Tafiyar minti talatin suka yi ya iso dan madaidaicin gidan nasa. Ya yi parking ya fito, ita ma ta fito tana karewa farfajiyar gidan nasu kallo, gurin ya mata kyau sosai,har ba ta san sanda sautin dariyarta ya fito ba. Tana ta kalle-kalle taga ya nufi wata golden din kofa ya bude ya dan waiwayo ya kalle ta, sai ta gane yana so ta biyo shi ne, dan haka da azma ta taho tinkis-tinkis abinta ta shige cikin kofar, inda ta wanzu a ciin wanin hadadden faslon da haduwarsa ya saka ta cisge nikaf din fuskarta,ta. . .