Baba Ladi ta kalle ni ta ce, "O' oh maganar auren ne ta mayar da ke haka?”
Ko gidan Yaya Auwalun da nayi niyyar zuwa kasawa nayi. Aikin da na saba yi na gida kuwa Umma ko saurarona a kai ba ta yi ba.
Al'amuran baya sai suka fara dawo mun. "To shi kenan shi kuma wannan auren idan na yi shi menene zai zamo nashi matsalar? Don kuwa a yanzu sai na fahimci cewa babu wata mata da take zaune a dakin mijinta ba tare da ta yi hakuri da wasu matsaloli ba sai dai kawai na wasu. . .