AN RUBUTA SHI TUN 2014
AN SABUNTA SHI 25 JULY 2020
Zuciyarsa ta buga, ya yi wani irin jifa da shebur ɗin hannunsa, ya yi baya a matuƙar razane yana kallon cikin kabarin. Shi fa tunda uwarshi ta kawo shi duniya, bai taɓa shiga tashin hankali irin na yanzun ba.
Gawa ce fa da furta kalmar SO... Gawa fa?
Wannan shi ne gobarar gemu! Wani irin amai ne yaji ya taso masa, kamar me son amayar da kayan cikinsa haka ya dinga sheƙa shi, nan da nan jikinsa ya ɗauki karkarwa, idanuwansa suka. . .