Skip to content
Part 63 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Idan ya ɗaga idanu ya kalli guntulalliyar kafarshi, da wacce aka yiwa aiki aka tare gefe da gefenta da ƙarafuna, da irin azabar ƙunan da yake ji a jikinshi wanda kullum sai an buɗe an wanke sannan a sake naɗewa da bandeji.

Sai kawai ya ɗage kai sama ya saki wani irin huci mai zafi da numfarfashi sama sama kamar mai fama da asma. Magana ma ta gagare shi, duk yadda Yaya Khamis ke jera mishi sannu ya kasa buɗe baki ya amsa, sai dai ya dinga gyaɗa kai yana cije baki gefe ɗaya kamar mai naƙuda.

Duk waɗannan kwanaki Yaya Yusuf ne tsaye a kanshi, shi ne yake ta ɗawainiya da shi babu gajiyawa. Idan ya tsaya ya ƙare mishi kallo sai ya ga tsakanin shi da shi ɗin ma babu wani bambanci, saboda yadda Yaya Yusuf ɗin ya rame kamar wani majinyaci.

Duk yadda iyalan ɗan’uwanshi da ƴaƴanshi ke ta safa da marwa a cikin asibitin hankulansu a tashe har su gama zamansu su fice ba ya taɓa buɗe idanu ya kalli ɗaya daga cikinsu. Shi kaɗai yasan irin ƙunci da raɗaɗin da ke danƙare a zuciyarsa.

Dr. Firdausi kam tunda suka mishi aiki, ta kuma duba shi da mishi tambayoyi a ranar da ya farfaɗo ya dawo hayyacinsa sosai, bata ƙara tunkarar inda yake ba.
Sai Doctor Hassan ne ke kulawa da shi.

A kwana na biyar, Yaya Yusuf yana tsaye a gefen gadon na shi da safe yana ƙoƙarin haɗa mishi shayi, ya ɗaga kai yana kallon Yayan nashi. Sai kuma ya kira sunanshi murya a dusashe kamar wanda yayi watanni yana mura
“Yaya!”

Yaya Yusuf tsayawa yayi da abinda yake yi yana kallon Khamis ɗin da mamaki, don tun sanda ya farfaɗo wannan ce magana ta farko da ya fara yi, kamar wanda aka mishi ɗinki a baki. Sai kuma ya amsa a mamakance
“Na’am Khamis, kana buƙatar wani abu ne?”

Sai a lokacin wasu zafafan hawaye suka gangaro mishi.

“Ka yi hakuri Yaya”
Ya sake faɗa a raunane.

“Ka yafe min don girman Allah ba don halina ba. Haƙiƙa na ci amana. Ban taɓa zama sanadin farin ciki a gareka ba sai sanadin baƙin ciki, wahala da zagi. Ni nasan mai laifi ne a wajenka amma don Allah ka yafe min ba don halina ba.”

Yadda yake maganar yana kuka sosai sai Yaya yaji shi ma gaba-ɗaya zuciyarshi ta karye. Ya haɗiyi wani dunƙulallen abu da ya tsaya mishi a maƙoshi, da sanyin murya ya ce,

“Kar ka damu Khamis, ka sani, ni dama ban taɓa riƙe ka a cikin raina ba. Kullum ina yi maka addu’a ne da fatan Allah ya shirye ka. Ka kwantar da hankalinka, mu cigaba da addu’ar Allah ya baka lafiya ya tashi kafaɗarka. Ni dai fatan da nake yi maka shi ne Allah yasa hakan ya zama sanadin shiriyarka, Allah kuma ya yafe maka kura-kuranka!”

Kuka ya ƙara fashewa da shi sosai, sai maimaita kalaman
“Ka yafe min Yaya don Allah ka yafe min! Ka roka min su Mannira su yafe min, haƙiƙa ban zama Uba na ƙwarai a gare su ba. Don Allah ka kira min Firdausi in bata hakuri, duk da na kasance azzalumi ne a gurin mutane da yawa, amma ina tunanin idan ta yafe min ko ɗan yaya ne zan samu sassauci a cikin tulin azaban da ke jira na. Idan kuwa bata yafe min ba, nasan wallahi wannan azabar da nake ciki kaɗan ne daga wanda ke jira na a lahira! Astagfirullah, Allah na tuba ka yafe min! Astagfirullah wa atubu ilaihi! Astagfirullah!!”

Hankali tashe Yaya Yusuf ya dafa kafaɗarshi ganin sumbatun na shi sun fara yawa. Da taushin murya ya ce,

“Ka bi komai a sannu Khamis, kayi a hankali kada ka janyowa kanka wata cutar ta daban kuma. Idan ka warke, sai ka bi duk waɗanda ka san ka zalunci rayuwarsu ka basu hakuri ka nemi yafiyarsu!”

A magauce ya hau girgiza kai yana ƙara ƙarfin kukansa,

“Ni dai Yaya ka kira su in nemi yafiyarsu. Yaya idan na mutu ban nemi yafiyarsu ba Allah ba zai rahamsheni ba! Yaya don Allah ka taimaka ka kaini wajensu in basu hakuri.

Yaya ka taimaka min!!”

Gaba-ɗaya ya bi ya susuce yana ta sambatu, tun suna bada ma’ana har suka daina. Dole Yaya ya fita ya samo likita ya danna mishi allurar barci kafin suka samu sauƙin surutan da yake yi.

Kujera Yaya Yusuf ya samu ya zauna daɓas yana sharce ruwan hawaye. Gaba-ɗya jikinshi ya gama yin sanyi. Tunanin halin Khamis ya dinga yi tun yana ɗan saurayinshi har kawo wa yanzu. Sai yaji tausayin ɗan’uwan na shi ya ƙara dabaibayeshi.

Haƙiƙa Khamis kaso saba’in cikin ɗari na rayuwarshi bai yi rayuwa mai kyau ba, bai kuma bi tafarki nagari ba. Tsoro ne ya ƙara lulluɓe shi, a fili yake roƙon Allah kar ya kashe Khamis sai ya nemi yafiyar waɗanda ya zalunta kuma ya aikata aiki na ƙwarai.

******

Daga yadda Mannirah take yawan kiranta cikin kuka take bata labarin irin munin hatsarin da Daddyn nasu yayi, da kuma yadda take sake jaddada mata ƙorafin yadda gaba ɗaya rayuwar Nauwara ya canja. Sai ramewa take yi a tsaye kamar mai cutar ƙanjamau, kuma a mafiyawancin lokuta tana farkawa tsakar dare taga Nauwarar tana sallah tana kuka, tambayar duniyar nan tayi mata amma sam ta ƙi faɗa mata abinda yake damunta.

Waɗannan dalilan suka harhaɗu suka sa a karo na farko tun bayan barowarta kaduna fiye da watanni goma ta ji hankalinta ya koma Kaduna. Ba kuma wai don ta koma da zama na din-din-din ba, ko kuma don ta koma ma auren Khamis, sai don kawai ta je ta duba jikinshi albarkacin ƴaƴa da ke tsakaninsu sannan ta titsiye Nauwara ido da ido ta faɗa mata abinda yake damunta.

Saboda duk irin hargagin da masifa da rarrashin da tayi ta yima Nauwarar a waya ta ƙi buɗa mata gaskiyar abinda yake damunta. Don haka ta yanke shawarar lallai ya kamata taje ta gane ma idanuwanta ta jiye ma kunnuwanta gaskiyar abinda yake faruwa.

Izuwa wannan lokacin duk wanda ya kalli Ziyada indai ba saninta yayi a baya ba zai rantse da girman Allah ba ita ce ta haifi su Nauwara ba. Daman tana da kyawun jiki sosai, kulawa da hutu da kwanciyar da ta samu a gurin ƴar’uwarta yasa ta ƙara kyau da ƙuruciya sosai. Tuni zawarawa manyan masu kuɗi abokan mijin Yayarta sun fara kai mata cafka, fau-fau tayi watsi da su a cewarta ita da aure ba yanzu ba, a wasu lokutan ma kai tsaye take faɗin ta gama aure har abada.

Idan ta faɗi haka sai dai Aunty Ruƙayya ta kalle ta tayi dariya kawai. Domin ta san abu ne da bazai yiwu ba da ƙuruciyar Ziyada su zura mata idanu ba tare da aure ba. Lokaci dai suka ba ta ta gama hutawa hankalinta ya kwanta kafin su sake matsa mata da zancen auren.

Canji ba’a jikin Ziyada kaɗai ba, hatta su Batula sun ƙara canjawa, sun goge sun zama kamar ƴaƴan turawa. Abinku da harkar kuɗi, tuni har an gama komai sun jona karatun boko da islamiyarsu a Lagos. Shi yasa ko da Mummynsu tayi shirin tafiya kaduna bata tsara da su ba, duk da sun san Daddynsu ba lafiya, sai dai an ɓoye musu irin jin jikin da yake yi.

Barr. Muhyi abokin aikin Aunty Ruƙayya kuma ɗaya daga cikin zawarawan Ziyada ba yadda bayyi su tafi tare ba ta ƙi, a ƙarshe ma bai san takamaimai ranar tafiyar nata ba sai a bakin Aunty Ruƙayya yake ji ai Ziyadan ta bi jirgi ita da Alhaji Sherif (mijin Aunty Ruƙayya) sun tafi kaduna a safiyar ranar.

Sakalau yayi da baki jikinsa a sanyaye, Allah ya sani yana tsananin ƙaunar Ziyada, amma irin yadda take wasa-rere da al’amarinshi shi ne abinda ke ɗaga mishi hankali. Shi kuwa bai fara son ta don ya daina a sauƙaƙe ba, don haka ya ture duk wasu ayyuka da suke gabansa a wannan ranar ya fara shirye-shiryen bin ta Kaduna washe gari.
‘Mai son ɗan tsuntsu ai shi ke bin sa da jifa in ji Mal bahaushe.’

Ko da isar Ziyada da Yaya Babba (yadda take kiran mijin yayarta) Kaduna kai tsaye asibitin da aka kwantar da Khamis suka wuce. Bayan ta yi waya da Yaya Yusuf ya ba su cikakken kwatance.

Hankalinta ne ya tashi sosai, tsoron Allah da ganin girma da buwayarsa ya ƙara lulluɓeta lokacin da ta ga halin da Khamis ya koma cikin ƙanƙanin lokacin. Lallai mai rai ba’a bakin komai yake ba, kuma duk iskancin da bawa zaiyi talala kawai Ubangiji ke masa, amma idan ya tashi damƙarsa zai masa mummunan kamu ne a lokacin da bai taɓa tsammani ba.

“Ziyada? Kin ga halin da nake ciki ko? Don girman Allah ki yafe min…”
Kalaman da Khamis ya furta mata cikin kuka.

Bata san hawaye ke tsiyaya a idanunta ba sai da Yaya Babba ya ciro wani lallausan tissue daga aljihunsa ya miƙa mata. Har suka bar asibitin zuwa gidan Yaya Yusuf in da su Mannira suke ta kasa furta komai ga Khamis, duk kuwa da yadda yayi ta mata naci cikin kuka da azabar ciwo yana mata magiyar ta yafe mishi. Ga kuma yadda ya ƙi kwantar da hankalinshi, shi yasa ako wane lokaci ciwukan jikinshi kwan gaba kwan baya suke yi. Sauƙin da likitocin suke hange zai samu cikin ƙanƙanin lokaci idan ya kwantar da hankalinshi ya nutsu, har yanzu ya ƙi samuwa.

Duk yadda Babban Yaya yaso ta je gidansu ta huta sosai kafin taje ganin ƴaƴanta ta kasa. Haƙuri ta bashi kan ko ta zauna hankalinta bazai kwanta ba, hakanan ya haɗa ta da direba aka wuce da ita gidan Yaya Yusuf. Ganin yadda Nauwara ta koma ta rame ta lalace shi ne abinda ya ƙara ɗaga mata hankali. Ƴaƴan nata biyu haka suka ruƙunƙumeta suna rusa kuka kamar ransu zai fita. Ko basu faɗa mata ba, ta san sun yi kewarta ba kaɗan ba kamar yadda ita ma tayi kewarsu.

Amma irin kukan da Nauwara take yi ya bayyana mata lallai bayan kewa da damuwar halin da Daddynta ke ciki akwai wani abu a ƙasa da yake damun babbar ƴar tata.

Tsoro da fargaba ne ya ƙara lulluɓe ta, tsoron rayuwar duniya da irin abinda rayuwar ta ƙunsa. Fargabar abinda kunnuwanta za su jiyo mata daga bakin Nauwara bayan waɗanda idanuwanta suka gane mata dangane da halin da Khamis ke ciki.

Tun kafin rabuwar Khamis da Ziyada akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin Aunty Zainab da Ziyada. Ko a yanzu, haka ta baibaye gaban Ziyada da kayan ƙwalam da maƙulashe kala daban-daban ta zauna suna jajantawa juna kan abinda ya same su. Kafin daga bisani taja yaranta da ƙanwarta Aunty Ikilima suka fice suka ba ta damar ganawa da ƴaƴanta.

“Nauwara? Faɗa min. Mecece matsalarki? Yau dai ga ni ga ki ido da ido. Ko akwai wani abu da za ki ɓoye min a matsayina na mahaifiyarki?”

Jikinta a sanyaye ta girgiza kai alamar babu. Sai kuma ta duƙar da kai ƙasa ta cigaba da matsar ƙwallah, zuciyarta a ƙuntace.

Kamar Mannira ta fahimci sirri mai ƙarfi ƴar’uwar tata ke son yi da mahaifiyarsu don haka ta basu uzuri ta fita waje ta basu guri.

Amma ko bayan fitar tata bata canja zani ba, dambu da taliya Ziyada ta juya Nauwara amma ta ƙi buɗe baki ta faɗa mata ainahin abinda yake damunta. Tun Ziyadar tana bin ta da lalama har zuciyarta takai ƙololuwa gurin ɓaci. Ta kalle ta ranta a ɓace, idanunta sun kaɗa sunyi jajur saboda fushi da ɓacin rai. Muryarta na fita sama-sama ta ce mata a tsawace
“Ko dai irin mummunar ƙaddarar da ta afkawa ƙanwarki ne ke ma ta afka miki…?”

“Tawa ba ƙaddara bane Mummy…”
Ta katse uwar da sauri hawayenta na ƙara ƙarfin gudu a kumatunta. Tafukan hannayenta biyu tasa ta rufe fuskarta ta cigaba da magana cikin kuka.
“Sharrin shaiɗaniyar ƙawa da son zuciyata haɗe da kwaɗayin abinda ban rasa ba a gidan Ubana suka haɗu wajen ja min gora na jefa rayuwata cikin garari Mummy… Ido da Ido Daddy da Abba Yusuf suka kama ni a hotel Mummy… Amma na rantse da Allah a lokacin ban kai ga aikata komai ba… sai dai kuma ba wannan lokacin ne na farko ba… Abu ne da ya sha faruwa a mabanbantan lokuta…”

Saukar duka ta ko ina a sassan jikinta su suka sa tayi shiru ba don ta gama zazzage maganganun da suke danƙare a cikinta ba. Kamar dutse, haka ta zauna kakim, kamar de ba jikinta ake duka ba. Ko kuma ba ta jin zafin dukan da ke sauka a jikinta.

Amma fa ba ko ɗaya a cikin abubuwa ukun, tana jin shigar dukan a jikinta fiye da yadda ake tsammani. Kawai dai ta yi shiru ne tana karɓar dukan domin a ganinta ta cancanci fiye da wannan hukuncin.

Kuma wani abin ikon Allah shi ne da yake ƙofar ɗakin a rufe ne, kuma Mummy Ziyada tana dukan idanunta ne kaɗai ke tsiyayar hawaye zuciyarta na tafarfasa, ba wasu maganganu ko faɗa take yi ba, babu wacce tayi yunƙurin kawo ma Nauwara ɗauki daga waje sai da tayi ma Nauwara lilis, ta gaji don kanta sannan ta yarda wayoyin caja biyu da ta fincikesu a jikin bango ta zube a ƙasa ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka.

“Na tuba Mummy… kiyi haƙuri… Don girman Allah ki yafe min. Na ɗaukarwa Allah alƙawarin bazan sake aikatawa ba ko da kuwa zan shiga yanayin da in ban aikata ba zan rasa rayuwata. Abba Yusuf ya ce nan da wata uku zai ɗaura min aure da duk mijin da yaga dama… Yanzu haka zaman Istibra’i nake yi…”

Da saurin gaske Mummy Ziyada ta runtse idanu da ƙarfi tana jin saukar kalmar ƙarshe na kalaman Nauwara kamar zuban ruwan dalma a zuciyarta.

‘Barewa baza tayi gudu ba ɗanta yayi rarrafe… Abinda kayi shi za’ai maka.’
Sai yau ta ƙara gasgata waɗannan maganganu guda biyu.

Kukanta ta ci ma’ishi ba tare da ta iya sake kallon Nauwara ba ko kuma ta amsa ɗaya daga cikin kalaman neman yafiya da jaddada tuba da ƴar tata ke yi ta miƙe tsam! Mayafi da jakarta da suke ajiye gefe ɗaya ta ɗauka ta rataya jakar, ta yafa mayafin, ta fice daga ɗakin.

“Umman Nauwara ina za ki haka? Yanzu na tura Mannira ta bi direba sun je kai abinci wa su Abbansu a asibiti…”

“Aunty Zainab ba nisa zanyi ba, saƙo zan amso anan waje.”
Ta amsa ma Aunty Zainab da ɗasasshen murya sannan ta ƙara sauri a hanzarce ta fice daga falon don ma kar ta ƙara yunƙurin tsayar da ita.

Zuciyarta zafi yake sosai kamar zai babbake. Irin bala’in zafin da tunda uwarta ta haifeta a duniya bata taɓa jin irinsa ba. Ba zuciyarta kaɗai ba, hatta jikinta ya ɗau wani irin zafi ne kamar ta yaye kayan jikinta ta watsar.

Gidan kuwa kamar tana cikin ɗakin gasa biredi haka take ji a jikinta. Idan ba fitar tayi ba, ta zauna ta cigaba da kallon Nauwara, ko shakka babu za ta iya tsine mata albarka akan abinda sam ba laifinta bane, idan da laifinta a ciki ma, bai fi kaso talatin cikin ɗari ba.

Sakayya ce da aka yada sharri a baya ko an ƙi ko an so dole a tsince shi a gaba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 62Lokaci 64 >>

2 thoughts on “Lokaci 63”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×