Skip to content
Part 64 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

“Khamis ka cuci rayuwata, Allah ya isa tsakanina da kai.”

Tayi maganar a fili cikin kuka. Ɓacin rai da baƙin cikin irin mummunan gadon da Nauwara tayi na halin Khamis yasa hankalin Ziyada gushewa, tayi ta ja mishi tsinuwa da munanan alkaba’irai iri-iri. In da Allah ya taimaketa shi ne tana fita daga gidan bata daɗe tana tafiya ba ta samu mai adaidaita sahu. Da babu shakka kallon taɓaɓɓiya a cikin sababbin kaya za’a dinga yi mata.

Da ƙyar ta iya ɗaga ma mai keken hannu ba tare da ta faɗa mishi inda za ta je ko kuma suyi ciniki ba ta faɗa ciki.

“Muje, muje kawai Malam.”
Ta iya faɗa mishi da ƙyar, muryarta na fita a shaƙe sosai kamar wacce aka riƙewa maƙogwaro.

Cikin keke napep ɗin, sai ya zame mata kamar wata mafaka ko kuma lungun da aka umarceta da ta laɓe tasha kukanta. Kuka tayi ma’ishi, zuciyarta cunkushe da tsanar Khamis da duk wani abu da ya danganci Khamis ɗin.

Duk da ita da kanta ta san waɗannan ƙaddarorin abubuwa ne da ita da bakinta tasha faɗan zai biyo layin ƴaƴanta saboda munanan halayen ubansu ta ja ma Khamis Allah ya isa ya fi baki ashirin. A yadda take jin matsanancin tsanarsa a zuciyarta, tana ga ko da za ta ganshi cikin azaba fiye da wanda yake ciki yanzu haka a asibiti baza ta taɓa yafe mishi ba.

“Hajiya har yanzu baki faɗi inda zan kai ki ba?”
Mai keken ya katse mata hanzari bayan ya ji kukan nata ya ƙi ƙarewa.

Ta buɗe baki za ta amsa mishi wayarta da ke cikin jaka ya fara ringing. A kasalance ta janyo wayar daga cikin jaka, Abba Yusuf ke kiranta.

Ƙaramin tsaki taja tana jin wani masifaffen haushinshi saboda kusancinshi da Khamis ɗin, ba tare da ɓata lokaci ba ta katse kiran tana faɗawa mai keken inda zai kai ta. Ta ɗaga wayar da nufin mayar da ita cikin jaka wani kiran ya sake shigowa, bata ɓata lokaci ba ta katse. A jejjere sau huɗu yana kiranta tana katsewa sannan ya haƙura, a karo na biyu ta sake jan tsaki, ta buɗe jaka za ta saka wayar a ciki wani kiran ya sake shigowa, amma saɓanin Abba Yusuf, Babban Yaya ke kiranta.

Kamar baza ta ɗauka ba, saboda ta san shi da damuwa da halin da duk wani makusancinsa ke ciki, jin muryarta a ɗashe zai sake tabbatar masa da bayan rabuwarsu ma kukan ta cigaba da yi duk da yadda yai ta jaddada mata kalaman ban haƙuri da rarrashi kafin rabuwarsu.

Har ta saka wayar a jaka, sai kuma wata zuciyar ta bata shawarar ta ɗaga kiran, kila wani babban uzurin ne yasa shi kiranta a irin wannan lokacin da a tunaninsa tana tare da ƴaƴanta.

“Ziyada? Kina ina ne?”

Tambayar da ya fara jefa mata kenan ba tare da ya amsa sallamarta ba.

“Ga ni a cikin Keke napep zan zo nan gidanka…”

“Ok… Yi maza ki yiwa mai keken umarnin ya juya da ke zuwa asibitin da Daddynsu Nauwara ke kwance. Ni ma ga ni nan tahowa yanzunnan, mu haɗu acan ɗin.”

Bai bata damar cewa komai ba ƙit, ya katse wayar. Haka nan ba don zuciyarta na son sake tozali da Khamis ko wani da ya danganci ahalinsa a wannan lokacin ba ta faɗa ma Mai keken asibitin da zai kai ta. Don dai kawai Babban Yaya ne, tsakaninta da shi babu musu ko jayayya ko da kuwa zuciyarta bai so aikata abinda ya umarce ta ba.

Kasancewar sun fara nisa a tafiya zuwa gidan Babban Yaya, ko kafin su isa asibitin sun sake ɓata wasu lokuta masu ɗan dama. Wani abu da yasa ƙirjinta bugawa shi ne ganin Babban Yaya tsaye a bakin ƙofar asibitin yana jiran ƙarasowarta, shi ne ma ya sallami mai keke napep ɗin.

“Yaya? Lafiya kuwa? Me yake faruwa?”
Ta jera mishi tambayoyin idanunta warwaje tana jin yadda ƙirjinta ke cigaba da bugawa akai akai.

Bai amsa mata ba, a madadin yayi magana ma sai tsintsiyar hannunta ya riƙe da sauri suka nufi cikin asibitin. Fuskarsa babu walwala ko kaɗan.

Wani abu da yasa ƙirjinta tsananta bugawa shi ne ganin Nauwara da ta baro a gida rakuɓe a ƙofar ɗakin da Khamis yake kwance tana rusa kuka kamar ranta zai fita. Kallo ɗaya tayi ma yarinyar suka faɗa cikin ɗakin da sauri saboda wani irin nishi da gurnani mai ƙarfi da suke jiyowa daga cikin ɗakn kamar na mai naƙuda.

Ko da suka shiga cikin ɗakin…
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.”
Wani irin mummunan yanayi ne suka tarar da Khamis a ciki yanayi mafi tsananin muni fiye da ganin da tayi mishi ɗazu.

Fuskarsa, sassan jikinsa gaba ɗaya sunyi baƙi sosai kamar wanda yayi gobara. Kuma wannan gurnani da nishi mai ƙaran da suke jiyowa tun daga waje ba kowa yake yi ba face shi.

Yaya Yusuf, Kawunnan Khamis guda biyu da ƙanwar mahaifiyarsu suna tsaye a gefen gadon suna kuka suke biya mishi kalmar Shahada amma sam Allah bai bashi ikon kamawa ba.

Mannira ce take zaune a gefen kanshi ba tare da wani ƙyanƙyami ko tsoro ba hannunta guda riƙe cikin nashi, idanunta na tsiyayar da zafafan hawaye. Sannu a hankali take rera mishi karatun Suratul-Yaseen cikin zazzaƙar muryarta da ke fita da sautin kuka.

Har kusa da gadon Babban Yaya ya ƙarasa da Ziyada sannan ya saki hannunta. A tsorace kuma cike da firgici ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka sannan ta juya da sauri za ta fice daga ɗakin.

Da saurin gaske Inna Rabi ta damƙo kafaɗunta, cikin kuka da muryar da ke bayyana tashin hankali ƙarara ta fara magana tana cewa.

“Ziyada, kiyi haƙuri don girman Allah. A yanzu Kin ga halin da uban ƴaƴanki yake ciki, babu abinda yake nema sai gafara da yafiyarki da duk waɗanda ya zalunta ko zai samu sassaucin wannan azaba da uƙubar da yake ciki. Ba gobara yayi ba, yadda kika ganshi a haka muka shigo muka tarar da shi a babbake, ɗan’uwansa yana zaune akan dadduma yana barci shi ma bai san yadda al’amarin ya afku ba. Wani ƙudira da irada ta Ubangiji ce kawai ta sauka a kansa, a ɗazu sadda muka shigo, mun tarar yana iya magana cikin ihu yake kiran sunanki, mahaifiyarsa, da sunayen mata mabanbanta yake roƙon ku yafe mishi, daga bisani kuma bakin ya ɗauke ɗif, sai nishi da gurnanin azaba da uƙuba. Wannan shi ne dalilin da yasa Yusuf ya kira ku ahalinshi na kusa domin ku yafe mishi.

Kin gani dai, a yanzu babu abinda yake buƙata sama da yafiyarki ko Allah zai sa ya karɓi kalmar Shahadar da muke ta biya mishi tun ɗazu amma ya kasa buɗe baki ya amsa. Don Allah ki yafe mishi ko don darajar ƴaƴan da ke tsakaninku Ziyada.”

Duk wannan dogon jawabin da Inna Rabi tayi ma Ziyada ta kasa magana, kuma ta kasa furta kalmar yafiyar da Khamis ke buƙata a gare ta. A maimakon haka ma, duƙewa tayi a ƙasa ta ƙara fashewa da wani mahaukacin kuka.

Wani abu da halin zuciya da ako yaushe ta fi umarni da mummunan aiki sai a lokacin take ta tunasar da Ziyada irin cutarwa da zaluncin da Khamis yayi mata a zamantakewar aurensu. A cikin taƙaitattun lokutan har zuwa kan ƙaddarar fyaɗe da ya afkawa Mannira sanadiyar sakacinsa da kuma mummunar gadon da Nauwara tayi na irin halayensa.

Hankali tashe Babban Yaya ya ƙarasa kusa da Ziyada zuciyarsa cike da matsanancin tausayin Khamis. Ya ga jinya ta ajali iri-iri a gabanshi amma bai taɓa ganin irin ta Khamis ba, ace mutum ba gobara yayi ba ba komai ya faru da shi ba lokaci ɗaya fuskarsa da fatar jikinsa gaba ɗaya suyi baƙi-ƙirin kamar wanda yayi gobara? Lallai mai rai ya shiga uku, idan bawa bai ji tsoron Allah a duniya ya aikata aiki na ƙwarai ba tabbas sadda Allah ya tashi damƙarsa cikin ƙanƙanin lokaci zai gane kurensa.

Dubi Khamis dai, a lokaci ɗaya an sauya halittarsa kamar ba shi ne ingarman lafiyayyen matashinnan mai ji da gayu da ƙuruciya ba. Babu abinda yake tunawa sai sadda suka zo karɓar takardar sakin Ziyada irin fitsara da rainin da Khamis ɗin yai ta zuba musu, yana jaddada duk duniya bai ga uban da ya isa yasa ya saki matarsa ba.

Wai yau shi ne haka kwance cikin wani irin yanayi da munin halitta abin tsoro ga al’umma, su kansu in banda ya zama dole su tsaya a gurinshi da babu abinda zai tsayar da su a cikin ɗakin.

A tausashe ya fara magana ga Ziyada,
“Kiyi haƙuri. Allah yana tare da masu haƙuri. Ki yafe mishi don girman Allah da darajar fiyayyen halitta SAW…”

Cikin kuka ta katse shi da rawar murya tana cewa
“Yaya… Khamis ya cutar da ni da ƴaƴana… Ko ka san Nauwara ta yi gadon mummunan hali irin nashi…?”

“Ai don Allah na ce ki yafe mishi.”

Ya katse ta tun kafin ta ƙarasa maganar da take yi.

“Ba don halinshi ba za ki yafe mishi ba Ziyada.”

Ya sake faɗa mata a tausashe.

“Ki yafe mishi ko ke ma kya rabauta da gwaggwaɓar ladan da Allah yayi tanadi ga masu yafiya a lokacin da suke da ikon ɗaukar fansa kan zaluncin da aka yi musu.”

“Na yafe mishi Yaya.”

Ta faɗa da sauri har lokacin hawayen da take yi basu tsaya da sauka ba.

“Na yafe mishi ba don halinshi ba kamar yadda ka ce. Na yafe mishi ne kawai Don Allah da darajar fiyayyen halitta SAW… Khamis Allah ya baka lafiya.”

Tana gama faɗin haka ta fice daga ɗakin da sauri idanunta na tsiyayar da hawaye masu azabar zafi da ƙuna.

*****

Duk da yadda ta shiga cikin matsanancin firgici da tsoron ganin yanayin da ya koma a lokaci kaɗan. Zuciyarta tayi bala’in ƙeƙashewar da take ji inda za ta ganshi a cikin halin da yafi wannan muni baza ta iya yafe mishi ba.

Babu irin tunanin da take yi sai yadda Khamis ɗin yayi ta wala-gigi da rayuwarta kamar ƙwallon wasa a hannun ƙaramin yaro. In banda tsarewa da kiyayewa ta Ubangiji da yanzu tana gidan mahaukata a ɗaure, duk da bata yi babbar hauka ba. Ta yi ɗan ƙaramin haukan da sai da ta kwashe shekara biyu cif tana karɓar magani a asibitin mahaukata da ke Barnawa Kaduna.

Da taimakon ƙarfafan magunguna da irin gwanayen matan da suka dinga tafi da ita da shawarwari suna nunar mata abinda ya faru da ita ba shi ne ƙarshen rayuwarta ba, haɗe da addu’ar iyaye, ƴan’uwa, maluma mabanbanta Allah yasa ta yakice komai daga ranta ta fara sabuwar rayuwa.

Kuma cikin hukuncin Allah sai ya haɗa ta da nagartaccen malamin da ya cigaba da jan gorar rayuwarta a ɓangaren karatunta har zuwa lokacin da sannu a hankali yai ta tafiya da ita cikin hikima da ƙwarewa har zuwa yanzu da ya zama bango abin jinginarta. Masoyinta, mijinta, uban ƴaƴa biyu da Allah ya bata.

Tayi gabas, ya sha gabanta, ta juya yamma, ya sake shan gabanta, za ta juya kudu yayi saurin riƙo ta da sauri ya haɗa ta da ƙirjinsa ya ruƙunƙumeta da ƙarfi.

Ya buɗe baki zaiyi magana kamar ta sani tayi saurin katse shi da cewa,

“Umarni kake bani Malamina?”

“Ba umarni bane ɗalibata.”

Ya faɗa da muryarsa a sanyaye.

“Shawara ce nake baki da kuma kwaɗayin da nake miki na samun ladar da ke cikin yafiya ga duk wanda aka zalunta…”

“Idan ban yafe masa ba, zunubi za’a rubuta min?”

Ta katse shi tun kafin ya rufe bakinsa.

Izuwa yanzu ya kasa magana, sai kai ya girgiza mata alamar a’a.

A hankali ta cire kanta daga ƙirjinsa, ta riƙe hannayensa biyu ta ja shi suka zauna akan kujera mazaunin mutum uku da yake cikin ƙayataccen Ofis ɗin.

“Tsakanina da Allah, ko da na furta na yafe mishi abu ne da ko kusa da maƙogwaro na bai kai ba balle ya ƙarasa cikin zuciyata. A ranar da aka kawo shi, na danni zuciyata na bashi dukkan kulawa saboda kai ne da girman Allah da ka haɗa ni da shi.

Amma kalmar yafiya tsakanina da Khamis abu ne da bazai taɓa giftawa ba har gaban abada. Duk da na san nima mai laifi ce, amma Khamis yayi min zaluncin da bazan taɓa iya yafe mishi ba. Na fi so ni da shi mu haɗu gaban Allah ayi mana hisabi… Kayi haƙuri Malamina.”

Daga haka bata ƙara cewa komai ba ta miƙe tsam! Ta shige banɗaki don ma kar ya ƙara tsare ta da wasu maganganun da ko kaɗan bata ji a ranta za suyi tasiri a gare ta ba.

‘Khamis? Ai ni da kai sai a lahira ma haɗu ayi duk wacce za’ayi a gaban maƙaginmu da ya haramta zalunci a tsakanin bayinsa.’

Ta faɗa a zuciyarta sannan ta shige banɗaki.

******

Ashe da gaske ne da malamai suke cewa idan bawa yazo gargarar mutuwa, duk irin munanan abubuwan da ya aikata a cikin rayuwarsa haka zai ta ganin komai suna gittawa a cikin idanunsa kamar an kunna faifan bidiyo?

Khamis bai yarda da haka ba sai yanzu da shi da kansa ya tabbatar Lokacinsa ya zo ƙarshe a duniya. LOKACIN da yai ta shan alwashin tun kafin ya zo zai tuba ya daina aikata duk munanan ayyukan da yake aikatawa. LOKACIN da ko a mugun mafarki bai taɓa hangen zuwanshi a yanzu, a wannan ɗan ƙarataccen LOKACIN da suka rage mishi ba. Ashe haka rayuwa take? bawa yana tsaka da jin daɗin rayuwarsa idan ajali ya kusanto duniyar za ta juya mishi kamar juyin waina a tanda?

Da fari kamar a cikin mafarki al’amarin ya fara zuwar mishi… ko da ya buɗe idanunsa a firgice Ummansa ne ya gani da Rufaida tsaye a kansa sanye da fararen kaya, fuskokinsu sunyi jajur, a hannayensu riƙe da wani masaki da bai san ko me ke ciki ba.

A tsorace ya buɗe baki zai yi ma Yaya da ke barci akan darduma kawai sai suka kwara mishi abinda ke cikin masakin hannayensu, sai a lokacin kuma yaga ashe wuta ne a cikin masakin suka kwara mishi a jikinshi. Kafin ƙiftawa da bismilla kuma sai suka ɓace ɓat.

A karo na biyu ya buɗe baki zai kwara ihu saboda wani azaban raɗaɗi da zafi da ya game jikinsa lokaci guda amma sai yaji muryarsa ba ta fita sam. Ga shi dai ihu yake yi, amma shi kaɗai yake jin kayansa.

Haka yai ta juyi yana birgima akan gadon wuta tana cin jikinsa kaɗai ba tare da ta kama gadon ko kayan ɗakin ba har sai da ya ƙone gaba ɗaya jikinsa. Sannan wutan ta mutu murusa, sai matsanancin azabar da jikinsa ya ɗauka kamar wanda aka sheƙa ma ruwan dalma. A lokacin ne kuma muryarsa ta fara fita yana ihun kuka ƙasa ƙasa, sai ga shigowar Kawunnanshi da Inna Rabi suka tarar da shi a wannan mummunan halin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 63Lokaci 65 >>

1 thought on “Lokaci 64”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×