Skip to content
Part 62 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Mummunan haɗari ne ya afku wanda rabon da a samu faruwar irinsa tun kafin Gwamnan jihar kaduna Nasir El-rufa’i yayi gyaran tituna a gurare daban-daban. Wani mai mashin ne ɗauke da fasinja ɗaya da yake ta sharara bala’in gudu, a ƙoƙarinsa na yima wani mai tirela Overtaking direban tirelan a fusace yayi awon gaba da su, bayan cilli da aka yi da su gefe ɗaya mashin ɗin ta ɓangaren salansa ya danne ɗaya daga cikinsu a ƙoƙarin direban na cigaba da tafiya zuwa inda ya nufa ba tare da ya waiwayi waɗanda ya buge ba ya sake bi ta ƙafafun wanda salansa ta danne sannan ya wuce a guje.

Waɗanda hatsarin ya faru akan idanunsu da sauri suka kawar da kawunansu suna jan salati da sallallami saboda tsananin munin hatsarin. Hankulansu a bala’in tashe, mummunar haɗari ne aka yi wanda baki bazai iya fasalta muninsa ba, nan take motoci suka fara fakawa don duba abinda ya faru. Al’ummar Annabi da suke zaune gefen titi kuwa a zabure suka nufi inda hatsarin ya faru, don ganin wane hali waɗanda hatsarin ya rutsa da su suke ciki? A mace ko a raye?

Da ƙyar suka iya janye mashin ɗin da ya sauka akan jikin wanda tirelar tabi ta ƙafafunshi, wani abin ban tausayin shi ne yadda salansar mashin ɗin tayi mishi mummunan ƙuna. Irin jinin da ya zuba a wajen kuwa, babu wanda yayi tunanin wannan bawan Allah zai rayu. A haka dai aka ɗauke su biyun da mai jin jikin da me ɗan dama-daman aka yi asibiti mafi kusa da su.

Ko da suka je asibitin, ƙin kallon su aka yi saboda babu ɗan sanda a kusa. Dole sai da wasu daga cikin mutane suka koma zuwa police station mafi kusa suka taho da ƴan sanda biyu sannan aka karɓe su.

Kai tsaye aka turasu A&E.
Wanda motar ta bi ta Ƙafafunshi shi ya fi jin jiki, shi ɗayan cikin ikon Allah buguwa ce yayi sosai, sai ƙuƙƙujewa da yayi a wasu sassan jikinshi.
Ɗayan ne abin na shi yafi muni babu kyawun gani ko kaɗan, don haka a dole biyu daga cikin manyan likitocin asibitin suka dira a kan shi suna kokarin ceto rayuwarshi.

Cak! Macen Likitar ta ja ta tsaya lokacin da idanunta suka faɗa kan fuskar majinyacin da suke tsaye a kanshi bayan ɗaya daga cikin ma’aikatan jinyar ta gama goge jinin da ya wanke fuskarsa, duk a ƙoƙarinsu na ganin ko akwai wani mummunan rauni a fuskar majinyacin.
“Khamis?”
Ta furta a fili muryarta na cike da firgici da maɗaukakin tashin hankali.

Sannu a hankali ta saki kayan aikin hannunta suka faɗi ƙasa, sai kuma ta fara ja da baya tana girgiza kanta a ruɗe.
‘Duk juyin-juya hali irinna rayuwa da canje-canje masu girma da ake samu tsakanin jiya da yau kamannin Khamis na ɗaya daga cikin ababen da take ji a ranta ko tana hauka tuburan baza ta taɓa mantawa ba saboda munin tabon da ya bar ma rayuwarta.

Da mamaki sosai ɗayan likitan da suke aiki ya dakata da abinda yake yi ya tsaya yana kallonta,

“Doctor Firdausi?”
Ya kira sunanta a tausashe.

“Lafiya? Me yake faruwa?”
Ya ƙara da jefa mata tambayoyin har lokacin mamakinta bai bar kan fuskarsa ba. Ita ɗin macece mai matuƙar ƙoƙari wajen ganin ta kula da marasa lafiya kan jiki kan ƙarfi, bata kuma cika nuna tsoro ba komai munin hatsari.

Shi yasa ma kai tsaye ya nemo ta saboda yasan ita kaɗai za ta iya taimasa masa fiye da yadda yake tsammani duk kuwa da lokacin komawarta gida yayi.

‘Doctor Firdausi, Intern doctor center dake aikin internship ɗin ta a cikin asibitin. Ƙwarewarta da hazaƙarta da jajircewa a wajen aiki yasa tun ma kafin ta gama aikin asibitin suka nemi da su ɗauketa aiki na din-din-din. Duk da cewa hakan ba wani babban alfarma suka mata ba, domin Medical Director na asibitin maigidanta ne, ta ji daɗin lamarin sosai kuma ta karɓi aikin da hannu bibiyu. Haka ta kama aikinta kan jiki kan ƙarfi har zuwa yanzu da ta zama kusan ko wane likita da ma’aikatan jinya suna jin daɗin aiki da ita.’

Ganin bata ma san yana yi mata magana ba yasa shi ma ya ajiye kayan aikin hannunshi yana ambatar sunanta da ɗan ƙarfi. Ganin haka yasa sauran nurses biyu da ke tattare da su a ɗakin suka taɓa ta sannan ta yi firgigit! Tana kallonsu kamar dai a lokacin ta tuna cewa ba ita kaɗai ba ce a gurin.

A karo na biyu likitan ya sake ce mata
“Lafiya? Me yake faruwa?”

Idanunta da suka fara canja launi saboda tashin hankali ta ɗaga tana kallonshi, sai kuma ta kalli mara lafiyan da ke kwance rai a hannun Allah bai ma san inda kanshi yake ba.
“Dr. Ba zan iya wannan aikin ba, ka nemo wani likitan ya taya ka. Kayi haƙuri pls”

Da sassarfa ta juya za ta fice shi kuma yayi saurin shan gabanta yana cewa a mamakance
“Ban gane ba, Kamar ya in nemo wani likitan ya kama min? Kina sane da cewa bayan ƙwarewarki da yasa kowa ke son aiki da ke a yanzu haka babu wani likita a cikin asibitinnan sai mu biyu?”

“To ni kam dai bazan iya ba. A yau sai dai kayi mishi aiki kai kaɗai, idan kuma ya kama dole sai an taimaka maka nurses su cigaba da taya ka ko kuma ka nemi wani likitan ya shigo ya taya ka.”

Ta yi maganganun da ke nuna ranta ya fara ɓaci da yadda yake neman tursasa ta.

Kallonta yake kawai, a zuciyarsa yake ayyana ko dai gamo tayi? Saboda kwata-kwata ya kasa fahimtar inda zantukanta suka nufa. Nannauyan azuciyar zuciya ya sauke da ya tuna hakan ya saɓa ma ɗabi’arta, wataƙila tana da ƙwaƙƙwaran dalili na turjewar da tayi, don haka ya sassauta murya ya cigaba da cewa,

“Kiyi haƙuri. Allah ya huci zuciyarki. Amma don Allah ki faɗa min me yake faruwa ne? Kin san shi ne? Ko kuwa wani abu ne na daban yake faruwa? Ai koma menene ina ga kiyi hakuri ki ajiye shi a gefe, ki duba halin da yake ciki don Allah mu cece shi tukunna. Ko menene a tsakaninku sai ya zo daga baya…”

“Bazan iya ba.”

Ta katse shi a zafafe. Sai kuma cikin raunin murya kamar za ta fashe da kuka ta ce
“Da ka san ko wanene wannan mugun mutumin kai kanka baza ka taɓa marmarin taimaka masa ba. Ina mai sake tabbatar maka da cewa da ka san abinda ya aikata, da haƙiƙa kai ma ba za ka ba ni goyon bayan in kalleshi ba, sai dai ka bani ƙwarin gwuiwar in bar shi ya mutu kawai”

Cike da tsananin mamaki yake kallonta. Da ƙyar ya iya buɗe baki ya cigaba da rokon tayi hakuri ta daure, amma fafur ta ƙi. Babu irin magiya da ban baki da basu mata ba amma ta ƙi saurarensu. Ƙarshe ma kukan da take ta riƙewa ne ta fashe musu da shi sannan ta raɓa ta gefenshi ta fice daga ɗakin da sassarfa.

Tana fita suka ci karo da MD na asibitin da tawagarshi su kuma zasu shiga saboda hayaniyar da suka ji tana tashi sama. Bata yi wata-wata ba ta faɗa jikinshi ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai.

Da sauri ya tattageta cikin jikinshi yana tambayar lafiya? Ta kasa yi mishi bayanin komai sai Dr. Hassan ne ya matsa yana bashi labarin abinda yake faruwa.

Cikin kukan da take yi ne ya tsinto kalmar
“Khamis ne”
Da take ta maimaitawa cikin rishin kuka.

Ya riga ya san duk wani labari na ta da abinda ya faru da rayuwarta na baya daɗi da akasin haka. Sunan Khamis shi ne kalmar da har gobe ta kasa mantawa, ɗaiɗai ranar da ba ta kama sunan taja mishi Allah ya isa da fatan afkuwar masifu kala-kala. Don haka kai tsaye ya fahimci abinda yake faruwa.

A hankali ya ja ta suka kauce daga idanun jama’a yayi gefe da ita yana lallashinta da kalaman ban hakuri da ban baki har ya samu tayi shiru.

“Haba Babyna. Na zaci lokacin fushi da riƙo ya wuce a rayuwarki tuntuni duba da irin cigaba da ɗaukakar da Allah yayi miki bayan duk abubuwan da suka faru a baya? Kar ki manta, Allah yana son masu haƙuri da yafiya a inda suke da ƙarfin ramuwa kan abinda aka musu.”

Ta girgiza kai tana fyace majina cikin hankicin da ya miƙa mata tace,
“Ka fi kowa sanin irin rashin adalcin da wannan mutumin yayi min. Sai da yasa na tsani rayuwa, na dinga kokonton ko in kashe kaina kawai in huta? To ni kuma akan me zan ji tausayinshi? Me yasa zan ceci tashi rayuwar bayan ni ya sanya tawa cikin garari da tashin hankali?!”

Ƙara janta yayi cikin jikinshi yana shafar bayanta cike da alamun lallashi ya ce,
“Idan kika yi hakan, kin nuna shi ya faɗi, ke kuma kin yi nasara. Saboda yafiya da hakuri suna cikin kyawawan halaye da aka san magabatanmu na ƙwarai da su. Ki taushi zuciyarki Nanata, kiyi riƙo da hakuri kamar yadda na sanki da shi. Wannan aikin jahadi ne zaki yi, kuma Allah shi kaɗai yasan irin ladar da zai baki. Kada ki manta da alkawarin da kuka ɗauka yayin gama makarantarku, na za ku kula da majinyata a kowane hali. Kiyi hakuri kin ji? Haba babyn Malaminta, haba ƴanmatan Malami?”

Ƙuru tayi mishi da idanu tana mar-mar da ƙwayoyin kamar za ta saka kuka, ta kasa cewa komai. Sai shi ne ya sake cewa

“To ko ɗan murmushin ma yau ba za a yiwa Malamin ba ya ji sanyi-sanyi a ranshi?”

Babu yadda ta iya hakanan ta saki ranta ta ɗan ware ta fara mishi murmushi sama-sama.

Da haka ya samu ya cigaba da lallaɓata da tausasan kalamai har de ta yarda za ta koma cikin ɗakin su duba Khamis ita da likitan da ke kan aikin. Sai da ya raka ta har bakin ƙofa ta shige ciki sannan ya koma Ofis ɗin sa.

Sosai ta danni zuciyarta ta yi iyaka bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta ba Khamis kulawar da ta dace. Ba tare da ta duba abinda yayi mata a baya ba ko kuma tayi yunƙurin aikata wani mummunan abu a kanshi don ramuwar gayya duk da damar da ta samu na yin hakan. Yanayin ciwukan da ke jikinsa sunyi munin da dole sai sun buƙaci taimakon wasu likitocin guda biyu bayan su, don haka ta nufi hanyar fita daga ɗakin a gaggauce don zuwa Ofishinta tayi magana da sauran likitocin a wayar salula.

Tana fitowa daga ɗakin ta kama hanyar Ofishinta ta ci karo da Yaya Yusuf ya shigo gurin a hargitse. Kallo ɗaya tayi mishi daga sama har ƙasa ta fahimci irin ɗimauta da firgicin da yake ciki, takalman kafarshi ma ɗaya sau ciki ɗaya buɗaɗɗede, ga wuyan riga a shagiɗe, hula kuwa ba a maganarta.

Ashe ɗaya daga cikin waɗanda suka kawo Khamis asibitin ne ya ɗauki wayarsa, ko da ya duba emergency list ɗin shi sai ya ga sunan Yaya Yusuf, don haka ya kira ya sanar da shi halin da ake ciki. Daga yanayin halin da yake ciki yasa duk mutanen wajen suka fidda rai da shi, shi yasa ko da mutumin ya kira shi ma kai tsaye faɗa mishi ya yi sai dai yayi hakuri, amma ba lallai yana da rai ba.

Irin yadda ya fito a haukace, Aunty Zainab tana tambayarshi me yake faruwa ko tanka mata baiyi ba, ya faɗa mota a hanzarce ya fige ta a guje, iko da kiyayewar Allah ne kaɗai suka kai shi asibitin lafiya.

Yana ganin Firdausi kuma sai ya ja ya tsaya turus, jikinsa a sanyaye, shi da ita suka fara kallon-kallo. Ƙwarai ya tuna ta, ta ina ma zai iya manta ta bayan duk irin ta’asar da Khamis yayi a rayuwarta?

Ita ma da ta gane shi sai taja ta tsaya tana mishi wani irin kallo, ko da ta tuna irin tsayuwar dakan da yayi mata a wancan lokacin sam ya ƙi goyon bayan ɗan’uwansa sai ta sunkuyar da ƙwayoyin idanunta ƙasa, ta duƙa har ta gaishe shi a ladabce. A zuciyarta tana sake ƙudurta lallai za ta yi iyaka bakin ƙoƙarinta don ceto ran Khamis, ko ba don kowa ba, don Yaya Yusuf kaɗai da ya kasance mutumin kirkin da ita da iyayenta suka daɗe basu manta karamcinsa ba.

A mutunce ya amsa gaisuwarta, a fuskarsa take karanta mamakin da yake yi na ganinta a matsayin likita. Amma ko kusa bai tambayeta yadda aka haihu a ragaya ba har ta wuce shi a gaggauce zuwa ofishinta, yana nan tsaye ta sake dawowa ta wuce shi ba tare da ta sake ce mishi kanzil ba.

Cikin ikon Allah bayan wasu awoyi sun yi nasarar ceto rayuwar Khamis. Ƙafarshi ta hagu dai ta riga ta gama ragargajewa, dole sai dai a cire ta gaba-ɗaya saboda ba yadda za ta gyaru, ita kuwa ta damar za a iya cetonta amma sai da taimakon ƙarafuna. Rabin jikinshi kuwa tun daga ruwan cikinshi zuwa cinyarshi yayi wani irin mummunan ƙuna sanadiyyar salansar da ya kwanta a jikinsa. Sauran jikin nashi kuma lafiya lau sai ƙwarzane-ƙwarzane nan da can da baza a rasa ba.

Yaya Yusuf yana kuka share-share da hawaye kamar ƙaramin yaro haka ya sanya hannu a takarda aka yi aikin Khamis. A rayuwarshi tunda yake bai taɓa shiga kwatan-kwacin tashin hankali irin wannan ba, ko lokacin rasuwar iyayensu kuwa.

Domin a wannan lokacin zafi ne kan zafi, yana cikin firgici da tashin hankalin irin yanayin da suka tsinci Nauwara da idanuwansu sai kuma ga wannan mummunan hatsarin da ya rutsa da Khamis.

Shi kam dai ya fara sallamawa da rayuwar duniya, yana ga damuwar Khamis da ta iyalinshi ne za su zama sanadiyyar mutuwarshi.

Yana tsaye kamar mutum-mutumi aka gunguro Khamis zuwa ɗakin da za’a kwantar da shi, ƙafafuwan da aka yi aikin lulluɓe da bandeji, rabin jikinshi ma gaba-daya lulluɓe da bandeji. Kamar gawa, haka aka wuce da shi har zuwa ɗakin da za’a kwantar da shi shi kaɗai.

Da ƙyar ya iya daidaita nutsuwarsa yayi ma waɗanda suka yi jigilar kai su Khamis asibiti godiya mai yawa kafin ya zauna a reception ya buga tagumi da hannu bibiyu, zuciyarsa a cunkushe. Ya ma rasa wani irin tunani ya kamata yayi?

*****

Sai da Khamis ya kwashe kwanaki uku kafin ya farfaɗo sosai ya dawo cikin hayyacinsa. A wannan ranar yasan ashe ma kuka rahama ne. Domin kukan ma gagararshi ya yi, Idanunshi sun bushe ƙayau babu alamun ɗigon ƙwalla a cikinsu. Sai wani irin zazzafan suya da ƙuna zuciyarsa take yi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 61Lokaci 63 >>

1 thought on “Lokaci 62”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×