɗin ma ko basu samu labari bane? Babu wacce ta halarci bikin. Da wannan dalilin yasa Ango da Abokansa basu wani sha wahala wajen hidimar ƙawayen Amarya ba. Rahma ce kaɗai, ita kuma matar aure ce da mijinta ke ta kaffa-kaffa da ita ba tare da kunyar idanun jama’a ba.

Ƙarfe shidda daidai iyayen Amarya da dangi suka gama duk nasihar da za suyi aka ɗauki Amarya zuwa gidan mijinta. Duk da gidajen babu nisa sosai, haka Abokan Ango suka yo hayan wadatattun motoci aka dinga ɗiban mutane zuwa gidan Amarya.

Zuwa ƙarfe takwas na dare kowa ya watse sai Rahma da Inna Fatu, ita ma Innar sauri-sauri ta ƙarasa goge-gogen da take yi ta wuce gidan Umma, daman ba komai ya tsayar da ita ba sai taya Rahma ƙara gyara ɓangaren Amarya da yawan jama’a masu shige da fice yasa suka ɗan zubda datti a wasu gurare.

Izuwa yanzu sun gyara ko ina ƙal-ƙal. Ta ko wane ɓangare na sasan Amarya daddaɗan ƙamshin turaren wuta yake fitarwa. Duk da babu wutan nepa ko ina hasken Invater ya haske tar kamar rana.

Ƙarfe tara da rabi Salim ya je ɗaukar Rahma, duk yadda Samira taso ta jira zuwan Ango ƙiyawa tayi.

“Bar ni in tafi kin ji, in dai ba so kike in ƙure haƙurin bawan Allah ba. Tun da muka shigo ƙasar nan ban bashi wani lokaci na ba. Kwanaki biyunnan kam ɓata su zanyi gurin tarairayarshi, duk yadda ake ciki dai za muyi waya.”

Haka suka rabu da juna fuskokinsu cike da farin ciki da ƙaunar juna. Har ta fita can sai ga ta ta dawo a gaggauce, babban envelope ne a hannunta da aka yi sealing ɗin bakinshi.
“My dear ne ya dawo da ni. Wai wannan saƙon ki ba Ango, ki faɗa mishi za suyi waya bayan an kwana biyu. Yana mishi fatan alkhairi da addu’ar Allah ya bada zaman lafiya.”

Bata jira cewar Samira ba ta aje mata envelope ɗin a cinyarta ta fice da sauri.

Shi ma Ango kamar ya san babu kowa sai Amaryarsa, shi kaɗai ya kai kansa ɗaki ba tare da rakiyar abokai ba. Hannunsa riƙe da ledar kaza da drinks na al’ada kamar yadda ko wane ango yake shiga ɗakin Amarya.

A wannan dare, ko basu faɗa ba duk su biyun zukatansu cike yake da farin ciki. Da gaskiyar bahaushe da yace labarin zuciya a tambayi fuska. A fili suke karanta labarin zukatan junansu.

Ba tare da wani kunya ko ƙauyanci ba Ango ya ciyar da Amaryarsa kaza da lemun exotic, ita kuma ta dinga karɓa a kunyace, yangace, ƙasaice, ɗan kaɗan taci ta ce ta ƙoshi. Bai matsa mata ba, shi ma ya ɗan tattaɓa sannan ta tattara komai ta kai kicin rakiyar idanunsa, a zuciyarsa ji yake kamar ya kamo ta ya haɗiye don tsananin so da ƙauna.

Ko da ta dawo bata zauna ba, ɗaki ta shige ta ɗauko mishi saƙon Salim mijin Rahma, sai da ta durƙusa har ƙasa sannan ta miƙa mishi, ta kuma faɗa mishi daga inda saƙon ya fito.

“Toh fa! Me muka samu Matata?”
Kafin ta amsa yasa hannu ya riƙo nata ya zaunar da ita a gefensa, sannan ya warware envelope ɗin sannu a hankali.

Daga shi har ita baki buɗe suke kallon bandir ɗin ƴan dubu-dubun har guda biyar, sai wata ƴar ƙaramar takarda da aka yi rubutu kamar haka,

“Ango ga ƴar ƙaramar gudumuwa daga gare ni, Allah ya bada zaman lafiya. Samira yarinyar kirki ce, ako wane lokaci haka matata take yawan faɗa min. Don Allah ka kula da ita sosai, kuma sai ka yi haƙuri a matsayinka na jagora, domin Mata sai da haƙuri. Allah ya baku zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba. Salim Kanta.”

Sannu a hankali ya sauke nannauyar ajiyar zuciya bayan gama karanta takardar. A slow motion ya miƙar da ita tsaye, idanunsa a cikin nata ya fara warware naɗin lafayar da ke jikinta har ya warware gaba ɗaya.

Ya janyo ta a hankali ya rungume a ƙirjinsa, wani abu da bai taɓa tsammanin zai faru a gaske ba sai ga shi cikin hukuncin Allah ya faru. A lokacin da bai taɓa tsammani ba.

A tare ita da shi suka sauke nannauyar ajiyar zuciya. Tana jin yadda yake ƙara ruƙunƙumeta kamar zai tsaga ƙirjinsa ya saka ta a ciki, ita kuwa ta lumshe idanunta tana jin yadda wani daɗi mai cike da nutsuwa yana ratsa ilahirin sassan jikinta.

“Alhamdulillah!”
Suka haɗa baki gurin faɗin haka a fili.

_Asubah ta gari Samirar Is’haƙ._

******

A waɗannan ranakun su Nauwara suka shiga students week a makarantarsu. Duk da cewa ba a lectures, kuma ba kowa yake zuwa makarantar ba, amma ita ta gwammace ta tafi makarantar ta yini a hostel ko wajen da ɗalibai ke shagulgulan murna, akan dai ta zauna a gida wajen su Aunty Zainab.

Ta shirya tsaf cikin shiga ta kamala kamar yadda ta saba, ta yiwa mutan gidan sallama. Uncle Yusuf ya ɗauki dubu ɗaya ya bata kamar yadda ya saba, ta fita direba ya tuƙa ta zuwa makaranta.

Kai tsaye hostel ɗin mata ta wuce, ta samu gadon wata ƙawarta ta haye ta hau danne-dannen waya. A ganinta, hakan ya fiye mata akan dai ta zauna a gida ana sanyata aiki da yawan maganganu.

Kiran Amina da ya shigo wayarta ne ya katse mata game ɗin da take yi. Da kamar ba za ta ɗaga ba, daga ƙarshe dai ta ɗauka, ko ba komai sun kwana biyu basu yi magana da Aminar ba.

“Kina ina ne Babe?”

Tambayar da Amina ta fara yi mata ba tare da amsa sallamarta ba.

“Ina ina kuwa da ya wuce makaranta? Kin dai san halin da nake ciki na takura yanzu idan ba na gida to tabbas ina makarantar boko ko islamiya.”

Ta amsa muryarta na bayyana ƙuncin da zuciyarta ke ciki.

“Good! To wallahi ki san yadda za kiyi ki taho yanzunnan. Mommy ta ce ni da ke muna da manyan baƙi da suka zo daga Kano. Idan kuwa har baki zo yau kin tarbi baƙinnan da ta daɗe tana cin burin zuwansu ba, to duk wani uziri da take miki ya ƙare.

Kin daɗe kina karya dokar ƙungiya tana kawar da kai. Kuma dai kin san idan tayi fushi abinda zai biyo baya bazai miki kyau ba. Don haka ni dai ba ruwana, ki zo kawai.”

Tayi narai-narai da ido kamar Aminar na gabanta ta ce,

“Amina kin sani fa sarai irin halin takurar da nake ciki. Wallahi idan Abba ya ji labari sai ya kusa kashe ni. Ke na tabbata na lahira sai ya fi ni jin daɗi…”

“Ke dai har yanzu baki waye ba Nauwara.”

Aminar ta katse ta da sauri.

“Abinda ke bani haushi da ke kin cika masifar tsoro kamar farar kura. Shi Abban naki Allan-musuru ne da shi da zai san kina makaranta ko ba kya nan? Abu ne fa na dan ƙanƙanin lokaci. Na faɗa ma Mummy ƙarfe huɗu da rabi dai dai za mu bar baƙin ki wuce makaranta ni kuma in wuce gida. Kuma ki tuna irin maƙudan kuɗaɗen da muke caska idan aka haɗa mu da irin waɗannan baƙin.

Baya ga haka ma na san fa kema kina buƙatar abinnan yadda aka kwana biyu ba a haɗu ba! Dallah kiyi sauri ki fito kawai Hajiyata, ba abinda zai faru sai alkhairi.”

Haka tayi ta mata daɗin baki har dai ta amince zata je.

Tana ɗaura niƙaf ɗin da ta ara nan gurin ƙawarta a wani sashe na zuciyarta take ji kamar kar ta tafi, amma inaaa… Shaiɗaniyar zuciyarta ta riga ta yi nasara a kanta, haka tasa ƙafa ta fice ba tare da tunanin abinda zai je ya zo ba.

Shatar keke napep ta ɗauka har gidan Mummy. Ko da ta isa bata ɓata lokaci ba a gaggauce Mummyn ta ɗuɗɗura mata magungunan mata emargency ta ƙara shiryata ciki da waje sannan tasa direbanta ya ɗauki Nauwara har zuwa hotel ɗin da baƙin suka yi masauki. Domin already sun riga sun wuce da Amina.

Shahararren hotel ne wanda sai wane da wane kaɗai suke iya cin abinci ma a wajen balle a kai ga zancen kama ɗakin kwana. Tun daga nan taji hankalinta ya ɗan nutsa, idan ta hango irin nairorin da zata caska sai ta ji nutsuwarta ya ƙara ninkuwa. A zuciyarta take ta ayyana yadda Mummy take ta ƙara jaddada mata kar ta kuskura ta je ma baƙinnan da kunya ko ƙauyanci, domin wayayyun mutane ne da suka saba gogayya da matan turawa.

Suna waya da Amina har ta isa ƙofar ɗakin da ta faɗa mata tayi knocking, sai ga Amina ta buɗe mata kofar, ta rungumeta cikin murnar ganinta.

Wasu irin yagalgalun ƴan iskan kaya ne a jikinta Aminar, wando bum shot da wata half vest da babu abinda ta rufe na daga halittun kirjinta.

Nan ta ja Nawwara cikin ɗakin inda ta samu baƙin suna jiransu. Kai daga ganinsu kaga babbar harka, wayayyun mutane da kallo ɗaya ta gane kuɗi da hutu ya ratsa jikinsu kamar yadda Mummy take ta faɗa.

Nan da nan kuwa ta shige ban ɗaki da jakar hannunta ta canja kayan jikinta zuwa tsinannun kayan da suka fi na jikin Amina bayyana tsiraici. Ko da ta fito kamar mayu haka matasan samarin biyu suka bi ta da kallo kamar za su cinye ta ɗanye.

Nan take ɗaya daga cikinsu da tun ɗazu ita yake jira ya janyota jikinsa ya fara lalubeta, daga bisani suka yi ɗaiɗaya suna cin abubuwan da aka kai musu, don ita Amina ma har giya ta fara sha ita da wanda yake a matsayin saurayinta, dama hakan ba baƙonta bane.

Cikin hukuncin Allah da tsarewarsa dai duk yadda ta so ta koya ma Nawwara shan giyar ta ƙi koya sam! Ko ɗanɗane bata taɓa yi ba.

Kafin kace me, abubuwa sun fara ɗaukar zafi, don haka Amina taja abokinta zuwa ɗakin gaba inda ya kama, ta bar Nawwara tare da wanda za ta kula da shi, Matashi mai suna D. Boy.

Gogaggen matashi ɗan duniya tuni ya fara hillatar Nauwara, a ƙanƙanin lokaci ta fara mantawa da kowa da komai ta biye mishi ta hanyar fara mayar mishi da martani tana nuna mishi ita ma fa ba kanwar lasa bane.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 57Lokaci 59 >>

1 thought on “Lokaci 58”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×