Skip to content
Part 59 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Da ganin yadda D.Boy yake tafiyar da ita tsohon ɗan hannu ne a bariki, wanda ya ƙware sosai a harkar ya kuma san duk wata mataɓa da zai motsa mace duk miskilanci da ƙasaitarta. Hakan da yake yi shi ya ƙara gigita nutsuwar Nauwara.

Lokaci mai tsayo suna cikin wannan ƙazantaccen yanayin kwatsam! Aka tura ƙofar ɗakin aka shiga. Kamar wacce aka finciko hankalinta daga wata ƙololuwar duniya zuwa wacce muke ciki, firgigit ta dawo hayyacinta, hankalinta ne yayi wani mummunan tashi ganin ashe bayan fitar su Amina ba a rufe ƙofar ba.

Zazzaro idanun da tayi ta fara make hannun D. Boy daga jikinta da ƙarfi shi ne abinda ya dawo da shi cikin hayyacinsa har idanunsa suka sauka kan abinda take kallo a tsorace kuma baki buɗe. Wani magidancin mutum ne tsaye a tsakiyar ɗakin yana daddana waya, kamar bai san da su a cikin ɗakin ba.

“Kwantar da hankalinki Beb, Oga na ne wannan. Tare muke da shi, ya taho da wani abokinmu ne. Idan za ki iya ɗaukarmu mu biyu ko ukun ma har gasa za mu saka miki na maƙudan kuɗaɗe matuƙar kika iya gamsar da mu biyu ko uku a lokaci ɗaya. “

Tana shirin buɗe baki ta ce mishi ita dai bata taɓa irin wannan tsarin ba kawai sai gani tayi an sake buɗe ƙofa, ko kafin tayi wani yunƙuri na yakice D.Boy daga jikinta ko ta suturta jikinta har ɗayan abokin nasu ya shigo cikin ɗakin fuskarsa cike fal da murmushi.

Idanunsu na faɗawa cikin na juna ita da wannan abokin su D.Boy ɗin da ya shigo bayan wannan dattijon da D.Boy ya ce Oganshi ne kamar haɗin baki a tare suka saki mahaukacin ihu.

Da wani irin bala’in hanzari da ƙarfin da bata taɓa tsammanin tana da shi ba ta ture D.Boy daga jikinta, a tsorace tayi wata irin alkafira ta faɗa can bayan gadon da suke kwance akai suna shaiɗancinsu.

Hakan bai ishe ta ba, a haukace ta sake fincikar bargon da yake kan gadon tana rufe jikinta hankalinta a bala’in tashe. Lokaci ɗaya zufa ya wanke ta kamar wacce aka sheƙawa ruwan sanyi, sai kuma ta fara rawar ɗari tana ƙif-ƙifta idanu kamar za ta tashi aljanu.

A slow motion ya tafi luuu ya faɗa jikin Ogansu da ke tsaye a gabanshi yana rarraba idanu tsakanin karuwar D.Boy da Khamis da suka haɗa baki gurin ƙwalla ihu. A gaggauce ya riƙe shi da kyau don kar su faɗi ƙasa su biyun, ya fara girgiza shi da damuwa a fuskarsa haɗe da kiran sunanshi yana tambayarshi lafiya kuwa?

“Me yake faruwa? Ka santa ne? Kar dai ace Beb ɗin ka ce da ka gama aminta da ita Big Aunty ta haɗa Duwan da ita ba tare da mun sani ba?”

Khamis dai inaaaa… Ba baka sai kunne saboda tsananin tashin hankali da mummunan firgicin da zuciyarshi ta shiga. Har lokacin kuma ya kasa kawar da idanunshi daga kan Nauwara wasu zafafan hawaye suna sauka mishi a guje kamar an buɗe famfo.

Suna cikin wannan hali na kiɗima da rashin sanin abin yi kuma sai aka ƙara turo kofar ɗakin aka shiga ba tare da neman izini ba. A lokaci ɗaya, su duka huɗun suka maida kallonsu ga ƙofar don ganin waye kuma ya shigo?

Idanun Nauwara cikin Baffa Yusuf yasa ta ɗora hannu biyu ta fashe da wani ƙaƙƙarfan kuka a haukace. A zuciyarta take ayyana shi kenan! Yau dai kam kashinta ya bushe… Ita da cigaba da rayuwar duniya kuma sai dai wani ikon Allah. Ta sani Daddy da Abba Yusuf baza su taɓa barinta da rai ba saboda duka da matsanancin azabar da za su gana mata.

Shi kuwa Abba Yusuf da babbar manufarshi na tahowa ɗakin hotel ɗin don ya kama Khamis dumu-dumu ne saboda ya kafa hujja a kanshi, mummunan ganin da yayi na ba zato ba tsammani yasa zuciyarshi ta nemi tsayawa da bugawa.

Cak! aka tsaya ana kallon-kallo tsakanin su ukun kamar umarnin darakta, babu mai bakin magana a cikinsu balle ƙarfin ɗaga ƙafafu. Tsakanin Duwan da yake zaune tsuru haihuwar gyatumarsa da Ogansu kuwa sai raba idanu suke yi tsakanin Khamis da yake jingine jikin Oga yana shatatar hawaye, da karuwar Duwan da take ta rusa kuka kamar ana zare mata rai, da Abba Yusuf da ba su da masaniyar ko wanene shi.

Kamar an ƙwato kalaman daga bakin Abba Yusuf ya furta su da ƙarfin gaske.
“Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un! Allahumma ajirnee fi musibati, wa akhlifnee khairan minha!!!”

Kalaman sallamawar da miƙa neman sassauci daga musiba da tabbatuwar alkhairin cikin musibar sun fito ne da wata irin kiɗima a muryarsa, zuciyarshi na tsalle tana dukan ƙirjinshi kamar za ta fasa ƙirjin na shi ta fito.

Sai kuma cikin sauri kamar wanda aka yi ma umarni ya rufe idanunshi yana girgiza kai, kamar dai hakan shi zai goge mummunan hoton da kwakwalwarshi ta riga ta ɗauka tayi musu muhimmin adani a lungun da bazai taɓa goguwa ba.

Khamis kuwa kalaman Yaya Yusuf su suka taka rawa gurin dawo da shi hayyacinshi, yayi ƙarfin halin miƙewa daga jikin Oga da wani irin ƙarfin zuciya a haukace. Yai gaba yayi baya sai kuma ya tsaya a tsakiyar ɗakin cikin rashin sanin abinyi, ya rasa inda zai tsoma rayuwarshi ya ji dama-dama. Kawai sai ya ɗora hannuwa biyu akai kamar wani ƙaramin yaro ya fasa wani irin ihu da ƙaraji yana kururuwa.

A zuciye Yaya Yusuf ya janyo Khamis ya gaura mishi wani gigitaccen mari. Cikin tsawa da ɗaga murya ya ce,

“Kai! Fita waje ka bamu waje mutumin banza da wofi.!”

Da ace Khamis a cikin hankalinsa yake, wannan ƙaƙƙarfan marin da aka sakar mishi babu abinda zai hana shi zubewa ƙasa. Amma saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki ya hana shi ya ji zafin marin, kawai jikinsa ne ke wani irin rawa da zabura kamar tsohon ɗan dambe.

A haukace ya fara magana yana zazzare idanu, sai nuna Yaya Yusuf yake yi da yatsarshi manuniya kamar wani sa’anshi.
“Kamar ya in fita in baku waje? Halan ka makance ne baka ga abinda yake faruwa ba?

Ƴata ce fa? Babbar ƴata Nauwara mai sunan Ummina. Yarinya mafi soyuwa a cikin zuciyata… Ba ka gani ne yadda wannan tsinanne la’anannen ya haiƙewa ‘yata ta cikina? Ko don ba ƴarka ba ce? Na rantse da Allah Wallahi babu inda zan je sai na raba shi da abin tunƙahon na shi. Sai in ga da me zai bi ƴaƴan wasu nan gaba.”

A haukace ya yunƙura da dukkan ƙarfinsa da nufin yin tsalle ya damƙo Duwan maganar da Yaya Yusuf yayi ta saka shi tsayawa cak! Kamar an danna mishi pause da remot control.

“Ka nutsu Khamis ka duba da kyau ka gani, ita yarinyar taka cicciɓota yayi ta ƙarfin tsiya ya kawo ta nan ko kuwa zuwa tayi da ƙafafunta? Ko a sadda ka shigo ka ga alamun tirsasawa a tare da ita?”

Jikinsa a sanyaye sosai ya sauke idanunsa akan Nauwara da har lokacin bata daina kuka ba, sai ƙara rakuɓewa take yi can lungun gadon da ta shige kamar ƙasa ya tsage ta shige don matsananciyar kunya da fargabar da take ciki.

“Ya zaki yi mun haka Nauwara?”

Ya yafito tambayar da ƙyar ya jefa mata.

“Me yasa zaki yi mun haka? Me na miki da zaki yi mun wannan sakayyar?? Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un!! Allah na tuba, wayyo Allah na…!”

Ya ƙarasa cikin kuka mai ƙarfi tare da ƙoƙarin sulalewa zuwa ƙasa.

Da saurin gaske Yaya Yusuf ya tare Khamis ya hana shi kaiwa ƙasa. Yana tangaɗi ya buɗe ƙofar ɗakin ya tura shi zuwa waje sannan ya mayar da ƙofar ya rufe ba tare da damuwa da halin da ya bar Khamis a ciki ba.

Ya juya yana ƙarewa ɗakin da mutanen cikinsa kallo, ko da wasa ya kasa yi ma Nauwara kallo na biyu balle ya iya mata magana. A karo na barkatai ya sake kallon abokin shashancin na ta da har lokacin bai samu sararin suturta jikinsa ba, kamar ma ya manta a yanayin da yake ciki.

Da shaƙaƙƙiyar murya ya ce,

“Babu abinda zan iya ce maka a yanzu, sannan babu wani mataki da zan iya ɗauka a kanka, saboda da amincewarta ka aikata komai. Amma kaje kawai… Duniya ce, ta ishi kowa riga da wando.

Shi ma Khamis da kake gani, irinka ne, ga kuma abinda Allah ya saukar mishi akan ƴarshi ta cikinshi a lokacin da bai taɓa tsammani ba. Idan hakan zai zame muku izina to, idan kuwa bai zama ba, ka je, za ka gani nan gaba.”

A fakaice ya mayar da idanunsa ɓangaren Nauwara ya ce.

“Ke kuma, ki saka kayanki ki zo waje ina jiranki!”

Yana gama faɗin haka ya fita daga ɗakin zuciyarshi tana wani irin tuƙuƙi ranshi na suya.

Khamis na durƙushe a bakin kofa ya haɗa kai da gwuiwa yana sharɓan kuka, yana jin an buɗe ƙofar yayi wani irin kukan kura ya danna kai cikin ɗakin. Duk yadda Yaya Yusuf yai ƙoƙarin riƙo shi inaa, tuni ya ƙwace ya faɗa cikin ɗakin, daman tun fitar Yaya Yusuf da suka ji wacece Nauwara a gurin Khamis hankalinsu yayi masifar tashi.

A firgice Duwan ya miƙe jikinsa na rawa ya fara saka rigarshi yana salati da sallallami a fili. Shi kuwa Oga idanunsa akan Nauwara sai maimaita mata tambayar.

“Ke? Da gaske Kham mahaifinki ne? Wai da gaske Babanki ne?”

Domin ko da Khamis ya gama yiwa Yaya Yusuf masifa yana faɗin an keta alfarmar ƴarshi sam basu yarda da maganganunshi ba. Sai da Yaya Yusuf yayi magana sannan suka yarda, duk jikinsu ya mutu.

Ita kuwa Nauwara ba baka sai kunne, ta kasa amsa tambaya ɗaya daga cikin wanda Oga ke mata. Kuma har lokacin bata miƙe ta fara mayar da kayanta da suke ajiye a cikin bayi da bayan isowarta ta shiga ta canja kaya ba.

Khamis na shiga ɗakin kan Duwan yayi gadan-gadan yana ƙoƙarin damƙo gabanshi, ba don Allah ya sa Yaya Yusuf da Oga sun yi azamar riƙo shi ba, da tuni yayi mishi mummunar illah.

A fusace Yaya Yusuf ya finciko shi ya dinga auna mishi mari a fuska sai da Oga ya ƙwace shi, zuciyarsa cike da tausayin Khamis ɗin. Magana ma ya kasa yi, sai yatsa yake nuna mishi alamun ya shiga taitayinshi.

Da sauri Yaya Yusuf ya fita zuwa bakin ƙofa wajen ma’aikatan hotel ɗin da suka leƙo saboda jin hayaniya. Haƙuri ya basu, sannan ya tabbatar musu ba wata babbar matsala ba ce, kawai mayar da magana suke yi abun ya nemi zama faɗa.

Kashaidi mai ƙarfi suka yi mishi akan lallai su kiyaye wannan hayaniyar sannan suka tafi.

Ko da ya koma cikin ɗakin, wani gigitaccen tsawa ya daka ma Nauwara babu shiri ta miƙe tsaye jikinta na rawa, sai gyara riƙon bargon da ya asirta jikinta take yi, har lokacin bata daina kuka ba. A tsawace ya sake umartarta kan ta wuce ta saka kayanta kafin ya rufe ta duka.

Daƙyar ta iya ɗaga ƙafafunta ta tsallaka kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ta nufi banɗaki, cikin ƙasa da mintuna ashirin ta yi wani zuru-zuru kamar wacce ta kwanta jinya na watanni. A yadda take ji kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki. Tunda take a rayuwarta ta duniya, bata taɓa jin kunya makamanciyar wadda take ji a yanzu ba. Kamar za ta kifa ta shige banɗaki.

Daga Yaya Yusuf har Khamis kallonta suke yi yadda cikin ƙasa da mintuna uku ta fito a nutsattsiyar yarinyarta sak, har da niƙaf ta ɗaura ma fuskarta. Ita kuwa ta kasa kallon ɗaya daga cikin iyayen nata ta fice daga ɗakin, haka nan Khamis ya bi bayanta yana tangaɗi kamar ɗan tsakon da ruwa ya ba kashi, Yaya Yusuf ya bi bayansu jikinsa a sanyaye.

Daman Khamis bai je gurin da motarsa ba, yana can gida yana barci ya saka wayarsa a silent, ko da ya farka, ya shiga bayi yayi wanka yana fitowa idanunsa kan wayarsa kiran Oga ya shigo mishi. Bayan faɗa da yayi mishi na yadda yayi ta kiransa bai ɗauka ba sannan ya sanar da shi sun shigo Kaduna tare da su Duwan.

“Tun safe sun neme ka a waya basu same ka ba. Sun so ka sama musu ƴan shila sabbin ƙyanƙyasa rashin samunka a waya yasa suka tuntuɓi Big Aunty, ita tayi musu duk abinda ya kamata. A yanzu haka dai suna can suna hutawa, nima na fito ganawa da Sanata Kasim Habib ne, duk inda kake ka fito yanzu ka same ni a Sultan Road akwai muhimman maganganun da nake so mu tattauna da kai.”

Wannan shi ne dalilin da yasa bai fito da mota ba, ya tari acaɓa har Sultan Road suka haɗu da Oga sannan suka ɗunguma zuwa hotel domin gaisawa da su Duwan. Ashe rabon zaiyi kyakkyawan gani ne.

Gaba ɗaya su ukun suka ɗunguma zuwa motar Yaya Yusuf, jiki a sanyaye yaja motar har suka isa gida babu mai ƙwaƙƙwaran motsi a cikinsu.

Wani taimako da Allah yayi musu shi ne gidan babu kowa, Aunty Zee ta kwashi iyalanta gaba ɗaya sun shiga kasuwa siyo kayayyakin buƙatu. Don haka suka zube a nan falon kowa da irin tashin hankalin da yake danƙare a zuciyarshi.

Nawwara na gurfane a gabansu gwuiwa a ƙasa kamar mai neman gafara. In banda sautin shessheƙar kukan Khamis da Nauwara baka jin komai a cikin falon.

Yaya Yusuf ya kalli Khamis ya galla mishi harara, ƙwayoyin idanunsa sun kaɗa sunyi jajur.

“Na rantse idan baka min shiru ba zan miƙe in naɗa maka matsiyacin duka Khamis.”

Amma a maimakon yayi shiru kamar yadda aka umarce shi sai wani kukan mai sauti ya ƙara ɓallewa da shi, ga murya na garjejen namiji sai yake fita kamar an kunna generator. A hakan kuma ya fara magana yana yi yana kuka.

“Haba Yaya! Ni ya kake so inyi da rayuwata…? Ka duba fa kaga irin cin zarafin da aka min? Wannan gayen fa abokina ne na ƙud da ƙud kuma yayi lalata da ƴar cikina… kawai sai ka wani ce wai inyi shiru saboda Allah? Me na yiwa mutane haka da zafi suke neman tozarta ni? Nawwara me na miki? Menene bana yi miki a duniya? Menene ba na ba ki na gata da jin daɗi da har za ki zaɓi bin wasu mazan banza ba tare da kin rasa wani abu ba? Wannan wace irin baƙar ƙaddara ce? Wannan wace irin baƙar mummunar rana ce nake gani a rayuwata?”

A taƙaice, Yaya Yusuf ya saki wani irin murmushi da ya tsaya mishi a iya fatar baki.

Da sanyin murya ya ce,

“Khamis kenan! Wani abu da kake mantawa shi ne Shi Allah ba ayi mishi wayo. Kuma dukkan alƙawarin da ya ɗaukarwa bayinshi sai ya cika musu shi. Ya faɗa mana a cikin Al-Qur’aninshi mai Girma kada ku kusanci zina… Akwai kuma hadisai masu yawa da inganci da suka zo mana da gargaɗi duk don kar mu kusanci zina.

Bayan haka ita zina dama rai gare ta, komai daren daɗewa in dai kayi ta, to tabbas sai ta dawo maka, kamar ƴar aike ce. Amma kai sai kayi biris ka take umarnin Allah ba tare da tunanin LOKACI mai zuwa da baƙin al’amura ba. Duk a tunaninka ai ka killace ‘ya’yanka a waje guda, wai kai a dabararka idan kayi hakan, kuma ka ɗauke musu duk wasu buƙatunsu to ba za su taɓa bin maza ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 58Lokaci 60 >>

1 thought on “Lokaci 59”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×