Skip to content
Part 1 of 9 in the Series Mafarkin Deluwa by Fulani Bingel

AN RUBUTA SHI TUN 2014.

AN SABUNTA SHI 25 JULY 2020.

FARKO

A can gabas da ƙauyen Ɗan Duƙus da ke Jahar Kaduna Garin Gwamna, akwai wata maƙabarta babba da gyara ya wadace ta da kuma tsaro. Asalima dai duk hanyoyin shigowa dake kusurwowi huɗu na maƙabartar akwai masu tsaronta, waɗanda ko a wani lokaci sukan kula matuƙa da aikinsu. Sau da yawan lokuta duk gawar da ake ƙoƙarin kawowa cikin maƙabartar sukan yi  ƙoƙarin haƙa kabarin da za’a binneta ba tare da kaje nemo masu aikin haƙa kabari ba.

Wannan ce tasa mutane da yawa ke ƙaunar kawo jama’arsu cikin maƙabartar, duba da yadda ake kula da ita da kuma tsananin taimakon da masu tsaronta ke yi ga bayin Allah. Haka ta hannun Attajiran garin suke samun abinci, yadda babu wanda ya saka su aikin tsaron haka babu wanda ya hana masu yi musu ihsani su yi musu. Haka idan ka lissafa taku ɗari da saba’in da biyar (175) daga maƙabartar, za ka tadda wata makekiyar gona, anan suke ‘yan nome-nomensu, dan har tukwanen rufawa kabari suna siyarwa lokaci zuwa lokaci.

Sama da shekaru biyar da wanzuwarsu gurin, amma babu wanda ya taɓa jin kansu ta wurin ƙyashin juna ko makamancin haka, duk kuwa da aiki ne ya haɗa su gurin. Hakance tasa mutane da yawa ke mamakinsu tare da yi musu fatan dawwama a hakan.

Malam shitu shi ne babba, shi ne kuma wanda ke da muƙamin shugaba a maƙabartar, daga nan sai Malam Lawal da Malam Tsalha, sai kuma ƙaraminsu Malam Zaidu.

Kamar yadda suka saba

duk lokacin da ƙarfe 11:00 na dare ya yi sukan saka katakwaye su rufe kusurwowi  uku na shigowa maƙabartar, ya zamana saura ta

Malam Shitu, nan zasu taho su zauna a gurinsa a yi ta hirar duniya har zuwa lokacin da 12:00 za ta yi kowa kuma ya kwashe ‘yan komatsansa ya tafi ga iyali, zuwa kuma ƙarfe 9: 00 na safe da zasu fito a ci gaba da aiki.

Hakan ta kasance yau ma gasu Malam Shitu.

Malam Zaidu ke basu labarin wani Almajiransa da ya taɓa kwashe masa miyar salla ya kiɓa masa tutu a tukunyar, ya ɗaga filonsa ya zare ‘yar sigarinsa ƙara uku da ashana da kafin ya kwanta barci ya ciyo bashinsu, ya gudu. Gashi lokacin bashi da ko sisin da zai sai wata ‘yar kazar da za’ayi wata miyar, haka ya haƙura sai na maƙota suka ɗan lasa. Suna ta masa dariyar yadda bai kai tukunyar ɗaki ba, da yadda har aka ɗaga masa filonsa bai farka ba, yana faɗin sakacin matan fa malam? Ai dan sakarcin ta bisa murhu tabar miyar. Almajiri ko sai dai in rufa ido ya masa, dan ko shi idan yana barci ko kiyashi ne ya gifta ta gefensa yana ji!

“Sai ka tuno mini da ranar haihuwar Bintu…”

Malam Shitu ya furta yana kaiwa sauron dake ƙoƙarin shige masa hanci cafka, daidai lokacin kuma, suka ga duhu-duhun mutum kamar

ana tahowa gurinsu, kamar kuma an garo taya, da sauri Malam Tsalha ya kunna tocilan ɗin dake hannunsa ya haska kan hanyar, ga mamakinsu yarinya ce ‘yar ƙarama ke tahowa gare su. Suka idasa miƙewa gabaɗaya suka yi shiru gami da zubawa yarinyar ido har zuwa lokacin data

ƙaraso gurinsu ta yi sallama. A sannan suka yi baya gabaɗaya suna faɗin Rabbi Yasir Wala Ta’assir!

Ba muryar yarinyar ce tafi tsorata su ba a’a, tsantsar halittarta da abinda ke jikinta shi ne yafi razana su.

Baƙace wuluk! Idan aka ce wuluk ana nufin Jange, idan baku gane Jange ba, ku kwatantata da baƙaƙen nan ‘yan South Sudan(Junubul Sudan), to sun fita haske. Tana da fuska irin ta manyan mutane, sai kanta rusheshe, idanunta ƙanana ne kamar kwan tsaka, haƙoranta farare ne ƙal! Sai dai manyan laɓɓa kamar an tauna ganda. Sai Jikinta ɗan ƙarami kwatankwacin na me shekara takwas. Sanye take da atamfa ɗinkin doguwar riga, kanta ba kallabi ta yi kwal-kwal kamar bayan kwarya. Tasa ɗan siririn gyale ta shaƙe wuyanta kamar an saƙalo biri, irin dai yafen indiyawa.

“Na ce Assalamu Alaikum!”

Ta sake maimaitawa da garjejiyar muryarta mai kama da kukan injin markaɗe, sai lokacin Malam Zaidu ya yi karfin halin amsawa yana runtse idanuwansa da ke ƙoƙarin kawo ruwa.

“Don Allah taimako nake nema!”

Ta furta cikin rarraunar murya, duk da sautin muryar ya fita ne kamar an zabura tattabaru.

“Taimako fa?”

Malam Tsalha ya faɗi da hanzarinsa.

“Eh Malam! wata gawa nake so ku taimaka ku binne mini ita yanzu…”

Ta bashi amsa a taƙaice…

A razane suka dube ta duka su huɗun.

Kusan a tare suka tambaye ta “wacce irin gawa?”

Duk da kowannensu akwai tunanin da ya fara a zuciyarsa game da ita. ‘Tabbas fatalwace in dai ba fatalwa ba, babu ta  yadda za’ai kamar wannan yarinyar ta ce wai a taimaka mata da gawa. ai dama wanda bai ji bari ba zai ji hoho, tun yaushe iyalina ke hanani kaiwa 12:00  a maƙabarta. Lalle Hansai ba tai ƙarya ba da take faɗin akwai waɗanda ke zaune a cikin maƙabartu mune dai ba ma ganinsu. Idan ko hakane babu abinda yafi irin ince zan ɗan zagaya daga nan na samfe gida, wallahi ba yadda za’ai na bi wannan fatalwar ɗauko gawa, in dai ta haka zan sami lahira gwara na koma sharar masallaci ko babu kome nasan can babu fatalwu sai Mala’iku, mala’ika kuwa ba shi razanani sai ranar da ƙarshena yazo…’

Malam Shitu ne yake faɗin hakan a zuciyarsa, yana yi yana sharce

gumin da ya jiƙe masa gemu duk ko da sassanyar iskar dake kaɗawa.

To haka ga Malam Tsalha, tunaninsa ɗaya da na Malam Shitu ba abinda yafi ruɗa masa ciki irin kwal-kwal ɗin kanta.

“Eh lalle na taɓa ji wata Yafindona ta ce, wai dama fatalwi ba su da

gashin kai, haka su ba su da tsayi irin namu na mutane…!”

Murɗawar da cikinsa ya yine

ya sa ya yi saurin dafe cikin, ya kai kallonsa ga Malam Shitu da yana da tabbacin ya ji zancensa…

“Malam ai sai kaje kaga yadda za’ayi ko?”

Ya furta bakinshi kamar zai rabe biyu don rawa. Da hanzari

Malam Shitu ya ce,  “yauwa bari to na ɗan kewaya, kai Zaidu bita ta nuna maka gawar.” Ya furta ba tare da ya kai dubansa gun yarinyar ba. Ya yi gaba da sauri yana saɓa babbar riga tana faɗowa. Malam Tsalha ya zari butar dake kusan ɗan teburinsu, cikin rawar jiki ya ce, “to ɗan tsaya ni na rage cikina…”

Yabi bayansa da gudu-gudu.

Malam Zaidu da Malam Lawal

suka dubi juna lokaci guda.

Ahankali Malam Lawal ya yi ajiyar zuciya yana mai zurawa hanyar da su Malam Shitu suka bi ido kamar mai tunanin wani abu…

“Don Allah Malam ku taimaka ku binne mini shi, ba na so gari ya waye.”

Ta furta tana kallon Malam

Lawal da ya tsurawa hanya ido kamar ace kyat! Ya arce da gudu. Shi fa duk sa’ilin da ya ji muryarta jikinshi har girgiza yake don tsananin tsoron da yake ji. Shi fa baya tunanin za a tsaga halittar yatsansa a ga ɗigon jini ma. Shi fa a yanzun da yake tsayen, babu abinda yake tunawa sai wata yarinya da ya binne wata uku baya, ita ma kanta babu gashi, ance wai cutar dajin hanji ta kashe ta. Har ya gama binne yarinyar sai yaga kamar tana masa gatsine, har kuma jiya da daddare sai da ya tuna fuskar yarinyar! Mammatse ƙafafunsa ya hau yi cikin malum-malum jin kamar wani matsiyacin fitsari na taho masa!

“Bari…b…Bari dai kiga yanzu

na ma su Maaaaaalam…

“Bari…bar…bari kiga

na yi ma su Maalam Shitu magana Hajiyata…Ai fa shi magirbin yana wurinsu…”

Ya furta yana rasa daliinsa na cewa ‘yar fatalwa

Hajiya…

Bai jira kome ba shi ma yabi hanyar dasu Malam Tsalha suka bi da

zummar ya kirawo su.

Gurin ya yi tsit! Ba ka jin kome sai kukan gyare da na kyanwowi sai kuma guje-gujen gafiyoyo kamar yau take sallah…Ba dan akwai ɗan taimakon hasken tocilan dake hannun Malam Zaidu ba, da ba abinda zai hana shi daskarewa a gurin ganin

har kusan mintuna goma abokan aikinsa basu dawo ba…

A karo na uku ta ce…

“Don Girman Zatin Allah Kai ka taimaka mini, a halin yanzu na tabbata abokan gadinka gudawa suka yi saboda sun ga ban yi kama da irin su ba, wallahi malam ‘Yar Wada Ce ni, haka aka haife ni, ban kasance wacce kuke tunani ba, ni mutum ce kamar kowa, haka fasalina yake.”

Ba don ya taɓa jin wani

hadisi dake haramta rantsuwa akan ƙarya ba, da ba abinda zai saka shi ya amince da wannan tatsuniyar.

‘Eh to, ta wani ɓangare biri ya yi kama da mutum, in ba haka ba ta yaya FATALWA za ta nemi taimakon akai mata gawa kabari?’

Ya tambayi kanshi….

“To amma idan ba fatalwa ba ce mai ya haɗata da GAWA a wannan lokacin, ina kuma ‘yan uwanta da za ta zo nan ita kaɗai ba tare da tsoron kome ba?

“Ka kwantar da hankalinka ni ba mai cutarwa bace gareka, haka ban kasance mai maida alkhairi ga sharri ba.

Ina zalunci amma ba irinku

nakw zalunta ba sai wanda ya zalunce ni, kome kake son sani daga gareni zaka ji idan har zaka yi ƙoƙarin taimaka mini. Sannan kabar dukkan tambayoyinka har mu gama binne gawar, na maka Alƙawarin sanar da kai ko ni wace ce. biyo ni muje lokaci yana

Ƙure mini.” Ta furta gami da juyawa ta fara tafiya…”

A sanyaye Malam Zaidu yabi ta yana furta Ya Laɗeefu a duk takun da zai yi, ga mamakinsa sai yaji kwarin gwiwar

bin ta sosai har da ƙoƙarin ɗaga dafa danya tarar da ita..

“Da zaka kashe tocilan ɗin

da ka hutar da kanka, don ba na buƙatar haske”

Ta furta a lokacin daya tararta yana haska hanya, da hanzari

ya zura tocilan ɗin aljihunsa, yana mamakin yadda yake bin umarnin wannan hajiyar,  ba tare da yace uffan ba suka miƙa.

Tafiya suka yi kaɗan, can

bayan wasu bishiyoyi yaga sun nufa, mota ce ƙirar akori-kura jingine a wajen bshiyoyin nan yaga ta nufa ta buɗe bayan motar da aka haɗa ankwa aka rufe. Yana gani ta ɗan taka wani abu a bayan motar sai gata ta haye samanta tsaf! Naɗe cikin tabarma gawar take, ga mamakinsa sai yaga ‘Yar Wadar ta ɗaga gawar kamar ta ɗauki jarkar ruwa ta miƙo masa yana daga ƙasa, da hanzari ya karɓa yana mamakin nauyin

gawar haka. “Yauwa muje”. Ta furta bayan ta sauko.

“Hajiya bazan iya tafiya da ita ni

kaɗai ba.” Ya samu kansa yana furta haka, to bari na kama maka riƙe wurin kai ni na riƙe wurin ƙafa, burina ɗaya yanzu shi ne mu binne gawar…!”

Tafiya suka ɗan taɓa sannan suka isa tsakiyar maƙabartar suka shimfiɗe

gawar….

Da hanzari Malam Zaidu ya ɗauko magirbi da shebur ya fara aikin haƙa kabarin, ita kuma ta koma gefe lokaci-lokaci takan je ta buɗe gawar kamar me nazarin wani abu sai

kuma ta koma ta tsaya.

Ya gama tsaf cikin ƙwarewa ya fidda kome yadda ya

dace, tukunna suka kinkimo gawar suka aza ta bisa kabarin, ya ƙara rufe duk inda ya dace yana mamakin

ƙamshin da gawar ke yi, suka zirata cikin kabarin ta kauda kanta tana mai komawa gefe, ya ɗaga shebur ya fara mai da ƙasar ke nan ya ji ance,

“Ina sonki, bazan taɓa daina sonki ba, burina ɗaya koda an gama zuba mini wannan ƙasar ƙarshen kalmata na ƙara jaddada miki kalaman soyayyata gareki.”

Daga cikin kabarin…

Bingel

Say tnx…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Mafarkin Deluwa 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×