Skip to content
Part 2 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Aunty Hauwa’u kizo in ji Yayan su Lubabatu. Na waiwayo na zuba ma Tasi’u ido, na ce “In zo fa ka ce?

Ya ce, “Eh shi ne ya aiko ni gashi nan ma a zaure. Umma ta ce “To ki ka sani ko wani abu zai tambaye ki? Na ce, To bari naji naga bai taba aikowa gidanmu a kira ni ba.” Hijabina na
sako na fita kofar gida inda yake tsaye. Wata gaisuwar muka sake yi yana kallona “Ya na ganki fuskarki wata iri?

Na dan yi murmushi na ce, “Ai da ka kirani ne baka ji yadda zuciyata tayi ba, sai da gabana ya fadi.

Ya ce, “To da alama dai ba ki da gaskiya kenan.” Na ce, “A’a rashin gaskiyar me? Na dai dauka wani abu ne ya faru kuma ka san ban saba hakan ba.” Ya ce, “Eh to, ai komai dama farashi ake yi ko?”

Ya juya inda su Tasi’u da Sabi’u suke harkokinsu ya mika musu Naira ashirin ya ce a siyo biskit suka karba tare da fallawa da gudu don sayowan.

Ba wai don yazo wurina ko kuma kofar gidanmu ba ne yasa shi yin hakan, dama can dabi’arshi ce inda duk ya gan su to zai saya musu ko biskit ko cakulet.

Ya waiwayo inda nake “To ya ya yanmata ya karatu? Na ce, To mun gode Allah, ni yanzu kina aji nawa ne?” Na ce, “SS1.” Ya ce, “Dama nayi zaton kina tafiya ne tare da su Luba, sai dai a hanya za ki tsaya tunda ban ga alamar kina mayar da hankali tare da bada himmar yin karatun ba.”

Na ce, “Me yasa ka fadi haka? Ya ce, “A’a na gane kamar aure ki ke so.

Wayancewa nayi tamfar maganar bata bata mun rai ba.

Kuma kafin na samu amsar ba shi sai na hango Babanmu yana tahowa daga wurin aiki kuma yake na ce “Ni zan shiga gida ga Baba nan ya dawo. Har kasa Abdussamad ya tsugunna ya gaida Babana, sannan ya wuce ni kuma na shigo gida ina yi mishi barka da zuwa.

Ban wuce dakina ba abincin Babanmu na dauko na kai mishi dakin Umma tare da ruwa. Yana sanye da kayan gida da alamar har ya cire na aikin shi sannan na sake mishi sannu da zuwa na wuce dakina.

Washegari da sassafe kamar kullum sai da na hada mana abin karyawa, kunu da dumamen tuwo sannan na saka uniform dina na dauko hanyar Makaranta.

Kamar daga sama ina shiga ajinmu kafin na zauna sai ga Malam Ali ya shigo,
ya ce “Maras zuciya, ai dama nasan yau ma sai kin dawo shi yasa na bugo sammakon zuwa ajin naku don na gani.

Ba kuma zan bar ki ko darasi daya ki samu ba. Juya kawai ki tafi.” Na juyo na kamo hanyar dawowa gida, yau kam ta lungun unguwarmu na biyo don kaucewa idon Abdussamad. Ban tsaya yin komai ba kan yar yamushashshiyar katifata na hau na kwanta ba zan iya cewa ga iyakacin abinda Zuciyata take gaya mun ba, illa iyaka dai kawai nasan babu mamaki, ni din ba zan samu cikar burina ba ne a rayuwata shi ne na ni din na zama Nos, wato Malamar jinya.

Nayi kuka har na gaji ban san sanda barci ya dauke ni ba, na dai farka ne naji ana kiran sallar azahar.

Na mike tare da yin salati da na tuna ko abincin rana ban dora ba, tunda idan ina gida ni ce mai yi. Na fito cikin sauri na samu har Umma ta riga ta sauke tana rabo.

Shinkafa da wake ne, da mai da yaji. Nayi mata sannu sannan na shiga bandaki don kama ruwan in alwala. Har na gama hidimomina na gida yau ko waiwayon littafan Makarantana ban yi ba, don kuwa na fara fidda rai abinda kwata-kwata ban saba yi ba kenan. Dabi’ata ce kullum Zan yi bitar littattafai na koda nake da matsala wajen biyan kudin Makaranta ni din ina cikin daliban aji da suke da matukar kokari. Tunda har Malamaina ma sun shaida hakan, to amma ya zan yi? Malam Ali ya taso ni a gaba, bana kuma ganin laifinshi tunda aikinshi yake yi.

Duk wadannan tunanina ne kafin wayewar gari, don kuwa tsintar kaina nayi da fara shirin Makaranta, har na fito tunda sammako nayi ina yiwa Babana sallama wanda a yau din zan riga shi tafiya.

Ya ce, “Ke Hauwa’u ba Ummanku jiya ta ce mun satin nan kaf idan ki ka je makaranta koro ki ake yi ba?

Na ce, “Eh haka ne Baba.” Ya ce, “To amma a hakan ke gara miki kiyi ta zuwa ana korarki? Maganar gaskiya shi ne nayi baki wani abu ki kai Makarantar taku. To sai dai mu mamatsalar wurin aikin mu yawa ce da ita tunda wannan watan shi ne wata na wajen uku da ba a bamu albashi ba, amma daga zarar an bamu wani abu zan ba ki ki kai musu ko da babu yawa ne. Sai ki ba su hakuri yau din idan kin je.”

Na ce, “To Baba.” Na fito daga gida ina tafiya tare da tunanin maganar Babana ni ba abin in ce mishi ai yanzu ta kai ma ko saurarona basa yi ba.

Sai da babu amfani tunda ba da gangan yake kin biya ba.

Na shiga aji na zauna a darare ganin har karfe tara tayi Malam Ali bai zo ba, sai na waiwaya bayana inda Sadiya Tanimu ke zaune sai dai ban ganta ba, don haka na ce wa wacce suke zaune tare rmai suna Zubaida.

Dun Don Allah dan bani aron littafinki ná Chemistry na dan fara kwafa kafin a tashi.
Ta kalle ni ta dan tabe baki tare da girgiza kanta kafin ta ce, “A’a a gaskiya ba zan miki karya ba, ba zan iya ba haka kawai azo a kore ki na manta ki wuce mun da littafi.

Bari dai wacce ta saba baki tazo don naga itama kamar ke karatun ba damunta yayi ba, bambancinku kawai ita ana biya mata kudin Makaranta.”

Na juyo na ci gaba da wasu sabgogin ba tare da na tsaya bai wa Zubaida amsa ba.

Ba a ko kai mintina biyar ba bayan nan sai kawai Malam Ali ya shigo. Tun kafin ya fara kiran suna na mike na kamo hanyar dawowa gida, zuciyata cike da kunci da bacin rai.

Har na zo zan shiga gida sai naji ana kirana. Abdussamad ne. Na tsaya ya karaso inda nake.
Hauwa’u kenan, yau ma kin kasa zama ne kiyi karatun har zuwa lokacin tashi?

Wani gululun bakin ciki ya taso ya tokare ni, wai wannan me yake nufi ne?

Na dago kaina da niyyar ba shi amsa. Sai dai na kasa saboda dama kiris nake jira, don haka da na lura kawai kuka zai kubucemun sai na shige gida ba tare da na sake sauraronshi ba.
Ina shiga gida wurin Umma na wuce na durkusa, kuka na kama yi babu kakkautawa, ba tace mun komai ba sai da na yi ya ishe ni ina share hawayena sai ta ce “To ni kam Hauwa’u ai bani da abin yi miki da ya wuce na ki hakura da wannan sintiri da ki ke yi ana koro ki ba tare da fashi ba.

Ki dan saurara kema ki samu nutsuwa amadadin wannan zirga-zirgan da ki ke yi.
Idan Babanku ya samu kudi ai ya gaya miki zai ba ki dan wani abu ki kai musu ko? Kafin karshen wata muga abinda Allah zai yi.”

Na dawo daki na debi kayan wanki na fitar na hado da na su Tasi’u gaba daya na fara yi, sai wajen Azahar na gama nayi wanka na nemi wuri na zauna da niyyar hutawa a ka yi sallama da ni.

Na riga nasan Abdussamad ne, don haka kamar ba zani ba sai kuma na dauki gyalena na fita.

Yana tsaye a kofar gidanmu sanye da wandon Jeans da riga shirt fitted na gaishe shi a dake.
Ya ce, Hakuri nazo baki don naga kamar dazu na bata miki rai, kiyi hakuri ban yi da nufi ba. Na ce “Babu komai.

Ya ce, “Kin tabbata? Na dan yi murmushi na ce, “Uhum!”

saboda yanayin yadda ya yi tambayar.
Ya ce, “Ban san dalili ba Hauwa’u, sai nake
ganin kamar ni din ina da ruwa a cikin al amarin karatunki.

Don kuwa ko babu komai ai ke kanwata ce. ko ba haka ba? Na ce, “Eh haka ne.

Ya ce, “To idan mutum ya samu halin yin abu to baya sakaci da wannan damar har takubuce mishi. Kiyi amfani da kuruciyarki ki taimaki kanki kiyi karatu.

Muka shiga wata hirar ta daban, yana tambayata wasu abubuwan ina ba shi amsa har Babana ya dawo.

Yau ma ya gaishe shi ya wuce na biyo shi a baya yana tambayata yau an bar ki kin yi karatun ko kuwa an sake koro ki?
Na ce, An koro ni Baba. Ya ce,To sai kiyi hakuri muga abin da Allah zai yi.”
Na ce, “To.

Har satin ya kare ban koma makaranta ba, haka nan kullum bayan sallar La’asar Abdussamad yana zuwa mun hira.

Ranar Lahadi da yamma kwatsam sai ga Sadiya Tanimu, na tare ta cikin farin ciki ba kadan ba. Makwabtanmu na tura aka sayo mun Zobo mai tsabta,

Na kuma yi sa’a dafaduka muka yi mai kyau ta kuma yi dadi na kai mata dakina bayan sun gaisa da Umma. Tana cin abincin muna dan hira tana bani labarin abubuwan da suka faru bana nan, da irin gwajin da aka yiyyi a aji.
Naji wani iri a raina. Ta tashi zata tafi na mike da niyyar yi mata rakiya. Da nisa sosai na kaita har kusan barin unguwarmu gaba daya.
Ta wuce ni kuma na kama hanyar dawowa gida. Baiwar Allah salamu alaikum. Jin yanayin sallamar ne ya sani juyawa, wani mutum ne a tsaye sanye cikin farar shadda jampa da wando.

Na amsa tare da nufin ci gaba da tafiya. Dan dakata mana yanmata. Tun daga dan nesa fa nake bin ki ban dai yi miki magana ba ne saboda ganin yanayinki. Na san ba yarda za ki yi ki tsaya cikin mutane ba, shi yasa ban tsaida ke ba sai da naga mun zo nan wurin. Sunanki nake so ki fada mun.

Na ce, “Hauwa’u.” Ya ce, Gidanku fa? Ba tare da yin wani dogon tunani ba na yi mishi kwatance. Ya ce, “To ya
gode. Na dawo gida na ci gaba da harkokina. Har a yau Monday ma ban yi nufin zuwa Makaranta ba, saboda maganar da Babana ya yi mun na jiranshi zuwa karshen wata don ganin abin da Allah zai yi.

Da yamma ne aka yI sallama da ni, cikin zuciyata Abdussamad ne, don haka hijabina na dauko na fito ga zatona. Abdussamad din ne, Sai kawai naga mutumin jiya.

Yau ma sanye yake cikin tafafe na kamala, jamfa da wando, rigar half jampa ta matukar yi mishi kyau.

“Ina wuni? Na fara gaishe shi cikin girmamawa, don kuwa ba karamin yaro ba ne.
Lafiya Hauwa’u, yaya karatu? Na ce, “Mun gode Allah.”

“A aji nawa ki ke a Makaranta? Na gaya mishi ya dan yi murmushi “Kina da saura dai ashe.” Muka dan yi hirar karatu kadan, abinda ya sa na saki jiki da shi.

“Kina da sha’awar yin karatu mai zurfi nee? Ko za ki tsaya ne daga gama Secondary?” Na ce, “Idan na samu halin ci gaba haka nake so.”
Ya ce, Eh yana da kyau, kin san karatun ‘ya mace ba karamin abu ba ne ga ya’yanta, da kuma mijinta baki daya.

A daidai lokacin ne Abdussamad yazo, ganinmu yasa shi juyawa ya tafi. Mutumin ya kalle ni yana dan murmushi. Ina fata dai ban tsarewa saurayin naki wuri ba’? Na ce, “A’a ba saurayina ba ne. Ya ce, “Menene, abokinki ne?” Na dan yi murmushi, ya dan yi ajiyar zuciya ya ce, “To Malama Hauwa’u, ni dai kin ganni ba yaro ba ne karami, don haka ya kamata ki gane ba da wasa ko yaudara nazo wajen ki ba.
Na gan ki ne na yaba da halinki da kuma dabi’arki ta nutsuwa da na gani a tare da ke. Ni ba mutumin garin nan ba ne, nazo wani dan aiki ne wanda nake ganin kamar zai dauke ni tsawon shekaru uku zuwa hudu.

Sunana Ishak, ina kuma aiki ne da ma’aikatar noma wato (Ministry of Agriculture). Ina fata zan samu hadin kan da nake nema a tare da ke? Ina so na gaya miki ba zan tauye ki na hana ki karatunki ba, don kuwa kina da kuruciya sosai. ldan aka yi miki hakan ba a yi miki adalci ba.

Don haka ina so kiyi tunani mai yawa a kai zan dawo rana ita yau din nan don jin abin da ki ke ciki. Na ce, To. Ya sa hannu ya miko mun kudi, ya ce “Ungo wannan. Na dan yi jim kamar ba zan karba ba, ya ce “A’a karbi kawai.”

Na ce, To na gode. Sannan ya bude bayan motar shi ya sauke mana doya manya goma da buhun shinkafa da wata leda babba baka. Yayi sallama ya tafi. Na dade a wurin a tsaye kafin na shiga gida.

Ummma ta zubawa kayan idanu ta ce, “Ikon Allah! Shi kuma wannan ko waye sai Allah. Na zauna na jawo ledar na bude, zannuwa ne masu kyau guda biyu da kayan shafa masu daraja. Sai da Babana yaci abincine sannan ya kira ni na same shi a zaune. “Ke Hauwa’u ashe dama kin fara tsayuwa da samari ne ni ban sani ba?” Naji wani iri a cikin jikina, na kuma rasa abinda zan ce mishi. Ya ce, Ke ía nake sauraro don ni nayi zaton shi wanan yaro Abdussamad da nake ganinku da shi ba wani abu ba ne a tsakaninku face makwabtaka da mutunci.

To shi kuma wannan a ina ki ka same shi?” Nayi wa Babana bayanin komai game da mutumin, har da ranar gamuwvata da shi da kuma abinda ya gaya mun da kan shi ya ce “To tashi ki tafi.”

Na dawo dakina na zauna bayan na kai wa Umma har da kayan atamfofin da kudin wanda ta mika su ga Babana gaba daya.
Washegari Abdussamad bai zo ba kamar yadda ya saba, sai bayan kwana biyu ne inda dawowa daga siyo sugan da naje yi a shagon unguwarmu, na ganshi tsaye kusa da shagon.
Ya ce, “Hajiya Hauwa’u. Na ce “Ni din ce kuma Hajiya a yau?” Ya ce Eh mana, ba dole nace Hajiya ba, wannan irin luntsumemiyar mota haka ai kin san mai niya ake cewa hajiya ba wanda yaje ba. Kin ga yanzu dole mu rinka yi a hankali kenan tunda Tunku ma yasan shurin da yake yi wa kashi.

Na ce, “Haka ne.” Ban tsaya cigaba da jin abinda yake fada ba, tunda na fahimci so yake ya soka mun magana sai kawai nayi gaba.
Ranar da Ishak ya ce zai zo kuwa sai gashi ya dawo, na kuma isar da sakon Mahaifina a gare shi ta yana son ganinshi.

Bai tsaya wani dogon bata lokaci ba ya ce, zai jira shi ba sai yaje ya dawo ba, don haka shigowa gida nayi na bar shi da nufin shi na sai yaga Babana kafin ya tafi.

Hakan kuwa aka yi, ban san yadda suka yi ba, bani kuma da damar tambaya, don haka harkokina kawai nasa a gabana.

Na dai yi nufin tambayar Umma ko Babana zai bani kudin nan naje na biya kudin Makaranta dashi, sai dai na gagara saboda nauyin da nake ji.

Ban yi zaton zuwanshi a washegari ba, kwatsam sai ga shi. Ina tsaye yayin da yake jingine jikin motarshi ya ce, “Na dawo ne yau don nayi miki magana kan al’amuran da muka tattauna da Baba. Muyi magana da ni da ke sabodafahimtar juna. Jiya ganin da nayi mishi ya bani izinin turo magabatana don daidaita maganar aure.”

Cikin wani irin mummunan faduwan gaba na dago kai na kalle shi, karo na farko da nayi hakan a karo na uku da fara zuwanshi gidanmu.

Yana cikin matsakaitan mutane, shi din ba kyakkyawa ba ne, haka nan ba za a kira shi mummuna ba.

Shi da kanshi ya lura da canzawata, ya ce “Shi yasa na ce zan ganki don mu tattauna a tsakaninmu. Kina da matsala a kan turo magabatana da zan yi?”

A hankali na girgiza kaina alamar a’a, don kuwa babu wani hukunci da Babana. Zai zartar na sa kafa na shure shi da sanina, kuma ina cikin hayyacina ba.

Ya ce, To ya naga yanayinki ya canza? Ban san dalili ba sai na samu kaina da ce mishi “Karatu nake yi.” Ya dan yi murmushi.

Don ta wannan nayi wa Mahaifinki alkawarin zan sa ki a Makaranta kiyi ta karatun har ki gama, bayan wannan kuma sai me? na ce, “Babu.” Ya ce, “To ni ranar Jumma’a zan tafi Kaduna gida wurin iyayena, don mu zanta kan maganar.”

Na ce, “To Allah ya kiyaye hanya.” Ya ce, Amin. Ya miko mun kudi a hannunshi na karba tare da godiya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mai Daki 1Mai Daki 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×