Skip to content
Part 10 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Ita kuwa har yanzu Yaya kuka take yi saboda cin zali yarinya na jego? Wane irin hali ne wannan? Har da rokon Yaya da na zauna nayi ta yi bata fasa shirin ta ba. Ta rantse akan gobe zata tafi. Ba dukana da Ishak yayi ba ne damuwata, tafiyar Yaya ne. Don kuwa nasan tana barin gidan zamu koma zamanmu na baya.

Na durkusa a gabanta na ce “Yaya don Allah kiyi hakuriki zauna ko sati biyu ki kara kin ji?” Ta zuba mun ido. Zuwa can ta ce “Aiya! Abinda dan uwana yayi miki bai bata miki rai ba, don na dan faranta mata sai na ce “eh Yaya.”

Ta ce, Ikon Allah kenan yanayin wanda yafi haka. Kin ga kuwa ba zan tsaya sai an yi kafin na tafi ba ko? Babu yadda na iya da ita don haka na shiga daki na dauko turamen zannuwa masu kyau sosai na bata guda biyu. Na hada da kayayyakin su turare sabulu da omo da hijabai tare da kudi ma dan auki na ce, Yaya to ga wannan tunda ban san haka tafiyar taki zata zo mana ba. Ta ce, na gode miki Hauwa’u ki kuma yi ta hakuri kin gane ko? Na ce, eh. Na dauko Naira dubu biyu na ce mata wannan ki siya ma Rukayya sweet a hanya ki ce mata in ji ni.

Tayi murmushi abinda yasa na fahimci hakan yayi mata dadi ba kadan ba. Ta ce zan gaya mata.

Kicin na wuce don nayi girkin dare, don ba zan jira sai Yaya ta tafi ba, 1tama tana shirin kayanta. Da daddare ina daki ina jin su da Ishak fama yake yi da ita. Amma ko sauraronshi bata yi, wasu irin maganganu take yi mishi masu zafin gaske. Hakuri yake bata amma bata sauraronshi. Kayi kokari itama ka koreta sai kuma ka san nayi. Amma ina tabbatar maka zuwa gidanka na daina yi, idan har ba taitayinka ka shiga ka kama kanka ba.

Ni dai bacci ya dauke ni ni na sake farkawa na jiyo su na gyara kwanciyata ban bude ido ba sai da aka yi kiran sallah. Yaya na samu har tayi wanka ta gama shiri cikin sauri na ajiye mata tunda ni har yanzu sallah ta bata daidaita ba. Wani lokaci ina ganin alama. Ta ce, kai ni Hauwa’u wani kari zan yi, na ce yi hakuri Yaya ki karya, ta ce to.

Ina zaune a gefen ta ina shayar da abulkhairi ta kalle ni, “Hauwa’u. Na ce, Na’am Yaya. Kada kijewa iyayenki a haka da wannan idon ki bari sai ya washe.” Na ce, To.

Tafiya Yaya tayi bata dauki ko kwandalar da lshak ya bata ba. Duk kuma alama ne na tsananin fushin da tayi da shi. Gidan yayi mun wani iri don dama-dama Abulkhairi yana rage mun ‘yar damuwa. Wunin ranar kuma Ishak bai leka ko ina ba.

Na gama abincin rana na dauko na kawo mishi dakinshi ya ce, kai mun falo gani nan zuwa. Bai fito ba sai da ya yi wanka yayi sallah ya gama cin abincin shi ya shigo dakin ya same ni ina bai wa Abulkhairi nono.

Ya zauna a gefen gadon yana kallonmu. Na gama ba shi nono na mika mishi shi ya karbe shi. Yana dan mishi ‘yan wasanni. A raina na ce Ya iya wasa da danshi kuma kana ganin irin yadda yake tafiyar da yaron zaka gane yana da muhimmanci a wurinshi.

Da ni ne kawai ko kuma na ce da matanshi bai iya mu’amalla ba. Ya dago kanshi ya kalle ni muka hada ido kadaran-kadahan fuskarshi. Na sunkuyar da kaina. “Me yasa idan na ce miki bana son abu ba kya bari? Kinga abinda hakan yaja mun Yaya ta tafi tana fushi da ni abin da bai taba faruwa ba.

To kada kiyi tunanin hakan zai sa na sassauta daga kan ra’ayina na bana son mu’amallarki da ita. Nayi shiru zuwa wani dan lokaci na ce, To amma menene dalilinka na hana ni mu’amalla da mutane da ka ke yi? A ciki har da yan uwana? Kana ganin idan kayi mun hakan kayi mun adalc1? Kada ka manta kafin aurena dą kai ina da kyakkyawar muamalla tsakanina da ‘yan uwana a yanzu ko inda suke ba ka barina naje?

“Ba hana ki mu’amalla da su nake yi ba. A yanzu kin yi kuruciya, ki fahimci abubuwan da nake kokarin fahimtar da ke, don haka ba zan Zauna yin wannan bayánin ba a yanzu.” Ya dauki Abulkhairi ya fita da shi. Na bishi da ido har ya gama fita a dakin nayi ajiyar Zuciya a hankali.

Ban je gida ba sai bayan sati guda cif da tafiyar Yaya. Ina zaune a gaban Ummana farin cikinta bai misaltuwa. Su Tasi’u kuwa sai kokarin a ba su Abulkhair su dauke su. Umma ta hana har Yaya Auwalu ma ya baro kasuwarshi da wurwuri da nayi mishi waya na gaya mishi muna gida. Shi ma Ishak bai zo daukata ba har Babana ya dawo daga aikinshi ya same mu. Muka hadu muna ta hira gwanin dadi.

Ishak bai zo ba sai karfe shida na yamma, kirana yayi a waya ya sanar dani isowarshi ban kuma nemi ya shigo ba don nasan ko na nema ba samu zan yi ba. Na shiga daki muna sallama da Umma na ce, Ni Umma kina ganin za ki iya yin wata sana’a kuwa ta cikin gida’? Ta ce, Eh to me zai hana sai na gwada na gani.

Hannu nasa a cikin Jakata na ciro mata kudin da na tanada wanda na tara a lokacin bikin sunan Abulkhairi. Na mika mata gaba daya na ce, Ga su nan ki gwada muga abinda Allah zai yi. Ta ce, Ke ko a ina ki ka samu kudi haka? Ban tsaya yi mata wani bayani ba goya Abulkhairi kawai nayi na fito muka tafi.

Abubuwan Ishak sun dan ragu, musamman da yake ya kan dawo gida a yanzu da dan wuri ko don Abulkhairi. Sai dai duk da haka ranar da abin nashi ya motsa sai ya kai sha daya na dare. Kullum naga yanda Ishak yake tafiyar da yaron mamakinshi yana kama ni. Menene hujjarshi na har a yanzu da na fara haihuwa da shi bai yi tunanin ya gaya mun komai game da labarin ‘ya’yanshi ba?

Wani lokaci sai naji kamar nayi mishi magana amma sai naga to ma menene na hanzari ne bari dai na kyale shi naga iyakacin gudun ruwanshi. Yau kuwa da ya dawo aiki da wuri zaune muke duka a falon yayin da Abulkhairi yake kwance kan Cinyarshi yana barci.

Ya dauko wayar shi ya daddanna ya fara magana na kuma gane da Yaya ne don haka na nemi ya bani wayar na gaisheta. Muna gaisawa ina tambayarta abubuwa da gangan na ce Yaya ya su Rukayya? Ina ganin irin kallon da Ishak ya watso mun wanda ban san ma’anar shi ba.

Yaya ta ce, tana nan lafiya gata nan ma a kusa da ni na ce bata mu gaisa, yarinyar ta fara gaishe ni cikin muryarta mai sanyi ta ce mun, Ina Baba karami? Nayi murmushi na kuma san Yaya ce ta sa ta ta tambaya. Na ce Baba karami yana nan lafiya Rukayya, to ai ba ki tambayi Baba babba ba?

Ta ce, To ina Baba babba? Na ce gashi nan bari na baki ku gaisa. Na mika mishi wayar har yanzu kallona yake yi. Ban zauna ba’ wuce shi nayi na shiga daki na zauna. Sai dai a madadin naji dadin abinda nayin wani gululun bakin ciki ne ya tokare mun kirii. Ishak ya raina ni yana yi mun wani gani-gani to amma babu laifi.

Da kanshi ya shigo dakin yazo ya gyarawa Abulkhairi wurin kwanciya, ya ce zan samu wuri kuwa a nan? Na ce me zai hana idan kana bukata na gyara yanayin kwanciyata shima ya kwanta yana fuskantata.

Juyawa nayi na fuskanci bango da nufin na kaucewa kallonshi nayi bacci sai dai abin ya gagara. An kai kamar awa daya bayan nan sai naji ya kira sunana ban amsa ba har ya sake tare da dan daga murya.

Na amsa ya cé, juyo muyi magana. Na juyo ina fuskantarshi. Ba tun yau ba naso na zaunar da ke don muyi wasu yan maganganu sai dai ban samu lokaci ba. Nasan babu mamaki kin ji wadansu maganganu daga wurin Yaya. Na ce kamar

*****

Don kuwa yadinan shadda bandir biyu ya saya da atamfofi da kuma wasu kananan abubuwan amfani iri-iri. Nima koda nake da kayan amfani ya karo mun da kuma Abulkhairi da yake na fara bashi abincin gongoni. Muna zaune a falo ana gobe zai tafi rike yake da abokiyar hirar tashi Jarida na ce ni haka zamu zauna ne a gidan nan idan ka tafi dagani sai Abulkhairi?

Ya dauke Jaridar a fuskarshi ya kalle ni “Ban gane ba?” Na sake maimaita mishi tambayar ya ce, Eh to menene?

Na ce, “Ba zan iya ba ne ina jin tsoro. Kuma nayi tunanin kai da kanka zaka fahimci hakan ba tare da nayi maka magana ba. Sai naga ba ka yi ma wannan tunanin ba. Kuma ai ya kamata ka fahimta. Da kanka cewa ko ba na tsoron zaman ni kadai ma ai ba1 yi tsari ka tafi ka bar ni daga ni sai yaro mai watanni biyar a cikin gida irin wannan ba. Ko mutanen gari ne suka fahimci baka nan ai…”

“To naji ya isa haka.” Na ja bakina nayi shiru shima ya ci gaba da karatunshi.

Abulkhairi yayi bacci na mike na shiga daki na shimfide shi na fito falon na sake zama lokacin ne ya kalle ni.

“To menene ra’ayinki?” Na ce ni bani da wani ra’ayi idan a kan wannan ne. tunani yazo mun a cikin raina.

Mutumin da bai yarda da mu’amallar matarshi da kowa ba ba shi da kyakkyawar mu’amalla ko kankani da makwabtanshi balle da mutanen waje.

Ban taba ganin mutum irin Ishak ba. Naja bakina nayi shiru ni dai kawai nasan ba zai tafi ya bar ni a gida ni kadai sai Abulkhairi ba.
Na sake tashi don zuwa kwanciya tunda dare ya soma yi na kwanta har na fara bacci sai naji yana tashina na bude ido ki shirya kayanki mu tafi tare, na ce to. Kayan Abulkhairi nafi diba tunda shi yaro ne sai na dauki nawa guda hudu ban da na jikina.

Sai ‘yan tarkacen amfani, tunda dai ya ce kwana uku zai yi. Tafiya sosai muka yi don kuwa cikin awowi hudu sai ga mu a Kaduna gidan Yaya.

Murna sosai tayi tana rike da Abulkhairi da itama take cewa Baba tana ta shafa shi tare da yaba girmanshi ta ce,

“Ikon Allah! Wato yaron nan da magajinshi ya ke kama?

Ishak ya dan yi murmushi ya ce, Nima lokaci-lokaci sai naga kamar hakan. ta ce,
Ai babu ko wai a ciki, to Allah yasa ka gaji halinshi.

Ta kalle ni yau ga Hauwa’u a gidan Yaya, nayi murmushi muka sake gaisawa na ce, Yaya ban ga yara ba ta ce eh sun tafi makaranta. Tafiyar taku babu sanarwa.

Babu komai?

Ya ce, Eh ban sa rän yinta ba a yanzu nima, ta dauro ne kawai tunda kin ga hutun kwanaki uku kawai na dauko duk da kwanakin sati sai su zama biyar.

Ta ce, Eh hakan yayi kyau zaka wuce kaciya kenan? Ya ce, Eh su Abulkhairi za su gida kenan. Ya ce, A’a su a nan zan bar su.

Ta ce, Saboda me? Bai bata amsa ba sai dai daga ni har ita bin shi da ido muka yi.

Hajiya Baba kamar yadda naji yaron suna kiranta mata ce mai matukar mu’amalla da mutane sabanin kanin nata.

Tun da muka shiga gida kafar yara bata dauke ba haka nan babu abinda bata siyarwa na amfanin gida.

Don haka tana da rufin asirinta daidai ita, don kuwa kaninta a tsaye yake akan al ‘amuranta tunda gidan da take ciki ma a yanzu nashi ne, shi ne kuma ya biya mata ta sauke farali.

Su Rukayya ba su dawo ba sai wajen karfe biyu da rabi. Na bi yarinyar da kallo lokacin da ta durkusa tana gaishe ni. Ba za ta fi shekaru shida ba, ya yanta kuma takwas ta juya tana gaida Babanta ya miko mata hannu alamar ta karasa inda yake ta kwanta a jikinshi yana mata ‘yan tambayoyi.

Sai da ta gama ba shi amsa ya ce, To ba ki tambayi kaninki ba gashi can je ki ki dauke shi, ta taho inda nake zaune tasa hannu ta dauki Abulkhairi da ke zaune yana wasa.

Duk da sanin da nayi ba wani iyawa zata yi da shi ba, ban hanata ba. Ishak ne dai da yaga zata tima shi a kasa ya zabura ya karbe shi.

Sosai na sake da yarinyar saboda yanayinta na nutsuwa don kuwa tafi wanta, tana yawan zuwa inda nake saboda Abulkhairi, ba na kuma hanata daukanshi.

Washegari da sassafe Ishak ya wuce garinsu na sake a gidan Yaya sosai har kicin tare muke shiga ina kuma tayata sayar da kayanta.
Muna cin abincin rana take tambayata ni Hauwa’u ya mijin naki dai komai lafiya ko?
Na ce lafiya kalau Yaya. Babu wata matsala? Na ce ko kadan. Ta ce, To ai shi kenan tunda kin fadi haka, alama ne na ke din mata ce mai hakuri to sai ki kara a kan na da.

Bakunta mai matukar dadi muka yi har Ishak ya dawo washegari na roke shi ya kai ni na yi wa yara siyayya bai ki ba.

Siyayya sosai nayi musu dangin kayan sakawa kayan wasa da kuma na kwalama.

Murna sosai Rukayya ta rinka yi sannan na ce muje studio aka yi mata hoto da Abulkhairi wait and take.

Na bata nata nima na dauki kwafi daya, hoton yayi matukar kyau hakan ne yas Ishak cewa a wanke musu baba, duk da dai ba tsayawa karba zamu yi ba a baiwa Yaya.

Ni kaina bakuntar tayi mun kadan, amma haka muka taho gida washegari muka bar su cikin kewa Rukayya kuwa tana ta kukan a barmata Abulkhairinta.

A yanzu da Abulkhairi yayi wayo kuma nake ganin canji daga wurin Ishak alamar ya dan fara sassautowa daga tsamin halinshi, sai nake ta kwadayin komawata makaranta.

Tun da dai yaron yayi wayo a watanni goman da yayi ne a duniya yake gudunshi ko ina.

Samun Ishak nayi cikin dabara na yi mishi maganar Makarantata tun da ni dai babban burina kenan. Na ce, Don Allah ka bar ni na koma ko ba ka yarda nayi aiki ba ni bani da matsala. Amma burina dai yin karatun ne kawai zai amfane mu ba ki daya. Karatuna ba zai taba zama maka mätsala ba.

Bai ce mun komai ba har na yi maganganuna na gaji nayi shiru. Sai ma gyara kwanciyar shi da ya yi ya juya baya.

CA haka muka ci gaba da zama sana’ar da Ummana ta fara yi sai ya bunkasa ba kadan ba itama dai kayan gidan ne dangin man gyada, maggi, kalanzir har da su kuli-kuli.

Kai komai yanzu sayarwa take yi, kuma sana’a ce mai albarka ta rufin asiri. Ba na ko damuwa don ban bata kudi ba yanzu tunda nasan bata rasawa.

Rasuwa aka yi a unguwarmu kuma Ishak ne da kanshi yazo yake gaya mun, na kuma roke shi ina son yi musu ta’aziyya ya ce to.

Don haka da na gama ayyukana sai ma rike hannun ‘Abulkhairi muka fita na rufe gidan.
A gidan ta’aziyyar naga Hindu da Mominta muka fito tare don komawa gida. Hindu tana rike da hannun Abulkhairi tana gaya mun ta samu admission a Ahmadu Bello University da ke Zariya.

Murna sosai nayi mata ta ce ke dai Maman Abulkhairi har yanzu shiru. Nayi murmushi ban ce mata komai ba.

Muka yi sallama da Momi na mika hannu zan karbi Abulkhairi ta ce, a’a bar mun shi kawai zan turo Abubakar ya dawo da shi.

Na ce to, ba don raina ya so ba sai don kada suyi zaton wani abu sannan kuma shi da ai ba a rowarshi.

Na dawo gida sai dai gaba daya hankalina yana wurin Abulkhairi, har karfe shida a yanzu da Ishek bai cika yin dare ba ina tsoron ya dawo yaga danshi baya gida ban san abinda zan ce mishi ya fahimce ni ba.

Ina jin taba kofa na zabura na mike
cikin sauri na bude kofar, Abubakar ne rike da Abulkhairi sai dai an makara, don kuwa shima Ishak din gyaran parking yake yi.

Jikina a sanyaye na fara kokarin rufe kofar tunda shi ta cikin gareji zai biyo. Ina shiga daki shima ya shigo.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mai Daki 9Mai Daki 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.