Skip to content
Part 8 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Duk da neman yafiyarsu da Ziyada tayi. Ta kuma ɗauki alƙawari har da rantsuwarta kan cewa baza ta sake kula al’amarin Khamis ba.

Ummanmu bata ji a zuciyarta al’amarin zai kwaranye cikin sauƙi kamar haka ba. A ɗazu bayan ta idar da sallah ta yanke ma kanta wani mataki da take ganin ƙila, idan ta aiwatar ta samu sauƙin al’amarin. Idan da rabo ma komai sai ya wuce kamar ba’a yi ba.

Ana idar da sallar isha’i ta saka babban mayafi tayi sallama da ƴaƴanta kan cewa za ta shiga maƙwafta. A dawo lafiya suka yi mata sannan ta fice daga gidan.

Tana fita bata zame a ko ina ba sai gidansu Khamis. Cikin sa’a kamar yadda tai ta fatan ya kasance ta tarar da ahalin gidan gaba ɗaya suna nan, suna zaune a falo kan teburin cin abinci.

Ko da aka yi mata tayi da ɗan murmushi a fuskarta ta ce Alhamdulillahi. Alhaji Abubakar, Yusuf, Khamis har sun miƙe za su bata guri da tunanin ko gurin Hajiyarsu ta zo ta dakatar da su ta hanyar cewa
“Alhaji Bismillah! Ai zuwan nawa tafiyayya ce gare ku gaba ɗaya. Ina fatan ban shiga cikin lokacinku ba.”

“A’a babu damuwa Hajiya. Allah yasa dai lafiya.”
Ya ambata fuskarsa na ɗan nuna yanayin mamaki.

Kan kujerun falon suka zauna, sai ƴaƴan suka zauna a ƙasa kusa da ƙafafun uban. Sabon gaisuwa aka ƙara sabuntawa a tsakaninsu Hajiya Hauwa ta tambayi lafiyar yaranta ta amsa da lafiyarsu ƙalau. Ummanmu ta ɗan gyara zama da fuska kadaran-kadahan ta fara magana kan ainahin abinda ya shigo da ita a daidai wannan lokacin.
“Hajiya ya muka ji da firgicin wannan magana da yara suka tunkaro mu da ita…”

“Wace magana kenan kike magana akai Hajiya Khadija? Mu magana ai tuntuni ta mutu a gurinmu. Yara duk su biyun ƙananu ne, aure tsakaninsu abu ne da bazai taɓa yiwuwa a wannan lokacin ba.”
Hajiya Hauwa ta faɗi maganganun da wani irin ɗaurewar fuska.

Da Alhaji Abubakar mahaifinsu Khamis da Hajiya Khadija a tare suka bi Hajiya Hauwa da wani irin kallo. Ita kuwa ko a jikinta ta ƙare haɗe girar sama da ƙasa tayi murtuk, sai karkaɗa ƙafa take yi. Ita fa zance in dai za’a biyo ta kan laifin ƴaƴanta musamman shalelen zuciyarta Khamis to sam babu sulhu babu ɗaga ƙafa.

Ko shi ne ba shi da gaskiya takan rufe ido tayi ma ƙaryarsa kwaskwarimar da dole a zuba mata idanu ba tare da anja dogon zance ko kuma a ɗauki mataki akan yaron ba.

Shi kanshi Alhaji Abubakar ba ya iya wani kataɓus! Shi da ita ɗin zamu ce ta tadda muje mu, shi ma mutum ne mai bala’in son yara da kawar da idanu a mafiyawa daga cikin ƙananun abubuwan da ya kamata ace an kwaɓa musu.

Amma shi kasancewarsa namiji da ya fi mace hangen nesa sai ba’a gane son ƴaƴan nashi ƙarara a fili kamar na matarsa. Ko yanzu ma da mamaki a fuskarsa ya ce
“Me kike yi haka Hajiya? Ki nutsu mana don Allah.”
Sai kuma ya mayar da hankalinsa kan Hajiya Khadija, ɗan taƙaitacen murmushi ya sakar mata.

Yana girmama matar, yana ganin mutuncinta Sosai dattaku da kamewarta ke burgeshi tun da daɗewa. In banda zaga-zagan ƴan mata da suke gabanta da bazai iya riƙe mata ba da tuni ya sa kanshi cikin zawarawa.
“Hajiya ki kwantar da hankalinki. Lamarin duk bai kai yadda za’a ɗaga hankali ko a jefa kai cikin damuwa ba. Ni da mahaifiyar Khamis mun zauna mun yanke shawara aurensu a yanzu da waɗannan ƙananun shekarun bazai yiwu ba. Mun faɗa ma Khamis, ya fahimce mu, har ma yayi mana alƙawarin janyewa gaba ɗaya daga lamarinta.

Itama yarinyar sai ki sanar mata da haka. Ta kawar da komai daga zuciyarta. Su ajiye wani gigin soyayyar ƙuruciya a gefe su fuskanci hidimar karatunsu. Shi Khamis ko jiya ya tabbatar mana da ya ma manta da yarinyar…”

“Ya manta da ita? Ya manta da ita shi ne yake ta bibiyar al’amarinta yana zuga ta ta bijire ma umarnin iyayenta?”
Hajiya Khadija ta katse shi da faɗin haka cikin zafin rai, idanunta na kan Khamis da yake kallonta ido cikin ido.

Kafin ɗaya daga cikin iyayen yayi magana ta cigaba da cewa
“Alhaji, don Allah ka fahimce ni. Banzo gidannan ba sai da na samu tabbaci har yanzu Khamis bai ƙyale Ziyada ba. Ni maganar da ta kawo ni ɗaya ce zuwa biyu.

Khamis ya bi ta hanyoyi mabanbanta tsakanin ƙarya da gaskiya ya gama kame zuciyar Ziyadah, sai abinda yake so kuma ya ce tayi shi take aikatawa. Shin za ku aurar da shi yanzu ne?”

“Allah ya kiyaye. Duka-duka nawa Auta yake da zanyi mishi aure a waɗannan ƙananun shekarun? Kuma ko auren zan mishi ma ai bazan nemo yarinyar da suke shekaru ɗaya in aura mishi ba.”
Hajiya Hauwa ta jero maganganun da fushi sosai a fuskarta.

Tattare girar sama da ƙasa Hajiya Khadija tayi ta ɗaure fuska sosai. A kallonta kawai za’a fahimci matuƙar ta buɗe baki tabbas mai daɗi baza ta taɓa fitowa daga cikinta ba.

Fahimtar hakan da Alhaji Abubakar yayi yasa shi saurin cewa
“Hajiya, kiyi haƙuri don Allah. Khamis bamu shirya aurar da shi a yanzu ba. Ba kuma wai don Ziyadah bata kai ajin irin macen da muke so ya aura ba. Ki kwantar da hankalinki. Al’amuran duk mu miƙa shi ga mahaliccin sammai da ƙassai. Idan da rabon aure a tsakaninsu, can gaba za kiga sun sake haɗewa.

A yanzu kinga Khamis ko secondari ya ƙi ya mayar da hankali ya kammala. Mun gama yanke shawara ni da mahaifiyarsa makarantar kwana za mu kaishi, wataƙila acan zai fi nutsuwa ya mayar da hankali wajen karatu.”
Mahaifinsu Khamis ya faɗi haka ga Hajiya Khadija, muryarsa a tausashe.

Kafin Ummanmu tayi magana karaf Hajiya Hauwa ta ce
“To kin dai ji! Sai kije ki ja ma ƴarki kunne ta mayar da hankali kan abinda ke gabanta. Ba dai Khamis bane? To duk ku kwantar da hankalinku, za mu ɗauke shi daga unguwarnan don a daina ɗauko ko wace irin magana ana yaɓa mishi.”
Taja tsaki sannan ta tashi ta shige cikin ɗaki. Mazauna gurin duk suka bi ta da kallo.

Lallai ɗan kuka mai ja ma uwarsa jifa. Sunkuyar da kai Hajiya Khadija tayi idanunta suka yi ƙwalƙwal da hawaye. Sau biyu tana haɗiye miyau a jere ko za ta samu ta haɗiye wani malolon baƙin ciki da yayi mata tsaye a maƙoshi.

Kwarjinin Alh Abubakar shi ya hana ta buɗe baki ta yi ma Hajiya Hauwa wankin babban bargo. Ta tsani a mata magana da siga ta wulaƙanci da ƙasƙanci, ita fa shiyasa sam nata bai zo ɗaya da Hajiya Hauwa ba.

Haka ta bar gidan jikinta a saɓule, ba tare da ta samu abinda take so ba. Ita abinda ta so, ta ko wane ɓangare su iyayan su kafa ma ƴaƴan dokoki mai tsanani. Su ƙara saka musu idanu a gaban idonsu da bayan idanunsu, su dinga kula da shige da ficen yaran, sannan su haɗa da addu’a. Amma iyayen Khamis gaba ɗaya sun gaza fahimtarta, sai wani irin maganganu suke mata da jirwaye mai kamar wanka. A yadda suke nuna mata ma kamar dai Ziyadar ita ce ta maƙale ma Khamis, shi tuni ya manta da al’amarinta.

Tana kallon sa’adda za ta fita Khamis ya bi ta da wani irin kallo har ta fice daga falon. Tana hanya ta yi ƙwafa ya fi sau goma kafin ta ƙarasa gida.
“Ziyada, Ziyada, Ziyada.”
Tana shiga ta fara ƙwalla ma yarinyar kira tun daga bakin ƙofar falon.

A tsorace ƴaƴan gaba suka fito suna kallonta, idanunsu a warwaje, hankalinsu a tashe. Gadan-gadan ta nufi Ziyada fuskarta a ɗaure tamau, da saurin gaske Ziyada ta duƙe a ƙasa tare da saka kuka. Ta zaci rufe ta da duka za ta yi, ta san kuma in dai wani dukan za’a sake mata bai wuce kan Soyayyarta da Khamis ba.

Cikin kuka ta fara rantse-rantsen ta rabu da Khamis har abada. Ayi mata haƙuri, in Allah ya yarda baza ta sake ba. Don girman Allah kar a sake dukanta.

Hannunta na dama Ummanmu ta damƙo da ƙarfi ta ɗaga ta tsaye. Fuskarta a ɗaure tamau, ta kalli Ziyadar na tsawon daƙiƙu goma sha biyar. Sai kuma ta finciki hannunta da ƙarfi ta tura ta kan kujera.

Kafin ta taso Ummanmu ta sa ƙafarta guda ta tokare gaban kujerar. Idanunnan sun kaɗa sunyi ja sosai, da tsawa sosai a muryarta ta ce
“Ziyadah! Wacece ni a gurinki?”

“Mahaifiyata. Ke mahaifiyata ce. Ke kika haife ni.”
Ta amsa a tsorace, bakinta na rawa sosai. Idanunnan a warwaje, hawaye kaca-kaca da fuskarta.

“Da kyau! Ziyada umarni zanyi miki a matsayina na mahaifiyarki. Tunda dai kin tabbatar ni ce na haife ki, daga yau na haramta miki kula Khamis har abada. Kina ji na?”

“Na ji, na ji Ummanmu, Wallahi na ji. Zan kiyaye in Allah ya yard…”

“Kar ma ki kiyaye. Kar ki kiyaye kin ji ko Ziyada? Da yaddar Allah Wannan shi ne karo na ƙarshe da zanyi magana da ke kan umarni ko hani a lamarin Khamis. Na baki umarnin daina kula shi a karo na ƙarshe. Idan kika sake… Hmmmm! Zan barki da lamarinsa, amma duk abinda ya biyo bayan taraiyarku kar ki kuka da kowa ki kuka da kanki.”
Fuuuu ta wuce zuwa cikin ɗakinta a fusace.

Wani irin ɗaci take ji yana tasowa tun daga can ƙasan maƙogwaronta har zuwa kan harshenta. Duk yadda ta so riƙe kanta ta kasa, kan hannun kujera ta ɗora kanta ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka.

Da saurin gaske yayyen nata suka rufu a kanta suna rarrashinta. Basu yi gigin bin bayan Ummanmu ba, tayi fushi sosai. Idan tai irin wannan fushin kuma ta hana su dinga shiga harkarta, bayan ƙanƙanin lokaci ita da kanta za ta sakko, a lokacin ne suke da damar ba ta haƙuri kan laifin da aka yi mata.

Rarrashin Ziyada sukai tayi da tausasan kalamai har tayi shiru. Cikin hikima suka dinga nusar da ita irin ladan da ke cikin bin umarnin iyaye, musamman mahaifiya. A wannan lokacin ta ƙudurce a zuciyarta Khamis ko shi ne autan maza za tayi yaƙi da zuciyarta ta fatattaki soyayyarsa daga cikinta.


Bayan wata biyu kamar al’amuran sun canza. Khamis iyayenshi sun ɗauke shi daga unguwar kamar yadda suka faɗa ma Ummanmu. Lamarin da yasa hankalinta da na ƴaƴanta kwanciya kamar tsumma a randa.

Suka cigaba da al’amuransu cikin nutsuwa, kwanciyar hankali, farin ciki da walwala kamar yadda suka saba kafin ɓullowar zancen Khamis. Saboda Ziyada ta watsar da al’amarinshi gaba ɗaya, duk ƙwaƙwar mai saka ido babu wanda zai ganta ya ce akwai wata ɓoyayyiyar damuwa ko kaɗan a zuciyarta.

Wata ranar litinin tun da suka tashi gabatar da sallar asubah ta fara yi ma ƴan’uwanta ƙorafin sanyi take ji, kamar za tayi zazzaɓi. Da tausayawa suke mata sannu, Aunty Rukayya ta sirka mata ruwa mai ɗumi a buta wanda za tayi alwala. Bayannan suka bata rigar sanyi mai kauri sosai ta saka, tana idar da sallah ta koma ta kwanta ta lulluɓa da bargo. Wannan shi ya taimaka mata wajen rage ƙarfin sanyin da tayi ƙorafin tana ji.

Har ta fara barci lafiya kalau cikin hukuncin Allah sai jin sanyin ya dawo sosai har fiye da ɗazu. Lokaci ɗaya ta fara rawan ɗari, haƙoranta sai haɗuwa suke kaf-kaf. Daga nan kuma sai zazzaɓi mai zafi ya lulluɓeta.

Abu kamar wasa haka ta yini tana zazzaɓi. A nan cikin layinsu akwai wani likita da suke kira Dr. Nura, bayan kasancewarsa likita akwai babban chemist da ya buɗe a unguwar. Duk marasa lafiya na cikin layi shi suke fara tuntuɓa, kuma cikin hukuncin Allah a mafiyawancin lokuta ana samun dacewa, sai dai idan ciwon babba ne shi da kanshi yake bayar da shawarar a wuce asibiti.

Ko da zazzaɓin Ziyada ya ƙi sauka bayan ta sha paracemol zuwa ƙarfe goma na safe Hajiya Khadija ta kira shi a waya ta sanar da shi. Uzuri ya bata kan cewar yana asibiti, ya buƙaci ta haɗa shi da Ziyadar a waya, daƙyar ta iya daurewa ta faɗa mishi duk yanayin da take ji.

Katse wayar yayi bayan mintuna goma ya kira Ummanmu ya ce ta aika chemist ɗinshi a bada magani. Ya kira ya faɗa musu duk irin magungunan da za’a bayar, har da allura na kwana uku.

Bayan ta sha maganin ɗaya daga cikin yaran shagon yayi mata allura a madadin jikin ya sauka sai ya ƙara ɗumewa. Haka suka kwana suka sake yini tana cikin halin rashin lafiya.

“Ya jikinta? har yanzu zafin bai ragu ba?”
Ummanmu ta tambaya da yanayin damuwa sosai a fuskarta.

A hankali Aunty Karima ta yaye ƙaton bargon da Ziyada ta lulluɓa da shi. Ta ɗan saka tafin hannunta a wuyan Ziyada sai kuma da gaggawa ta ɗauke.
“Ummanmu zafinnan ƙara hauhawa fa yake yi. Wannan karon dai treatment ɗin Dr. Nura ba’a yi a sa’a ba. Ko dai za mu kaita asibiti?

Kin ga jiya haka aka kwana asa-asa, kar yazo yau ma a maimaita irin na jiya, duk da dai ba’a fatan haka.”

A kasalance Ummanmu ta shiga cikin ɗakin. Hijabin jikinta ta cire ta ɗora a gefen gadon Rukayya. Ta ƙarasa kusa da Ziyada itama tasa hannu ta taɓa gefen kafaɗarta.

“Wash! Wash Allah na… Ummanmu hannunki sanyi sosai kamar kin ciro a frig”
Ziyada ta faɗi haka da rawar murya sosai irinta wacce zazzaɓi yayi ma muguwar damƙa, a cikin yini biyu kacal.

Da sauri Ummanmu ta ɗauke hannunta tana yi mata sannu. Ta buɗe baki za tayi magana sai ga Aunty Rukayya ta shigo ɗakin da sallama a bakinta.

“Rukayya ya ake ciki? Kin sami Dr. Nura?”

“Eh! Ummanmu yana nan. Ga shi can a falo ya biyo ni don yaga yanayin jikin nata. Ya ce mu fita da ita, idan kuma baza ta iya ba sai ayi mishi izini ya shigo yaga o.”

Basu yi yunƙurin fita da ita ba saboda yanayin jikinta, gyara mata kwanciya suka yi, akwai hijabi a jikinta. Ruƙayya ta koma falo tayi mishi izinin ya shiga cikin ɗakin.

Bayan gwaje-gwaje da tambaye tambaye irin nasu na likitoci sai ya ɗebi jininta. Sannan ya maƙala mata ƙarin ruwa bayan yayi allurai a cikin ruwan. Da mamaki yake ta kallonta, ya san Ziyada ba sani na sama-sama ba. Irin canje-canjen da yake gani a tattare da ita ya ɗan bashi mamaki.
Cikin jakarsu ta likitoci ya adana jininta da ya ɗauka, domin fara share ma kanshi tantama sai ya ce mata
“Yaushe rabonki da ganin baƙonki na wata-wata?”

A tare ƙirjin uwar da yayyinta ya buga daram. Idanu warwaje suke kallon likitan, sai kuma su mayar da hankalinsu kan Ziyada da tayi shiru tana tunani.

“Wannan watan ne kawai ban gani ba. Amma da yake yana min canjin kwanaki wasu lokutan, sai ban ɗauki hakan a wani ciwo ba.”
Ta amsa kai tsaye bayan ta gama tunani.

“Dr. Kana tunanin wani abu ne? Ko akwai wata matsala?”
Ummanmu ta tambayeshi da rawar murya.

Kallonta yayi, sai kuma ya sakar mata murmushi.
“Babu komai fa Hajiya. Kawai dai na yi mata tambayar ne da tunanin ko bacterial infection ke damunta. Zan wuce yanzu, na ɗebi jininta, zuwa goma na safen gobe in Allah ya yarda sakamakon abinda ke damunta zai fito.”

Godiya mai auki Ummanmu tayi mishi, gaɓɓan jikinta a saɓule. Haka kawai ta tsinci kanta da mutuwar jiki tun daga jin tambayar da likita yayi ma Ziyada. Ko bayan fitarsa haka ta zauna ta zuba tagumi da hannu bibiyu, zuciyarta cike da wasu irin saƙe-saƙe mabanbanta.

Ita zuciya kullum umarni take da mummunan aiki. Da wannan hali irinna Zuciya haka tai ta saƙa ma Ummanmu mugayen tunanin da ko a mafarki ba ta fatan ganin faruwarsu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 7Lokaci 9 >>

1 thought on “Lokaci 8”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.