Skip to content
Part 1 of 2 in the Series Mahaukacin So by Fatima Ismail Abdullahi

Wani mutum ne magidanci kakkaura zaune cikin wani tafkeken falo ,jarida ce bisa hannunsa yana karantawa.

Wannan mutum ba kowa bane face Alaji Muktar mazaunin kaduna

Mutum ne mai kudi bana wasa ba .

Wata dattijuwa ce ta shigo falon, kallo guda zaka ga babu wahala jikin wannan tsohuwa.

Tsayawa tai ta zuba masa ido tana kallon shi .

Bayan ya lura da ita ne , ya yi sum-sum ya cire gilashin dake fuskar shi yana aje jaridar .

“Hajjiya lafiya kuwa.”?

Ya yi wa dattijuwar tambayar

Kawai tsaki tai tare da juyawa ciki tana cewa.

“Duniya ce .”

Alaji Muktar ya yi murmurshi yana cewa.

“Hajjiya ke nan .”

Kallon hoton dake falon dakin take kamar zai motsi a yadda take gani , sake kura masa ido take tana kallon dayar matar da suke tare a cikin hoton da suke matukar kama da juna .

Wata mata ce ta katse mata tunanin data fara da cewa.

“To Mama zan tafi Allah ya jikansu Allah ya bada hakurin rashi.”

Sannan Mama ta dawo hankalinta tana kallon wannan matar tana cewa.

“To mun gode Zuwaira , Allah ya bada lada.”

Kana matar ta fice

Mama ta kalli Nasir dake tsaye da jaririya a hannunsa yana jijjigata ta ce .

“Sannu Nasir da raino , ai idan suka zo suka dauketa sai ka huta .”

Rai ya hade mata yana cewa.

“Haba Mama , ni fa baza a basu wannan yarinyar ba , kawai kar ma su zo.”

Mama ta kalli autarta Ummi dake gefenta suna hada idanu.

Sannan ta koma ta kalli Nasir tana cewa.

“Kamar ya baza a basu ita ba , yarinya jaririya kai ne zaka shayar da ita .”?

Nasir ya yi ajiyar zuciya tare da shigewa cikin daki ba tare da ya ce komai ba .

Gidan Mama ke nan mutuniyar kirki wacce tun shekarun baya mijinta ya rasu, kana kanwarta wacce suke tare ita ma Allah ya yi mata rasuwa, sai Mama ta zamo ita ka dai , sai ‘ya’yan ta da Alaji ya bar mata

Ibrahim, Nasir, sannan Ummi

Wanda a kwana uku da suka wuce ne babban dan nata Ibrahim da matarshi Allah ya yi musu rasuwa, sanadin hatsarin mota.

Wanda suka tafi suka bar jaririya yar karama mai suna Laila .

Sai dai tunda a kai rasuwar yau har kwana uku Nasir yaki bawa dangin matar jaririyar , ya ce ita kawai yake gani yaji dadi tunda babu yayanshi Ibrahim..

Wannan ke nan

Yana zaune a falo jaririyar sai kuka take , ya tashi ya dauko fidarta dake cike da madara ya fara dura mata , har ta fara sha , amman tasake bingirewa da kuka .

Ya mike tsaye ya dauko ruwa ya bata , sannan tai shiru ya fara yi mata waka yana jijjigata da cewa .

“Lailo, Lailo rigima, Lailo Lailo rigima, kukan ya isa haka .”

Tai shiru ta tsura masa idanu , yanayin wata rawa da yayi mata ya sa ta sake fashewa da kuka .

Sai ya cigaba da jijjigata yana mata wannan wakar .

A lokacin Mama ta shigo , ta kalli Nasir cikin takaici tana cewa.

“Wai Nasir mene kake yiwa yarinyar nan , saboda taurin kai ka basu yarinyar nan amman ka ki , kullum kuka a cikin gidan nan , yarinya jaririya duk ta rame ta yi baki , to wallahi bazan yadda ba sai ka basu yarinyar nan.”

Nasir ya yi ajiyar zuciya yana cewa.

“Haba Mama dan Allah, ni zan kula da yarinyar nan idan ku baza ku iya ba , babu inda zan kai ta .”

Mama cikin fada ta ce .

“To ai ka basu su shayar da ita ko , idan kuma kana da nonon da zaka bata naji .”

“Haba Mama, Laila fa watanta biyar a duniya, ai ta kai lokacin yaye , ni wallahi na yayeta babu wanda zai shayar da ita .”

Mama tai shiru tana kallon Nasir domin takaici ya sa ta rasa abin cewa.

A lokacin wata kawar Ummi ta shigo , ta durkusa da gaida Mama .

Sannan Nasir ya sa jaririyar shi a baya ya goyata .

Washe gari

Wajejen hantsi wata dattijuwa zubin masu fada tana zaune a tsakar gida ,

Tsinke ne a hannunta tana sakace, ta jefar da tsinke tare da tsaki da fadin .

“Bahijja, Bahijja.”

Tai kiran tana tura kanta cikin dakin da Bahijjan take .

Bayan Bahijjan ta amsa ne , ta fito tare da zama gaban mahaifiyar tata tana cewa.

“Gani Inna na yi zatan ma bacci kike yi.”

Inna ta ce .

“Shiryawa zaki mu je mu dauko wannan yarinyar idan baso suke su kashe taba .

Ita Maman Nasirun fin karfinta ya yi da baza ta ce ya bada ita ba , ya bayar .”

Bahijja tai ajiyar zuciya me zafi tana cewa.

“Dan Allah Inna kibar musu ita.”

Inna ta ce .

“Lallai ne Bahijja, ai daga ke har Nasirun babu wanda yasan zafin haihuwa, shi ya sa baku damu ba ,

Kuma wannan yarinyar Laila ai nima jikata ce , ina da iko da ita , dole zan je na karbota mu anan akwai wanda zai shayar da ita .”

Ta karasa maganar tare da mikewa tsaye ta shige daki , da nufin shiryawa domin zuwa gidan Mama.

Anan kuwa Nasir yana zaune a falo sai kwalawa Ummi kira yake yana fad’in

“Wai har yanzu ba a gama wankan ba ne .”?

Ummi ya yi mata kiran yafi a ‘yarga , harta gaji ta dena masa magana

Ita ma Mama dake zaune a falon ko kula shi ba tai ba , Kamar ma bacci take son yi .

A lokacin Ummi ta shigo rike da Laila a hannunta an san ya mata kaya masu kyau .

Sai suka ji ana kwankwaso kofar falon .

Nasir ya mike ya karbi Laila a hannun Ummi yana cewa.

“Je ki duba .”

Mama kawai taji dariya ce ma ta kamata .

Ya zauna tare da Laila a hanunshi , Ummi ta nufi kofar tare da budewa .

Inna da Bahijja ne , hakan ya sa cikin sakin fuska Ummi ta musu iso zuwa cikin falon .

Amman yadda Ummi ta kula furkar Inna babu annuri ko kadan , musamman yadda taji ta ratsa tsaki da ta ga Nasir.

“Sannunku da zuwa Inna , ku ne a gidan .”?

Mama ta fada yayin da take gyara musu gurin zama .

Zama suka yi , Bahijja ta gaisa da Mama cikin far a

Sannan Nasir ya kalli Inna yana cewa.

“Inna ina kwana .”

Ya mutse fuska ta yi sannan ta ce .

“Lafiya lau , kawota .”

Ta mika hannu, Nasir ya kalli Mama kamar bazai bada Laila ba sannan ya mika mata .

Murmurshi Mama ta yi tana kallon furkar Inna da babu annuri tana cewa.

“Ya mutanen gidan suke , ya karin hakuri.”

Inna ta kalli Mama tana cewa.

“Hakuri kam muna ta yi , tunda ga shi mun zo mun ga yarinya jaririya duk ta canza , saboda wahala .

Shi ya sa na taso domin yau zaku bamu ita.”

Inna ta aje maganar tana kallon Nasir

“Tafiya da ita kuma .”?

Nasir ya tambaya

Inna ta maida masa da amsa da cewa .

“Ehh ko zaka hana ne ubanta .”

Nasir ya mike tsaye tare da cewa .

“Amma ai na ga mu ne dangin mijin yarinyar nan , dan haka mun fi kowa iko da ita.”

“Wallahi idan ka ce zaka min rashin kunya zan kwashe ka da mari anan wajen .”

Inna ta maida masa

Mama ce tai ajiyar zuciya tare da kallon Inna tana cewa.

“Ki yi hakuri Inna, ai abin bai kai haka ba , za a baku ita .”

“Mama kamar ya za a basu ita , a kan me .”?

Mama ta kalli Nasir cikin fushi tana cewa.

“Idan ka sake samin baki a magana sai na bata maka rai .”

Inna ta kalli Ummi tana cewa.

“Shi ga ki debo mini kayanta .”

Mama tai saurin dakatar da ita da cewa .

“Ba sai an yi haka ba Inna in Sha Allah gobe da kai na zan zo na kawo muku Laila, in Allah ya yarda .”

Nasir yaji wani abu ya tokare masa zuciya

“To shi ke nan Allah ya kai mu goben , muna jiran ku.”

Inna ta karasa maganar tare da mikawa Ummi jaririyar tana kuma tashi tsaye

“Haba ! Ko ruwa baku sha ba zaku tafi .”

Mama tai magana tana kallon Inna , yayin da ita ma Bahijja ta mike tsaye

“Eh zamu tafi muna da komai a gida, sai naji ku goben .”

Tana gama fade ta fice Bahijja tabi bayanta…

Mahaukacin So 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×