Bayan kwana shida, abubuwa da yawa sun faru, ciki harda ƙoƙarin da Bukr ya yi na koyawa Deluwa yadda za ta amsa dukkan tambayar da za su yi mata, musamman tambayar abinda taje yi a mataarr ɗin (Airport), in da ya ba ta dabarar ta ce ta je kaiwa wasu larabawa kaya ne.
Ya ci baƙar wuya kafin Deluwa ta gane larabcin har ta haddace amsarsu, da yake tana son fita sai ga Deluwa na kwana bitar kalmomin da basu kai shida ba da za a haɗa su a jimla guda. Haka nan ya fidda wasu riga. . .