Skip to content
Part 14 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

“Ranki shi dade.”

Na ce, “Tare da naka.” Yayi murmushi ya ce, To amin ya azumin? Na ce, Mun gode Allah. Ya kasuwa? Ya ce kullum muna godiya ga Ubangiji.

Na kira ne na shaida miki ayi abin buda baki da ni don ina kan hanya. Cikin mamaki na ce, Gaskiya ko wasa?

Ya ce, Akwai wasa ne a tsakanina da ke? Shiru nayi. Ai maganata da ke babu wasa a cikinta, abinda na kudura a raina kenan kuma kema ina fatan ya zama haka a wurinki.

Sammani na tura ya taho da Ahmad daga inda ya tsaya, sannan ya shigar da shi dakin su da ke zaure na samarn. Muka fara gaisawa yana dan tambayata wasu abubuwa ina ba shi amsa.

Na ce, Nayi mamaki sosai da ka ce mun kana hanya, sai daga baya na tuna ka ce mun kusa da garin ku ne.

Ya ce, Eh kusa da garinmu ne amma ai da nisa a tsakani koda dai ba sosai ba. Ni dan Kano ne Challawa. Kuma saboda rashin adalci irin naki sai ki ka yi tunanin garinmu na zo ba wurinki ba.

Na dan yi murmushi na ce, A a ni haka nake nufi ba. Ya ce, To me yasa ki ka yi riko da wannan hujjar idan ba haka ki ke nufi ba?

Na taso ne takanas nazo wurinki don ki tabbatar da duk wata magana da zan yi miki ko kuma wacce zata biyo baya. Ina kuma fatan ba zan samu matsala daga bangarenki ba. Shiru nayi ina sauraronshi tare da yin wani tunani a cikin raina.

Ba zan son na sake yin gaggawa a cikin zancen neman aure ba, da koma wayea yanzu nafi bukatar fahimtar juna farko tukunna.

Don kuwa babbar matsalar da na gamu da ita a gidan Ishak kenan, koda dai a lokacin ban san komai game da zaman aure ba. Don haka yanzu daban.

Shirun da ya ji nayi shi ne yasa shi ci gaba da magana.

“Na riga nayi booking din wurin kwana a cikin gari, don haka zan dawo gobe don mu ci gaba daga inda muka tsaya.

Zan iya shiga na gaidamutanen gidan? Na ce, Eh bari nayi musu magana. Ya ce,

To.

Kasancewar su Baba dan Juma ba sa nan sai kawai ya gaisa da su Baba Ladi ya wuce.
Kwana nayi ina tunane-tunane ranar saboda ban taba yin zaton cikin dan kakanin lokaci zan fada cikin harka ta zancen aure ba.

Koda Babana ya tabbatar mun ba zai yiwu na koma Makaranta ba sai nake tunanin a kalla zan shekara ko ma fin hakan kafin kuma na sake yin wani auren.

Ko ma don na dan huta wasu abubuwa na 6acin rai da fargaba da ke cikin aurén.

Don haka maganar da na tsayar kawai a raina ita ce ba yanzu zan yi wani auren ba, don kuwa zan fi son idan nayi aure nan gaba nayi zamana ba tare da na sake fitowa ba, tunda dai ba jeka ka dawo ba ne.

A Kamar yadda ya ce haka din kuwa ya yi, karfe sha daya daidai ya yi sallama. Kwalliya mai sauki nayi ta atamfa (Cote Divoire) sai gyale mahadinta. Muka gaisa ya ce, Ina fata dai ban bugo sammako ba ko?

Na ce, “A’a haba. Ya ce, To ai ban sani ba don kuwa da kyar na iya bari goma da rabi tayi.
Ya ce, To me ki ka ce Hauwa’u? Tunda kin ga matafiyi nake dole ina so na koma gida a yau in Allah ya yarda saboda mahaifiyata.

Don haka nake so ki taimaka ki bani amsar da ki ka yii alkawari don ina san halin da nake ciki.

Na ce, To a gaskiya ni bana son maganar aure ta zamo cikin gaggawa, in da hali ina son fahimtar juna ta zamo farko.

Tunda shi din abu ne da ake yi ba da nufin rabuwa ba. Zuba mun ido yayi yana kallona.
Zuwa can ya ce, Kin yi magana irin ta manya, na kuma yaba da zurfin tunaninki.

A matsayin da ki ke a yanzu lokaci kamar yaya ki ke so a bai don ki fahimci mutum, shekara daya ko biyu ko fiye da haka?

Amsar da na kasa ba shi kenan saboda na gane gatse yake yi mun. Kina ganin mutum kamar ni zan iya yi miki irin wannan neman?

Kuma nema na aure? Ni ba karamin yaro ba ne ina da ‘ya’ya ina da mahaifiya, bayan haka kuma ina zaune ne a yanzu bani da iyali.

A irin kallon da nayi miki da iya abinda na fahimta a tare da ke a yanzu bana zaton iyayenki za su bar ki zuwa wannan tsawon lokacin ba tare da aure ba.

Na dade kwarai ban ji wani abu game da wata mace ba kamar yadda ki ka zamo mun Hauwa’u.

Don haka kada kiyi mun rashin adalci wajen zartar da hukunci a kaina. A hankali
na ce mishi to ka bari na dawo gida tukuna.
Ya ce, To shi kenan yadda duk ki ka ce mai neman a ba shi ai ba ya fushi.

Atamfofi masu kyau ya kawo ya baiwa su Baba Ladi dukansu ya ce su ci sallah.

Mun ci gaba da yin waya da Ahmad, kullum yake kirana safe da yamma muna gaisawa.

Cikin dan kankanin lokaci sai muka yi sabo sai kuma na fahimce shi don kuwa ko a waya sai na gane yana da bambanci da Ishak.

Don kuwa shi mai barkwanci ne. ban shirya dawowa gida ba sai ana azumi ashirin da biyar kenan sallah saura kwanaki hudu.

Tsaraba sosai aka yi mun, Baba Ladi da kishiyoyinta kaf dinsu tsarabarsu ta Umma ce.
Don kayan Siyarwarta irin su kuka, bushasshiyar kubewa, daddawa, barkono da dai sauransu tsaraba sai da naki diba saboda sanin da nayi dole sai na biya kudin motarta idan nazo tasha.

Amma duk da haka ban tsira ba, don kuwa kudi mai yawa suka karba saboda bugun shinkafar da suka hado ni da shi.

Tun ina hanya Ahmad yake kira har na kusa sauka. Muna gab da motarmu zata shiga tasha ya kira ni.

“Ga Direbana zai zo ya dauke ki zuwa gida. Na ce, “A’a ayi hakuri yallabai kada Babana ya kore ni a gidan. “

Ni dai har yanzu ban daina mamakin Ishak ba. Ashe ya iya magana cikin tsanaki yi ne ba ya yi.
Ya yi mun alkawura masu yawa amma duk wadanda kudi ne za su aiwatar da su shi kwata-kwata ma bai fahimce ni ba kenan tsawon, zaman da nayi da shi.

Ya manta bai yi mun alkawarin ba zai sake dukana ba zai ba ni lokacin shi ya nuna mun so da kauna da kulawa da tausayawa wadannan abubuwan sune manyan abubuwan da na rasa a gidan Ishak.

“Kiyi mun magana Hauwa’u don Allah.”

Na ce, “Ishak! Ka saurare ni ka ji abin da zan gaya maka, kaje ka samu wata matar ka aura ko kuma ka maida wata daga cikin matanka na baya da ka saką zai fi maka akan zuwa kofar gidanmu da ka ke yi ka ke sawa ana kirana.

Auren da zan yi aure ne na sosai da sosai da zuciya daya ba tare da wata manufa ba, ina son Ahmad ina kuma fatan auren da zamu yi ya zamo mana alheri a duniya.da lahira.

Kai kuma ina yi maka addu’ar Allah ya kara maka hakuri ya kuma baka mace wacce zata iya zama da kai kuma ta kwarai ko don dana da ke gidanka.

Ina kuma rokonka da kada ka sake zuwa gidan nan ka kira ni don gudun bacin rai.”

Zama nayi na yi wa Umma bayanin abin da ya faru tsakanina da Ishak ta ce,
“To! Haka Allah ya kaddara amma wannan al amari.

Hirarmu ta yi nisa da Uma har na rinka bata labarin abubuwan da suka rinka faruwa da ni a gidan Ishak, wadanda ko sau daya ban taba fada ba.

Ta ce, “Ikon Allah, ai shi yasa aka ce wai MAI DAKI shi yasan inda yake yi masa yoyo.”

Na ce, “Shi yasa na yi matukar mamaki da yazo yake kokarin naje na kashe aure na dawo gidanshi.”

Umma ta ce, “To ke dai sai kiyi a hankali, ki kuma yawaita addu’a shi wannan din ya zamo miki alheri, shi kuma Isiyakun Allah ya ba shi wacce zata zame mishi alherin shi ma.

Ai shi yasa wani lokaci sai abu ya same ka kayi ta bakin ciki sai daga baya ka gane alheri ne abin.

Ba gashi ba da yanzu kina can a wannan halin tunda mai hali ai ba ya fasawa kuma maganar gaskiya ita ce zama da miji mai duka abin akwai matukar wahala.

Ki kuma kudura a ranki za ki yi zaman auren ki da zuciya daya.” Shirin aure sosai nake yi da Umma, kudin hidima da Ahmad ya bani shi ne nayi amfani da shi wajen yin kayan daki.

Sai kawai dan cikon da aka yi akai wajen siyan asalin kayan kamfani dan odar da kuma na’urorin kicin.

Duk wani nawa na gayyace shi ciki har da Hindu da Momi, abin ya yi musu dadi ba kadan ba, Momi ce kuma ta kawo mun guzurin littafin girki na turanci (Woman and Home) da ya kunshi girke-girke iri-iri wajen kala dari biyu.

Kayan aure na musamman Ahmad ya yi mun tunda ai ko Hausawa ma sun ce wai masu abu da abunsu. Don kuwa komai a cikin kayan na asalin mai kyau ne.

Mutanen birnin kudu kuwa kamar ajiyar garin suka bayar don kuwa wadanda ba su zo ba kadan ne.

Da addu’ata fal baki da zuci na sa kafa na shiga gidan Ahmad.

<< Mai Daki 13Mai Daki 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.