Skip to content
Part 7 of 9 in the Series Mafarkin Deluwa by Fulani Bingel

Bayan kwana shida, abubuwa da yawa sun faru, ciki harda ƙoƙarin da Bukr ya yi na koyawa Deluwa yadda za ta amsa dukkan tambayar  da za su yi mata, musamman tambayar abinda taje yi a mataarr ɗin (Airport), in da ya ba ta dabarar ta ce ta je kaiwa wasu larabawa kaya ne.

Ya ci baƙar wuya kafin Deluwa ta gane larabcin har ta haddace amsarsu, da yake tana son fita sai ga Deluwa na kwana bitar kalmomin da basu kai shida ba da za a haɗa su a jimla guda. Haka nan ya fidda wasu riga da wando ya ba ta ta canja a banɗakin cikin ɗakin bayan kayan da aka ba su a firzin ɗin, wanda suka kara maidata namijin gaske sosai.

Haka suka share kwanaki shidan nan har zuwa yau da Deluwa take alla-alla gari ya waye, don ta fita da ga sijin.

Wanshegari da duku-duku aka fito dasu, sa’annan aka jera su a layi, aka hau bincike, nan dai kowa ya nuna ba wanda ya sani a garin, da dai tarin maganganun da suka tanadar don kare kansu. Haka akai ta tafka bincike da haɗin bakin Baban Bukr da yake ɗan Agulla me kuma ido ga manyan mahaman wurin(lawyers) aka wanke Deluwa.

Ƙarshe dai sai ga jakarta an fiddo aka bata, cikin azama aka dannasu a mota ita da sauran yaran aka yi unguwar Shaari Almansoor da su.

Sai dai ga mamakin Deluwa, lokacin da ta tabbatar ta zauna a motar, lokacin ne ta ji wasu busassun hawaye na zubo mata na kewar sijin. Lalle ta shaƙu da wurin ba kaɗan, watakila kuma kayan dadin da ta ci a wurin ne sanadin kukanta.
*****

Ta yi ƙuruuuuu, tamkar bushiyar da ta hango silalowar miciji bakin raminta tana kallon yadda abokan tafiyarta ke watsewa ɗaya bayan ɗaya tun bayan saukarsu daga motar da ta kwasosu. Idan ka kalli fuskarta a halin yanzu lalle zaka ga damuwa lulluɓe da ita.

Sharf ta manta ba ta tambayi Bukr sunan masaukin baƙi da larabci ba, balle yanzu ta tambaya a nuna mata gun. Ta ja wani dogon tsaki mai kama da gyatsar ɓera, kana ta fara waige-waige ko za ta hango wani cikin yaran, ‘Ahaf sun watse wallahi!’ Ta furta a ranta,

“To ai shi kenan tafiya zan ta yi duk inda naga gininsa ya faye tsayi da kyawu kawai nan zan shiga, na tabbata idan basu jin Hausa, ai suna jin yaren bebaye, aikin banza kawai an…” “Ukhty…” ta ji an furta daga bayanta, ta juyo da sauri tana kallonsa, sai kuma ta washe wargajejen bakinta alamun murmushi take, yaron ya kauda kai da sauri sakamakon hango ƙarshen makwallatonta da ya yi. “Ukhty ki tafi masaukinki mana, kin tsaya a shaari ke kaɗai, wanda hatsari ne ga baƙo irinki, gashi ko fuskarki da hannuwanki ba ki rufe da nikabi ba ko safa, a kowane lokaci Askarawa masu kame zasu iya zuwa nan, kuma can za a m…”

“Dakata Bukr” ta katse shi da sauri.
“Wane irin ‘Yankame za su zo nan ? Sata na yi? Ko kuwa zagin ubansu na yi da za su dinga bin rayuwata haka, wai ni halan ƙasar nan tsatson ubansu ce? Ni kawai ka faɗa mini in da masaukin yake naje.. ”

Ya yi saurin gintse dariyarsa ganin yadda ta rikice tun kafin ya tumma mata zancensa…
“Ukhty dama baki da mai kula dake anan ɗin kika zo ke kaɗai?”

“Yaro idan ina da ai bazan tambayeka masauki ba.” Ta furta tana ƙara ƙanƙance idanuwanta.”

“Aiwaa mo mishkila! Yanzu to shige muje na nuna miki wani Funduk (hotel) nan kusa ki fara zama kafin na yiwa Abbu magana ko zai baki gurfa guda a shiggarmu, kin ga gidanmu na tahit ɗinmu duk masu irin harshen ki ne.” Ya faɗi yana ƙoƙarin kamo ‘yan guntayen hannuwanta.

Tafiya sassauka suka yi bayan arye-‘aryen wasu tituna sai gasu a ƙaton masaukin bakin, kai tsaye yaron ya shige gaba cikin wajen hannunsa na harɗe dana Deluwa. Da wani sanyi ya ratsa Deluwa bata san sanda ta ƙara ƙanƙame hannun ba, sai da ya juyo yana mai nuna mata hannunsa tukunna ta tuna ta sassauta, ga mamakin Deluwa sai taga yaron ya na gaisawa da mutanen da ke ciki…

kowa kuma na ambaton sunansa, cikin ƙanƙanin lokaci taga sun yi abinda zasu yi, bayan sun tambayeta kuɗi, ta buɗe jakarta gami da zaro duk abinda ke ciki ta zube musu duka, wanda duka canjin Dala ce, cike da rashin damuwa da sakarcinta, suka ƙirgi iya haƙƙinsu suka maida mata sauran.

Nan aka umarci mai kula da baƙi, da ya kai Deluwa ɗakinta ita da Bukr, ya cika kuma dukkan aikinsa na nuna mata wayar da za ta kira masaukinsu a duk lokacin da take son fita zuwa Ɗawafi harami (A zatonsu Umara ta zo) ga Bukr nan zai dinga mata tarjama.

Ita dai Deluwa tana ƙame a gefe tana mamakin hatsabibancin yaron na yadda taga yasan kowa a cikin otel din.

Har dai zuwa lokacin da suka gama kome aka nuna mata wani dogon tsani me tafiya da kansa (Lifter) aka ce wai nan za ta bi zuwa ɗakinta.

Ta kuwa warce hannunta da ƙarfi tana hararar Bukr… “Ka kyale ni Yaro, wallahi ka ji na rantse maka ba na hawa wannan tsanin mai injina ga Bene can ina hange, irin namu na mutane, in ma ba jaraba ba ta ya ya wannan tsanin zai kai ni sama, da wannan uban ƙarafan, idan na hau ya datse mini ƙafa sadaki na ya ragu, uban me zan cewa Chibunzu?”

Ta faɗa tana sauke numfarfashi, Bukr da tunɗazu yake naci ya yi saurin jan hannunta gami da bin bene, ganin tana ƙoƙarin tara musu mutane da garjejiyar muryarta. Da ƙyar da naci Deluwa ta iya gane dukkan abinda suka nuna mata, musamman banɗaki gurin bambance madannin ruwan zafi da na sanyi, kana bayan wasu shuɗewar rabin Awa Bukr da mai kula da baƙi sukai mata sallama suka tafi, ita kuma ta tuɓe ta afka toilet ta hau sille baƙar fatarta.

*****

“Ka tabbata tun safen har tahowarka nan babu yarinyar daka gani cikin waɗanda aka sauke a Shaari Mansoor?”

“Abuya wallahi dai yadda na faɗa maka tun fari hakan yake, gabaɗaya yau iya maza ma suka sauke, babu mace ko ɗaya cikinsu, kuma yara ne ai.” Ya furta fuskarsa na nuna alamun damuwa sosai.”

Abuya ya nisa yana kallonsa kamar mai son ganin tabbacin zancen a fuskarsa, sai kuma ya duƙa yana wasu irin zane da Alƙalumansa, bayan kamar shuɗewar mintina goma ya ɗago ya ce “Ya Annur, ka saurare ni da kyau, ka kuma yi tunani sosai. A cikin yaran da kace ka gani, shin akwai wanda ka haɗa ido dashi ka ji faɗuwar gaba?”
Ya yi shiru yana kallonsa cikin kokwanto da zancensa, ‘Bukr!’ Ya furta a ransa…

Eh tabbas ya kalli Bukr riƙe da hannun wani yaro me ƙaton kai marar kyawun gani… Wanda kallo ɗaya ya masa ya kauda kansa sakamakon rashin jin daɗi da ƙunci da ya ji cikin ransa.

“Na’am Abuya! Na kalli Bukr wannan yaron ɗan gurin Jamal Hisen riƙe da hannun wani yaro marar kyawun gani, da alama shi ma Hausawy ne!”

“To maza koma ka nemo Bukr ya Annur, lalle matarka na tare da Bukr, shi kaɗai ne zai nemo maka ita, ba Alƙalamina ba, koma ka tambaye shi mai ya sani game da baƙuwar ‘yar Nijeriyar da aka kawo musu sijin, shakka babu baka dawowa nan sai da tabbacin ka sameta.”

Ya yi shiruu, Tunani da yawa na yawo kansa, amman sai kawai ya miƙe ba tare da ya tofa wani abun ba ya fice daga gurin a sanyayepp.
*****

“Kai ba za ka koma gun aikin kaba ko, harka fara yawo a gari salon ka ƙara tsokano wani a kwashe ku cikin Sijin ko?”

Matsakaicin mutumin ya faɗa yana mai ɗora hannunsa kan doguwar ƙeyar yaron dake gabansa. “Zan koma Akhee Annur, ra’ees ɗin Dammam dinne har yau ba a kawo masa jariran Rakuman ba, kuma fa ban shigo Makkah ba, sai da na rabbamasa Rakuma biyar.” “To kaje gurin Abbanka daka fito? Yaron ya yi zuru yana kallonsa “Aiwa to shi kenan, na gane baka je ba don haka gobe ka tabbata ka tafi gurinsa, karna ƙara ganin sawunka cikin Makkah”. Yaron ya gyaɗa kai da alamun yana girmama mutumin. “Uf! Yauwa Bukr! A sijin ɗin da aka kai ku ko ka kula da wata sabuwar baƙuwar ‘yar Nijeriyar da aka kawo?” Ya faɗa fuskarsa na nuna ya tuna zancen ne lokacin.

Yaron ya yi shiru kamar yana son tunowa, sai kuma ya fara gyaɗa kai. “A’a Akhee gabaɗaya waɗanda aka kama duka yaran takarin nan ne da suke ɗora musu talla cikin harami”. Ya yi shiru tunaninsa na bashi lalle duk yadda akai Malam Abuya ya masa ƙarya ne, kamar yadda sauran Malaman suka masa, fuskarsa ta fara canjawa da alamun ɓacin rai, amman dan ya akkada sai ya sake tambayarsa. “Lalle Bukr kace wannan karon ‘yan Nijeriyan namu sun yi hankali, tunda dai ba a samu baƙi cikinsu ba, sai zaunannun ƙas…”

“Lah! Akhee na tuna” Yaron ya yi saurin katsesa.
“Akwai wata da suka kamo a gefen Matarr, badan ta haɗu dani ba na tabbata da tuni sun maidata gida, amman yanzu haka na nuna mata wani funduk tana can cikinsa tun jiyan da muka fito, ita kaɗaice na sani sabuwar baƙuwa.” Ya faɗi yana sauke wani nannauyan numfashi, da alama yaron baya jure jera zance.

Cikin zumuɗi ya riƙo hannun yaron duka biyun, fuskarsa cike da yalwataccen murmushin dake nuna lalle farin cikin da yake ciki ya kai lungun zuciyarsa “ka tabbata ko Bukr, ba ni labari game da ita, wane irin kyawu gareta, wane irin Saut (murya) gareta, zazzaƙar murya ko? Ta dace da ni ko Bukr?”

Yaron ya yi satato yana kallonsa, zuwa yanzu ya kasa fahimtar zancen ɗan uwan nasa, “ka santa ne”? Ya ji bakinsa na furtawa a hangame , “Itace matata Bukr, itace Uwar ‘ya’yana, lalle yau na ƙara godewa ubangiji bisa wannan falalar tasa gare ni, ashe dama bil Adama na ganin amfanin haƙurinsa?” (A Habbak Kathirr ya Abuya) Ya faɗi gami da rungume sandararren yaron da ya daɗe da sandarewa sakamakon jin harɗaɗɗun maganganun ɗan uwan nasa. Kamar a kunnensa yaji yana faɗin “wuce muje Bukr, kai ni naga CIKON FARINCIKI NA.” Ba musu yaron ya karɓe jikinsa, kana ya riƙo hannun Annur dake ƙoƙarin zaucewa.

Zatonka zai iya zama daidai sa’iin daka dubi fuskar yaron lalle akwai tarin sanyin jiki tare dashi, musamman na jin zantukan da yarintarsa ba za ta barshi ya yi tunaninsu ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mafarkin Deluwa 6Mafarkin Deluwa 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×