Skip to content
Part 65 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Kalmar yafiya ga ruhin da ta kasance azzaluma, ko ɗan yaya ne idan aka samu yafiyar gun ɗaya daga cikin waɗanda aka zalunta kuma aka yi yafiyar da zuciya ɗaya to tabbas za’a samu ɗan sassauci a ƙunci da azabar da ake ciki.

Kamar haka ne yafiyar Ziyada ta kasance ga Khamis, ya ɗan samu sauƙin azabar da yake ji a jikinsa, ihu da gurnanin da yake yi ya daina. Amma fa duk yadda ƴan’uwa da ƴaƴansa suka so ya karɓi kalmar Shahadar da suke biya masa Allah bai bashi iko ba.

A haka dai, yai ta gurmususu yana juyi da furta wasu irin sambatu waɗanda sam ba sa gane abinda yake cewa saboda harshenshi ya karye. Ga tsananin azaba da raɗaɗin fitar rai wanda ko ga ruhin da ta kasance saliha fiyayyen halitta SAW ya ce
“Haƙiƙa mutuwa tana da magagi.”

Tun da Babban Yaya yaga yanayin jikin Khamis ya fice daga ɗakin yana matsar ƙwallah ba tare da ya iya musu sallama ba. Gaba ɗaya tsoro da firgicin rayuwa ya gama cika shi, a fili yake addu’ar Allah yasa mu cika da imani.

Gaba ɗaya ƴan’uwan Khamis kuka suke yi kamar ransu zai fita, hatta Nauwara da take waje ta shiga cikin ɗakin saboda irin sautin kuka da salati da salallamin da ta ji yana tashi a cikin ɗakin.

Mannirah tun tana iya karatu kasawa tayi, a ƙarshe ficewa tayi tana rangaji ta kira likitoci amma ko da suka zo sun kasa yi mishi komai, su da kansu sun tabbatar lallai Khamis ya zo gargara. Ficewa suka yi a ɗakin da cewar za su ɗauko wata allura da za suyi masa basu sake komawa cikin ɗakin ba.

Yaya Yusuf ne ya cigaba da nanata ma Khamis kalmar shahada ƴan’uwa da ƴaƴa na taya shi amma sam Khamis ya kasa karɓa, Har zuwa lokacin da suna ji suna gani ba tare da sun iya yin komai ba mala’ikan mutuwa ya zare ransa daga gangar jikinsa.

(Duniya zancen banza. Kai/ke bawa mai rayuwa ka/ki tuba, ka/ki roƙi Allah yafiyar zunubanka/ki tun kafin LOKACI ya ƙure mana. Allah yasa muyi kyakkyawan ƙarshe.)

******

“Mumcy ko? Ni na kashe ta da hannuna. Wuƙa na ɗauka na caka mata a ƙahon zuciyarta. Ƙarshen da ya dace da maciya amana kenan. Shi kanshi Ikky in banda ƴan sanda sun iso kafin in gama ɓalle ƙofar banɗakin da yake ciki na rantse da Allah babu abinda zai hana in farke cikinsa. Saboda Allah duk irin halaccin da nayi masa irin mummunan sakayyar cin amanar da zai min kenan?”

Da ta zo nan a maganganunta sai ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka mai cin rai.

Maganganun da Amina take yi tana ƙara nanatawa kenan duk in da aka shiga da ita. Kamar dai wacce notocin kanta suka fara kwancewa.

Ko da lauyan da Yayyinta suka ɗauka mata ya nemi fakewa da maganar tana da taɓin ƙwaƙwalwa, ya kuma ƙara da neman alfarmar a basu damar kai ta asibiti don binciken likitoci su tabbatar da maganarsa.

Wani ikon Allah shi ne duk yadda likitoci suka kai da binciken ƙwaƙwaf akan ƙwaƙwalwarta lafiya ƙalau take. Da alamun dai hakkin rai ke bibiyarta. Ƙwaƙwalwarta lafiya ƙalau kuma bata daina sambatu tana faɗin abinda ta aikata haɗe da tona asirin irin yawon ta zubar ɗin da ta daɗe tana yi.

Wannan shi ne abinda ya sauƙaƙa shari’ar, duk tambayoyin da lauyan gwamnati yayi mata akan alaƙarta da Mumcy da Ikhlas zallar gaskiyar magana take faɗa babu ɓoye-ɓoye.

Iyaye da ƴan’uwanta maza sunyi kuka kamar ba gobe. Duk yadda suka so suyi amfani da manyan lauyoyi wajen kuɓutar da ita abun ya gagara. A dole suna ji suna gani za su bar shari’a tayi aiki da gaskiya, wanda ko sun ƙi ko sun so sun san abinda zai biyo baya bazai taɓa yi ma zukatansu daɗi ba.

Aka ce da-na sani ƙeya, Iyayenta sai a lokacin suke matuƙar da-na sanin yadda suka yi wasa-rere da tarbiyarta, ba ma ita kaɗai ba, har sauran ƴan’uwanta maza. Waɗanda tsarewa da kiyayewar Ubangiji kaɗai ita tasa tarbiyarsu saisaituwa, ba don dagewa ko tsayuwar iyaye a kansu ba.

Ga shi yanzu ido rufe suke so suyi gyara akan kuskurensu amma LOKACI ya ƙure musu, lokacin da tunda ya tafi ya tafi kenan, ba su da halin su dawo da hannun agogo baya. Allah ya tsare mu da aikin da-na sani.

Bayan Shekaru Uku

“To shi kenan ƙawata, sai anjima. Ki isar min da gaisuwa gurin angonki.”

A hankali Sameera ta saki dariya a tausashe jin abinda Rahma take cewa ta cikin wayar da suke yi.

“Haba dai, wane irin ango kuma ana zaune ƙalau? Mun fara tsufa a gidan miji fa, ko kin manta sati biyu da suka wuce muka yi walimar cika shekaru uku da aure?”

“Kin san Allah? Ni a guri na kullum kallon sabbin auren sati biyu nake muku. Kin san dalili?”

Kafin Samirar ta amsa ta cigaba da cewa
“Kullum idan aka kawo miki ziyara ba kunya ko kara amarci kuke ci babu kama hannun yaro.”

A karo na biyu Samira ta sake ƙyalƙyalewa da dariya jin maganar da Aminiyar tata take yi. Amma sanin gaskiya take faɗa yasa bata wani yi ƙoƙarin kare kanta ba, sai cewa tayi cikin dariya.

“Ke dai kika sani Rahma. Ni dai yanzu sai anjima. Yi maza ki sallami babyna da ke tsala kuka. Wai har yanzu ba’a gama wankan bane? Wa ke kuka cikin su biyun?”

“Waye kuwa idan ba Sajid ba? Ai shi ne sarkin rigima ke ma kin sani, don Sayyid sam ba shi da irin waɗannan ƙananun rigin-gimun.”

“Allah ya raya mana su yayi musu albarka. Lokaci ne, zai daina a hankali. Yanzu dai bari in barki ki kula min da ƴaƴana, sai na shigo goben.”

Suka yi sallama tare da kashe wayar gaba ɗayansu.

A ɓangaren Samira, Jikinta sanyaye ta ajiye wayar ƙirar Samsung mai matsakacin kuɗi akan cinyarta. Sana’o’in turarukan wuta da humra da take yi wanda da taimakon Ummanta da maigidanta da Rahma suka haɗa mata jarin sun matuƙar karɓarta, ciniki take yi ba ɗan kaɗan ba. Don ma dai ba ta yarda ta riƙe maƙudan kuɗaɗe a hannunta da sun fara yawa sosai take yakice wani abu ta damƙa ma Ummanta da Maigidanta.

Sannu a hankali daga zaman shiru ta nutsa a duniyar tunani. Shekarunsu uku da ƴan kwanaki kenan da yin aure amma har zuwa yanzu Allah bai kawo rabo ba. A taƙaice ma ko ɓatan wata bata taɓa yi ba.

Rahma da ya kasance tazarar aurensu bai fi watanni shidda ba har ta yi haihuwa na biyu, na farko ta haifi baby boy yanzu ga shi ta sake haihuwar ƴaƴa biyu duka maza.

Bata taɓa sanin tana da son yara ba sai bayan aurenta, i zuwa yanzu Allah kaɗai Yasan iyaka asibitoci da likitocin da taje ta gani game da matsalar rashin haihuwa. Duka dai abu ɗaya suke faɗa mata kamar haɗin baki.

“Sakamakon bare-baren ciki da ta dinga yi a baya da kuma magunguna na hana ɗaukar ciki da ta dinga sha mahaifarta tayi raunin da ba lallai ta iya ɗaukar ciki ba. Tayi wankin cikin, anyi na mahaifa, magunguna iri-iri babu waɗanda bata sha, har dai daga baya ta koma gefe ta zubawa sarautar Allah idanu ta cigaba da addu’a.

Tana tsananin son ta ga ta haifi yara ita ma, gaba daya hankalinta da roƙo da fatanta ya ɗunguma ne kacokam kan Allah ya bata haihuwa ko ƙwara biyu ne.

Tana kuma son ta samawa Isiya ‘abokai’ kamar yadda yake faɗa mata lokacin da tana amarya. Shi yasa idan ta kalle shi ta kuma tuna har yanzu ta gaza zamowa cika-makin farin cikinshi sai ta ji hankalinta ya ƙara ɗugunzuma.

Ta kula sarai a yanzu sam bai cika son yi mata zancen ‘ya’ya ba saboda da yadda ta damu da son haihuwa. Shi yasa ya ke ta kokarin tausarta da nuna mata hakan bai dame shi ba, amma ita ta san ya damu.

Don ma dai Allah ya dube ta ya haɗata da dangin miji da surukai na kwarai, waɗanda basu cika tura kai cikin sha’anin rayuwar aurensu ba ai da ta shiga uku.

Nisan da tayi cikin tunani yasa bata ma ji lokacin da Isiya ya shigo gidan ba. Sai da ta ji ana shafa gadon bayanta a hankali. Tayi firgigit ta zabura tana kallonshi, kafin ta saki ajiyar zuciya a hankali tana mai sakar mishi murmushi a tausashe.

“Habibina barka da dawowa, Afuwan! ban ji shigowarka ba.”

Da martanin murmushi a fuskarsa ya zauna a kusa da ita har cinyarsu na gogan juna.
“Dama ta yaya za ki ji shigowata kina ta fama da tunani? Ba na hana ki waɗannan tunane-tunanen da sam ba su da amfani ba?

Tatsuniyar gizo dai bata wuce ta ƙoƙi, nasan duk akan damuwar rashin haihuwa ne. Ni kuma ina yawan tunatar dake, idan kika yi hakuri kika bari Allah yayi ikon shi, sai ki ga watarana hakan ya zama labari. Ma’aurata nawa ne suka yi aure shekaru fiye da goma ko fi basu samu haihuwa ba amma kuma da suka sallamawa Allah, kiga sun zo sun haihu sadda basu taɓa tsammani ba? Ni wallahi ko zamu ƙare rayuwarmu bamu haihu ba, ba zan taɓa damuwa ba. Saboda ke ɗin kin ishe ni.”

Tayi murmushi a sanyaye tana jinjina kai,
“Haka ne mijina, kayi hakuri don Allah. Wasu lokutan na kan manta da hakan, amma zan dinga tunawa da nasihunka in Allah ya yarda.”

Yayi murmushi
“Yauwa matata, haka nake son ji. Yanzu dai je ki ɗauko min abincina. Idan na ci sai ki ɗauko mayafinki mu fita. Gwanda muje can gida wajen Umma ki ƙarasa yini na san zaki fi warwarewa. In yaso idan na taso daga kasuwa da dare sai in biyo in ɗaukeki!”

Cike da doki da jindadi ta rungume shi sannan ta sumbace shi a laɓɓansa. Ta miƙe tsaye tana rausaya da rangaji kamar reshen bishiya a lokacin iskar damina shi kuma ya bi ta da kallon burgewa da matsanancin soyayyarta har ta shige kicin ɗin su.

Ba tare da ɓata lokaci ba ta shirya mishi fried rice da taji nama da hanta, a gefe guda kuma ga sassanyar lemun abarba da kwakwa da ta haɗa da hannunta.

Ko da ta zuba mishi abincin, bata barshi a zaune shi kaɗai ba. Ciyar da shi ta fara yi sannu a hankali tana ba shu lemun har sai da ita da kanta ta gamsu ya ƙoshi.

Alhamdulillahi! Suna cikin rufin asiri da buɗin rayuwa, basa tare da wata matsala ta azo a gani, Isiya mutum ne mai kokarin kawar da kai akan abubuwa da laifuka da za ta aikata a gare shi. Idan ma abun bacin rai tayi mishi, ya kan zaunar da ita ne a nutse ya fada mata cikin hikima da iya magana. A haka sai su fahimci juna ta kuma bashi hakuri. Itama kuma sai take kokarin yin koyi da shi a hakan.

Ta kauda kayan abincin, taje ta zura doguwar hijabi akan kayan jikinta ta ɗora da nikabi da safa. Kafin ta fito har ya karkashe kayan wuta ya kulle ko’ina, don haka ta rufe ɗakin ta bi bayanshi suka fita bayan sun rufe ƙofar ɓangarensu.

Har sasan iyayen mijinta suka shiga tayi musu sallama sannan suka fita ta haye bayan mashin ɗinshi yaja suka tafi gidan Ummanta.

******

Matashiya Mannirah Khamis Abubakar ce ta fito daga dakin daukar karatu dake cikin jami’ar Taibah University da ke Madina. Tafiya take yi a nutse, cikin shiga ta mutunci da ta saje da yawancin ƴan matan da ke kara-kaina a cikin makarantar.

Abaya ce a jikinta ruwan ƙasa, tayi rolling da dankwalin Abayar mai dan fadi, sai ta sanya takalmin sneakers a kafarta shi ma ruwan kasa.
Jakar goyo ce rataye a bayanta irinta dalibai da ke dauke da littafan karatunta a ciki. Ta sanya gilashin ido fari a fuskarta wanda ke taimaka mata wajen karatu.

Kallo daya zaka yi mata ka san cewa kaga mace wadda tasan nutsuwa da kuma mutuncin kanta. Ƙaramin earpiece ne makale a kunnenta tana waya da yar’uwarta Nauwara, lokacin da take kokarin saduwa da wajen cin abinci domin ta ci abinci kafin ta wuce wajen karatunta na gaba.

Lallausan murmushi take saki akai-akai tana sauraren yadda Nauwara ke mata ƙorafin maigidanta Alhaji Sanusi ya hana ta ci gaba da karatu bayan kuma shi da kanshi ya yarda da hakan kafin ta aure shi.

A yanzu da gaske so take yi ta ci gaba da karatun amma ya hana ta. Ya ce duk wasu bukatanta zai sauke mata su kar ta damu. Amma shi gidanshi babu zancen karatu balle aiki, gara ma tayi haƙuri.

A tausashe Mannirah take ba ta hakuri da kara tausarta da kalamai masu sanyaya rai tana nunar mata ai zaman auren shi ne gaba da karatun. Tunda dai ya hana ta haƙura shi zai fi alkhairi.

‘Tun bayan rasuwar Khamis, bayan irin gaggarumin tashin hankali da iyalan suka shiga sannu a hankali Ubangiji ya saka musu dangana. Nauwara ta cigaba da Istibra’i har ta gama a sirrance ba tare da sanin jama’a da yawa ba.

Abba Yusuf ya haɗa aurensu da wani abokinshi Alhaji Sanusi bayan shi da kanshi ya nuna sha’awar aurenta tun lokacin rasuwar Khamis da aka kira ƴaƴanshi suyi musu gaisuwa da nasiha.

Ɗan kasuwa ne mai rufin asiri, yana da matarshi ɗaya da ‘ya’yansu hudu. Tun kafin auren ya jaddada ma Abba Yusuf lallai zai riƙe Nauwara cikin amana da ƙauna haɗe da soyayya. Kuma Alhamdulillah yana iyakar ƙoƙarinshi.

Shekaru kusan biyu da auren na su amma har yanzu yana tattalinta da kulawa da ita kamar satin da ya wuce suka yi aure. Kowacce mata gidanta daban, yana kuma iyaka bakin kokarinshi wajen ganin ya kwatanta adalci a tsakaninsu.

Kuma itama Nauwara sai akai dace ta rike shi da iyalanshi hannu bibiyu. Dama babban burinta rayuwace ta gayu da fantamawa kuma ya tsaye mata daidai gwargwado, don a yanzu haka zancen zai saya mata mota ake yi toshiyar bakin hana ta karatu da yayi.

Ba a jima da yin auren Nawwara ba Mannirah ta gama makaranta. Cikin ikon Allah ta samu admission a jami’ar Al-Azhar inda tayi applying.

Da farko Yaya Yusuf ya so ya hana ta, a cewarsa rayuwar gaba ɗaya tsoro take ba shi. Gara tayi aurenta kawai a wuce gurin.

Amma da ta dage kuma ta nuna mishi ita sam ba auren take so ba a yanzu, ita mazan ma gaba-daya tsoronsu take yi.

Hankalinshi dai bai nutsa da tafiyar tata ba sai da ta mishi alkawarin duk lokacin da yaga damar aurar da ita da duk wanda yake ganin ya dace da ita, in dai zai barta ta karasa karatun ‘Islamic Law’ da take yi to za ta amince ba ja’inja.’

Zancen da take yiwa Nawwara kenan yanzu da ta zauna a cikin wajen cin abincin tayi odar bakin shayi da gurasa da zuma.
Fada mata take yi yadda jiya da dare Yaya Yusuf ya kira ta. Bayan sun gaisa sai yake tambayarta.

“Kin tuna alƙawarin da kika yi min lokacin da zaki taho makaranta Mannirah?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 64Lokaci 66 >>

3 thoughts on “Lokaci 65”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×