Idan ya ɗaga idanu ya kalli guntulalliyar kafarshi, da wacce aka yiwa aiki aka tare gefe da gefenta da ƙarafuna, da irin azabar ƙunan da yake ji a jikinshi wanda kullum sai an buɗe an wanke sannan a sake naɗewa da bandeji.
Sai kawai ya ɗage kai sama ya saki wani irin huci mai zafi da numfarfashi sama sama kamar mai fama da asma. Magana ma ta gagare shi, duk yadda Yaya Khamis ke jera mishi sannu ya kasa buɗe baki ya amsa, sai dai ya dinga gyaɗa kai yana cije baki gefe ɗaya kamar mai. . .
hakane
Allah ya rabamu da mugun jii da mugun gani
Allah ya shiryar mana da zuriya
Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani