"Khamis ka cuci rayuwata, Allah ya isa tsakanina da kai."
Tayi maganar a fili cikin kuka. Ɓacin rai da baƙin cikin irin mummunan gadon da Nauwara tayi na halin Khamis yasa hankalin Ziyada gushewa, tayi ta ja mishi tsinuwa da munanan alkaba'irai iri-iri. In da Allah ya taimaketa shi ne tana fita daga gidan bata daɗe tana tafiya ba ta samu mai adaidaita sahu. Da babu shakka kallon taɓaɓɓiya a cikin sababbin kaya za'a dinga yi mata.
Da ƙyar ta iya ɗaga ma mai keken hannu ba tare da ta faɗa mishi. . .
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun
Allah kasa muyi kyakykyawan karshe ka rabamu da mugun ji da mugun gani