Skip to content
Part 9 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

A wannan dare, wani irin barci na raba da rabi ne ya dinga walagigi da Ummanmu. Da ta fara barci kamar wacce ake tayarwa sai ta farka a firgice, hankalinta a ɗugunzume. Har wannan lokaci tunanin tambayar da likita yayi ma autarta ya ƙi fita daga zuciyarta. Daga ƙarshe da ta tabbatar ko ta kwanta baza ta samu barci a mutunce ba. Sai ta miƙe tsam ta shige bayinta ta ɗauro alwala, ta shimfiɗa sallaya ta saka zumbulelen hijabin sallarta ta fuskanci gabas, ta fara kai kukanta ga mahaliccin sammai da ƙassai.

Sai gaf da kiran sallar asubahi nannauyan barci ya ɗauketa mai tafe da munanan mafarkai. Ko da ta farka ta jiƙe da gumi tayi kashirɓin, idanunta na sauka akan agogo taga ƙarfe biyar da minti hamsin na asubahi. Har an idar da sallah, bata samu gabatarwa akan lokaci ba, abinda baza ta iya tuna lokaci na ƙarshe da ya faru da ita ba.

Jikinta a saɓule kamar wacce aka naɗawa na jaki ta tashi daƙyar zuwa banɗaki. Zuciyarta cike da tunanin mafarkin da tayi, duk da kaso sittin cikin ɗari na mafarkin ta manta takamaimai abinda ya faru a ciki.

Tana idar da sallah Kareema da Rukayya suka yi sallama a ƙofar ɗakin. Sabo ne da suka yi tun suna ƙanana da sun idar da sallah za su leƙa su gaida iyayen.

“Ummanmu Alhamdulillah! Ziyada sauki ya fara samuwa, jiya cikin dare barci tayi cikin nutsuwa. Sau uku muna farkawa mu taɓa jikinta ko za muji zazzaɓi amma har yanzu sanyi ƙalau. Daƙyar ma muka tashe ta ta sallaci asubah saboda daɗin barci. Kuma ta tabbatar mana babu inda ke mata ciwo sai rashin ƙarfin jiki.”
Rukayya ta faɗi maganar da karaɗin murnar fara samun sauƙin ƴar’uwarsu a muryarta.

“Uhmmm!”
Ta faɗa da ƙyar! Gefe ta kawar da fuskarta. A sanyaye ta ƙara da cewa
“Allah ya ƙara lafiya.”

“Ummanmu? Me yake faruwa ne? Ko baki lafiya?”
Kareema tayi ta jera mata tambayoyin yanayin fuskarta na bayyana damuwa.

Shiru tayi. A madadin ta amsa ma sai ta ƙura ma guri ɗaya idanu, alamu na afkawa a cikin zuzzurfan tunani. Ga damuwa ƙarara suna karanta a fuskarta.

A ruɗe suka ƙara matsawa kusa da ita. Ɗan girgizata suka yi hankali tashe suke tambayarta abinda yake faruwa. Ko kusa basu yi tunanin ciwon ƴar’uwarsu bane matsalar. Tambayar da likita yayi ma Ziyada kuwa tun bayan amsar da ya ba Ummansu wacce su a gurinsu ta zama gamsasshiya watsar da damuwar da tambayar da haddasa musu a zuciya suka yi.

Ganin sunyi narai narai da idanu za suyi kuka yasa Ummanmu riƙo hannayensu.

“Kar ku damu! Ku kwantar da hankalinku. Wani mummunan mafarki nayi da ya ɗaga min hankali. Amma na yi addu’a, in sha Allahu ko menene ma zai zo da sauki. Auta idanu biyu kuka baro ta ita kaɗai ko barci take yi?”
Ta tambayesu don kore tashin hankalin da suka shiga.

Addu’o’i suka yi sosai kan mugun ji da mugun gani Allah ya tsare ya kare su da duk al’ummar musulmai. Sannan suka amsa mata da sun baro Ziyada idanunta biyu, amma tana kwance ne.

Bayansu ta bi zuwa ɗakinsu domin taga yanayin jikinta. Kamar yadda suka faɗa, sosai jikinta yayi sauƙi akan yadda ta yini jiya.

“Na ji sauƙi sosai Ummanmu. Yanzu kawai jikina ne babu ƙarfi. Sai kuma bakina da nake jin shi sam babu ɗanɗano, lokaci lokaci miyau bakina sai ya dinga tsinkewa. A yanzu babu abinda nake buƙata sai abu mai ɗan tsami ko me ɗah ɗaci.”
Ziyada ta faɗa hannunta na riƙe cikin na Ummanmu.

Tagumi tayi, da idanu biyu take ƙare ma Ziyada kallo. Sai a yanzu da tayi mata kallo na nutsuwa sai ta fahimci wasu baƙin canje-canje waɗanda sam babu su a tare da Ziyadar.

Cikin hikima ta aika Kareema ta fara gyaran gida. Ita kuma Rukayya ta shiga kicin fara harhaɗa abinda za’a karya da shi.

Bayan ficewarsu a hankali ta miƙe zuwa ƙofar ɗakin ta kulle, ta murza makulli. Ita dai Ziyada sai bin ta da kallo take yi, zuciyarta cike da mamakin abinda Ummanmu take yi.

Hijabin jikinta ta cire ta ajiye gefe ɗaya. Ta zauna kusa da ƙafafun Ziyada.
“Tashi muyi magana.”
Ta faɗa fuskarta babu walwala ko ƙanƙani.

Tun kafin ta ji maganar da za suyi jikinta yayi sanyi. Wani irin yanayi mai kama da na tsoro ya lulluɓeta. A kasalance ta miƙe zaune ta takure ƙafafunta cikin hijabi, ta duƙar da kanta ƙasa tana kallon kan katifarta.

“Ziyada, ɗago kanki ki kalleni”
Ummanmu ta bata umarni.

A hankali ta ɗaga kai ta kalleta, da wasu raunanan idanu, ciccike da ƙwallah.

Tsawon minti ɗaya Ummanmu ta ɗauka tana sauke nauyayan numfashi. Har wannan lokacin ƙirjinta bai daina bugawa ba, ko kaɗan ba ta so zuciyarta ta yarda da canje-canjen da take gani a tattare da Autarta. Ƙoƙarin dannar kanta take yi, domin a yadda take jin wani irin zafi a ranta za ta iya shaƙe Ziyadar idan tayi ƙoƙarin yi mata ƙarya.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, har lokacin bata ɗauke idanunta kan Ziyada ba ta fara magana a tausashe.
“A iya sanina da ɗan gajeren tunanina, a gidannan ina iyakar ƙoƙarina gurin kula da tarbiyarku. Kuma daidai gwargwado buƙatunku ina biya muku. A cikin rani, bazara, hunturu bana taɓa gazawa da neman kuɗi, faɗi tashi nake yi ta ko wane ɓangare, ba kuma don komai na ƙi hutar da kaina ba sai don kar in gaza wajen sauke nauyinku da ya rataya a wuyana. A tunanina a talakance dai ba na ƙaunar ku nemi abu ku rasa, balle har idanunku ya kai kan kayan wasu, ko kuma ku fara tunanin bin mummunar hanya don ku samu abinda kuke so. Tsakanina da ke babu ɓoye-ɓoye Ziyada, Bazan ɓoye miki ba tun jiya da likita yayi miki tambaya kan al’adarki hankalina ya gaza kwanciya. Ko barci raba da rabi nayi saboda tunani da fargabar abinda zai je yazo. Don Allah ki faɗa min, kar ki ce za ki ɓoye min wani abu Auta. Wa kika bari ya ratsa alfarmarki ta ɗiya mace?”

Tashin hankali!! Wanda ba’a saka masa rana ko lokaci. Wani irin firgici da tashin hankali Ziyada ta shiga lokaci ɗaya, irin tashin hankalin da tunda take a rayuwarta bata taɓa shiga cikinta ba. Hannayenta biyu ta ɗora akai, idanunta warwaje kamar wacce kura ya rutsa a dokar daji. Sau biyar tana buɗe baki da niyyar yin magana amma ta kasa cewa komai. A ƙarshe da ta rasa abin yi kawai sai ta fashe da wani irin ihun kuka kamar wacce ake yankawa.

Da mamaki matuƙa Ummanmu take kallonta, tun ɗazu take karantar yanayinta. Bata fahimci komai a ciki ba sai rashin gaskiya.
“Shhhhhhhh”
Ta faɗa haɗe da ɗora yatsarta manuniya a baki. Da ɓacin rai sosai a fuskarta ta ce
“Kuka na tambayeki kiyi min?”

A tsorace ta girgiza kai alamar a’a!

“Na dake ki ko na zage ki?”

Nan ma babu abinda ta iya yi sai girgiza kai.

“Ki buɗe baki ki amsa min tun kafin a jiyo kanmu da ke Ziyada. Tun muna mu biyu a cikin ɗakinnan kafin mu zama mu uku ko huɗu…”

“Ummanmu… Na rantse da Allah… kiyi haƙuri Ummanmu… Ba ni bace…”

Ƙwanƙwasa ƙofar da aka fara yi shi ya ɗauke hankalin Ummanmu daga sauraren kame-kamen da Ziyada take yi cikin kuka.

“Waye?”
Ummanmu ta tambaya da tsawa-tsawa a muryarta.

“Ummanmu ni ce Rukayya, daman Dr. Nura ne yazo. Wai yana son ganinki.”

Wani mugun kallo ta aika ma Ziyada, tayi ƙwafa. Sannan ta ɗauki hijabinta ta saka taje ta buɗe ƙofar.
“Yana ina?”

“Ga shi can a falo.”
Rukayya ta amsa tana sake kallon yadda idanun Ummanmu ya canza launi. Ga tunanin ihun kukan Ziyada da suka jiyo ba zato ba tsammani, ba tare da sun san laifin da tayi ba.

“Je ki ce mishi ya shigo.”
Ummanmu ta katse mata tunani sannan ta juya cikin ɗakin.

Kasancewar sun samu kyakkyawar tarbiya da horo na musulunci ko da ta shigar da likita cikin ɗakin da sassarfa ta fice, haɗe da ja musu ƙofa. Duk da zuciyarta cike take da tunanin abinda za’a tattauna a cikin ɗakin ko kaɗan bata yi tunanin laɓewa jikin ƙofar domin jin abinda zai faru a ciki ba. Aikinta ta cigaba da yi, a zuciyarta take addu’ar ko ma menene Allah ya sauƙaƙa musu.

“Hajiya? Me yake faruwa?”
Dr. Nura ya tambayeta ganin yadda ɓacin rai ya bayyana ƙarara a fuskarta.

Daƙyar ta iya sassauta fuskarta. Taja da baya zuwa gefen katifar Rukayya ta zauna.
“Lafiya kalau Dafta. Ya kwanan iyali?”

Sama-sama suka gaisa sannan ya ƙarasa kusa da Ziyada yana tambayar yanayin jikinta. Ganin tana hawaye sai abin ya ɗaure mishi kai, ya maida kallonshi kan Ummanmu, sai kuma ya dawo da idanu kan Ziyada ya ce
“Kukan na miye? Ko har yanzu jikin ne?”

“Dr. Ka je asibitin kuwa? Menene sakamakon gwajin jinin nata ya bayar?”
Ummanmu ta katse shi cikin zaƙuwa da gundura da yadda yake ta jan Ziyada da taɗi.

“Hajiya, na je asibiti tabbas! Na gwada jininta. Kuma na gano haƙiƙanin abinda yake damunta. Ko za ki ɗan bamu guri minti biyu inyi magana da ita…?”

“Babu inda zan tafi Dr. Magana ko ta mecece kayi a gabana. Ko ka manta ƴata ce ba ƴar riƙo ba? Duk abinda bincikenka ya bayar ka faɗa kawai, kar ka wani damu.”

Tun shigowarsa cikin ɗakin ya fahimci lallai Hajiya Khadeeja ranta a ɓace yake. Tattausa muryarsa yayi, ya fara da yi mata nasiha, haɗe da janyo mata ayoyin da ke nuni da falalar da bawa ke samu yayinda ya rungumi duk ƙaddarar da ta faɗo masa mai kyau ko akasinta…

“Dr., Ziyada ciki ne da ita ko?”
Ta katse shi da tambayar muryarta na ɗan rawa-rawa. Daga jin yadda yake ta ɗan waken zagaye ta san inda zancen nashi zai dire kenan. Don haka ta sauƙaƙa mishi ta hanyar tambayarsa abinda take da tabbacin abinda zai faɗa kenan ƙarshen maganarsa.

Da farko shiru yayi, ya ƙura ma file ɗin hannunshi idanu. Sai kuma ya ɗaga kai a kasale ya kalli Ummanmu, ya amsa da
“Eh, ciki ne da ita na ƴan satittika…”

“Na sani Dr. Na yi tunanin haka… tun jiya da ka tambayi rabonta da al’ada hankalina ya gaza kwanciya. Mamaki nake, takaici nake, tunani nake, ta ina nayi saken da har ƴata za ta sami cikin shege ba tare da ni uwarta na ankara ba? Na zama sakaryar uwa ko Dr.? Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un…”
Irin maganganun da Ummanmu tai tayi kenan cikin ɗimuwa da tashin hankali kafin ta haɗe kanta da gwuiwa ta saka kuka.

Minti ɗaya tsakani sai kuma ta miƙe a haukace ta ƙarasa kusa da Ziyada tayi mata wani irin mahaukacin shaƙa kamar mai niyyar kashe ta.
“Ziyada, rayuwarki ba ta amfani a gare ni. Da in cigaba da kallonki da cikin da ba na sunnah ba na rantse da girman Allah gara in ga gawarki shimfiɗe a gabana. Da me na rage ki Ziyada? Menene ban yi muku ba a duniyar nan dukda mahaifinku ba ya raye? Ni za ki kunyata ki wulaƙanta Ziyada? Ni? Ni? Ni?”
Gwanin ban tausayi ta ƙara fashewa da ihun kuka tana cigaba da ƙara matse hannayenta a wuyan Ziyada. Idanun Ummanmu sun rufe da tashin hankali da baƙin ciki. Da gaske a wannan lokacin babban burinta tayi ajalin Ziyada.

Kallon idanunta da yanayinta kawai Dr. yayi yasan lallai abin babba ne. Hankalin Ummanmu ya riga ya gushe. Don haka ya fita daga ɗakin a gaggauce ya kira Kareema da Rukayya.

Su uku suka haɗu kan Ummanmu da Ziyada daƙyar suka samu nasarar ɓamɓare hannunta a wuyan Ziyada. Lokacin ta gama galabaita ƙwarai, sai numfarfashi sama-sama take ja tana wani irin tari da kakari mai ƙarfi.

“Ku tambayeta uban wa yayi mata ciki? Na rantse da girman Allah idan bata faɗi wanda yayi mata ciki ba yanzunnan zan tsine mata albarka…”

“Khamis ne! Khamis ne Ummanmu!!! Wallahi tallahi Khamis ne!!! Na tuba, na bi Allah na bi ki Ummanmu, don Allah ki rufa min asiri kar ki tsine min.”
Ziyada tayi maganganun cikin matsanancin tashin hankali da ihu mai tsanani. Kamar ba ita ce take numfarfashi da kakari kamar za ta mutu ba. Da sauri ta dira ƙasa daga kan katifar, da rarrafe ta ƙarasa kusa da Ummanmu ta riƙo ƙafafunta.

Wani irin fincikewa Ummanmu tayi kamar Ziyadan ta taɓa ta da wuta. Idanunta sun ƙara kaɗawa sunyi ja-jajur. Izuwa yanzu kukan da take yi ya tsaya, sai wasu irin zafafan numfarfashi take saukewa tana huci ita kaɗai kamar za ta ci babu.
“Daga yau, har zuwa sadda za ki haife shegen cikinki ki manta ni ɗin mahaifiyarki ce…”

“Haba Hajiya… Haba Hajiya, Idan hankali ya ɓata ai hankali ke nemo shi. Wasu irin maganganu ne kike yi haka kamar wacce…”

“Dr, dan Allah dan Annabi ka saurara min. Na gode da nasiharka a gare ni, kana iya tafiya. Cikon kuɗin aikinka zan tura Rukayya ta kai maka.”
Ummanmu ta katse Dr. Nura da sauri jin yana neman yi mata katsalandan kan hukuncin da take ga in mutanen duniya za su taru a kanta babu wanda ya isa ya hanata ɗaukar matakin da tayi niyya!!!

Rukayya da Kareema tun daga jin abinda Ziyadar ta ɗaɗɗako musu suka yi wani irin suman tsaye, bakunansu a buɗe, hankulansu a tashe har Dr. Nura ya fice basu dawo cikin hayyacinsu ba.

Sai da Ummanmu ta daka musu wani gigitaccen tsawa haɗe da dukan kafaɗunsu da ƙarfi sannan suka dawo hayyacinsu a gigice.
“Na’am! Iye!! Me kika ce Ummanmu?”
Suka haɗa baki gurin faɗin haka a firgice haɗe da zubewa ƙasa a gabanta.

Wani fusataccen kallo ta aika musu cikin jin haushi kamar su suka kar zomon. Ta nuna Ziyada da yatsarta manuniya, da wani irin yanayi a fuskarta mai bayyana tsananin tsana da ƙyama ta ce
“Ku janyo min wancan abar a wulaƙance mu mayar da ita inda yafi dacewa da ita.”
Da gama faɗin haka bata ɓata lokaci ba ta fice daga ɗakin, daman hijabinta na jikinta.

Da farko duk basu gane ‘Abar’ da take nufi ba. Amma da yake idanunsu na kanta kuma sun ga wacce ta nuna sai suka gane Ziyada take nufi. A raunane suka kalli junansu, sai suka kalli Ziyada da ta cusa kanta tsakankanin ƙafafunta tana rusa kuka kamar ranta zai fita.

Idanunsu ne ya cicciko da hawayen tausayinta. Zukatansu cike da tunanin ƙaddara kuma mummunan iftila’in da ya afka ma ƙanwarsu.

“Wai ina kuke ne? Ko baku ji umarnin da nayi muku bane? Ko kuma ku ma kun bi layinta ne za ku fara ƙetare umarnina?”
Suka jiyo muryar Ummanmu daga can falo da taratsi take jero musu tambayoyin.

Cikin sauri suka watsar ds tunaninsu, suka ɗaga Ziyada ta hanyar rirriƙe kafaɗunta gefe da gefe suka fice da ita. Ko da Ummanmu ta ga sun fito bata tsaya ba ficewa tayi daga babban falon suka bi bayanta.

Ko da Ziyada ta tabbatar ficewa za suyi da ita daga gidan Ubanta sai ta fara turjewa tana ihun roƙon Ummanmu don girman Allah tayi haƙuri ta yafe mata.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 8Lokaci 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.