Aunty Hauwa'u kizo in ji Yayan su Lubabatu. Na waiwayo na zuba ma Tasi'u ido, na ce "In zo fa ka ce?
Ya ce, "Eh shi ne ya aiko ni gashi nan ma a zaure. Umma ta ce "To ki ka sani ko wani abu zai tambaye ki? Na ce, To bari naji naga bai taba aikowa gidanmu a kira ni ba." Hijabina nasako na fita kofar gida inda yake tsaye. Wata gaisuwar muka sake yi yana kallona "Ya na ganki fuskarki wata iri?
Na dan yi murmushi na ce, "Ai da ka kirani ne baka ji yadda. . .