AN RUBUTA SHI 2014.
AN SABUNTA SHI 25 JULY 2020.
FARKO
A can gabas da ƙauyen Ɗan Duƙus da ke Jahar Kaduna Garin Gwamna, akwai wata maƙabarta babba da gyara ya wadace ta da kuma tsaro. Asalima dai duk hanyoyin shigowa dake kusurwowi huɗu na maƙabartar akwai masu tsaronta, waɗanda ko a wani lokaci sukan kula matuƙa da aikinsu. Sau da yawan lokuta duk gawar da ake ƙoƙarin kawowa cikin maƙabartar sukan yi ƙoƙarin haƙa kabarin da. . .