Ita kuwa har yanzu Yaya kuka take yi saboda cin zali yarinya na jego? Wane irin hali ne wannan? Har da rokon Yaya da na zauna nayi ta yi bata fasa shirin ta ba. Ta rantse akan gobe zata tafi. Ba dukana da Ishak yayi ba ne damuwata, tafiyar Yaya ne. Don kuwa nasan tana barin gidan zamu koma zamanmu na baya.
Na durkusa a gabanta na ce "Yaya don Allah kiyi hakuriki zauna ko sati biyu ki kara kin ji?" Ta zuba mun ido. Zuwa can ta ce "Aiya! Abinda dan uwana yayi miki bai bata miki rai ba. . .