Har aka kira assalatu barci ya gagari idon Deluwa, juyi kawai take saman gadonta tana hasko fuskar Annur a lokacin da ta ce masa sai ta yi tunani kafin ta yarda ta aure da aurensa. Za ta rantse da Allah taga walkiyar kalla cikin idonsa a sa'adda zai fita daga dakin, 'Oh ni Sarah! Kowane irin so yake mini da zafinsa zai kai shi ga yin kwalla?
Ta sake runtuma a guje zuwa gaban madubinta a karo na ashirin da shidda (26) tun tafiyarsu, ta shi fa kallon manyan kofofin hancinta tana kiyasta yadda suka ninnika na Annur girma. . .