Wani mutum ne magidanci kakkaura zaune cikin wani tafkeken falo ,jarida ce bisa hannunsa yana karantawa.
Wannan mutum ba kowa bane face Alaji Muktar mazaunin kaduna
Mutum ne mai kudi bana wasa ba .
Wata dattijuwa ce ta shigo falon, kallo guda zaka ga babu wahala jikin wannan tsohuwa.
Tsayawa tai ta zuba masa ido tana kallon shi .
Bayan ya lura da ita ne , ya yi sum-sum ya cire gilashin dake fuskar shi yana aje jaridar .
"Hajjiya lafiya kuwa."?
Ya yi wa dattijuwar tambayar
Kawai tsaki tai tare da juyawa ciki tana cewa.
"Duniya ce ."
Alaji Muktar ya yi murmurshi. . .